Uncategorized

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE HAUSA NOVEL

By
Zeey kumurya
7️⃣5️⃣

………..Lumshe idona nayi wani sanyin daɗi na ratsa zuciyata, a rayuwata bazan iya tuna wasu kalamai da naji suka mun daɗi kamar yadda kalma I love You ɗin yaya ta munba, ko haɗa aurenmu da Daddy yayi bekai wannan kalmar yimun daɗi a cikin zuciyata ba, gabadaya damuwar danake ciki na nemeta na rasa, wasu hawaye masu sanyi dana tabbatar na farin ciki ne suka zubo daga idanununa, a hankali shima ya lumshe idonsa yana jin wani matsananci feeling akanta, fuskarta ya hade da tata har suna jiyo hucin numfashin juna, a hankali yake goga karan hancinsa akannata numfashinsa na fita da sauri da sauri, buɗe lumshashshun idanunsa yayi da suka ka sukayi ja saboda fitina, harshensa ya fito fashi ya fara lashe mata hawayen fuskarta cikin matsanancin sonta dake ƙoƙarin tarwatsa masa zuciya, wani dogon numfashi ta sauke tana jinta a wata duniyar daban ta nishaɗi, kasa yayi da harshensa ya dora shi akan kyawawan laɓɓanta ya fara zagaye su cikin wani irin salo daya kusa zautar da Maryam, ƙanƙarmeshi tayi sosai wani baƙon yanayi me wuyar fassaruwa na riskar ta, sunyi 3 minutes a haka kafin a hankali ya raba fuskokinsu yana sauke numfashi kamar wanda yayi tseren gudu, kwantar da kanta yayi a kirjinshi ya shiga shafa bayanta ganin yanda jikinta yake rawa, numfarfashi na shiga saukewa nayi luf a jikinshi ina shaƙar daddaɗan kamshinsa, ganin ta dena rawar jikin ya ɗago ta daga jikinsa yana bin fuskarta da kallo, buɗe idona nayi na sauka daga jikinsa na koma na jingina da fuskar gado ina maida numfashi, bece komaiba ya sauka daga kan gadon a hankali fita yayi daga ɗakin gaba-daya, bin bayansa nayi da ido har ya fice, ajiyar zuciya na sauke farin ciki mara misaltuwa na ƙara mamaye dukkan zuciyata, “i love You maryam” na maimaita kalmar sa ta ƙarshe a gare Ni, wani murmushi na saki me sauti tare da kai hannu na shafa lips ɗina ina jin tamkar a yanzu yake lasarmun shi, inanan zaune cikin tsananin sauƙin sa, ya dawo ɗakin da sallama ɗauke a bakinsa, lumshe idona nayi da sauri domin wata irin kunyarsa nake ji, can ƙasan makoshi na amsa masa sallamar, kayan bacci ya ɗaukowa Maryam a ɗakinta a fitar da yayi, ajiye mata su yayi akan cinyarta ya ɗan rankwafar da kansa dai_dai fuskarta yace “ki tashi kiyi wanka mu kwanta inajin bacci” batare dana buɗe idonaba na gyada masa kai alamar Toh be ƙara cewa komaiba shima ya ƙarasa gaban mudubi ya ɗauki wayoyinsa, zama yayi akan stool ya shiga latsa wayarsa, a hankali na miƙe na sakko daga kan gadon ina satar kallon inda yake, kayan baccin daya ajiyemun na ɗauka na shige toilet dinsa, murmushi yayi bayan ta shige toilet din, singlet din jikinsa da wando three-quarter ya cire ya miƙe ya ajiye su, ya rage daga shi se boxer, kashe light din ɗakin yayi ya haye kan gado ya kwanta ya lulluba da blanket, ban wani jima a toilet din ba na fito, ajiyar zuciya na sauke me ƙarfi ganin ɗakin da duhu, dama inata tunanin yanda zan bari ya ganni da ƴar guntuwar rigar baccin dake jikina, a hankali nake taku na ƙarasa gaban madubi, ribbom ɗin kaina na cire na ajiye, wayarshi dake kan mudubi na ɗauka na haska na ɗauka lotion na shafa a jikina, sannan na ɗauki daya daga cikin turarukansa dake kan mudubin na fesa a jikina, switched din wayar nayi na ajiye, a hankali kamar me sanda nake taku wai ni karna tashesa na ƙarasa na hau kan gadon, ta bayanshi na kwanta ina fuskantarsa, kamar na matsa jikinshi na rungumeshi haka nakeji amma bazan iyaba dan karna ballowa kaina ruwa, kusan 5 minutes da kwanciyarta ya juyo a hankali yana kallonta, Maryam da idanunta suke a rufe amma ba bacci take ba, ta ɗan buɗe idonta kaɗan tana kallonsa itama, hannunsa yasa yajawota jikinsa, a tare suka saki wata sassanyar ajiyar zuciya, cikin rada yace “Ummu” nace “uhm” yana ƙara shigar da ita jikinsa yace “bakici abinci ba zaki kwanta?” nace “naci fa” yace “yaushe?” nace “kafin ka dawo” yace “wannan daban, dinner nake nufi” a shagwabe nace “to ai da yamma naci, kuma yanzu nasha choculate naci popcorn ya cikamun ciki” be ƙara cewa komai ba, se gashin kanta daya shiga shafawa, hannuna na ɗora akan kirjinsa kwantaccen gashin kirjinsa naja nace “mene wannan yaya?” yace “aush da zafi fa” ƙara ja nayi nace “hakanne da zafi” runtse idonsa yayi ya cire hannuna daga jikinsa, turo bakina nayi gaba nima na cire hannunshi daga kaina, murmushi yayi bece komaiba se ƙara rungumeta da yayi a kirjinsa yana shaƙar kamshin gashinta, a hankali ya ɗora hannunsa akan kafadarta cikin dabara yake ƙoƙarin sauke hannun rigar jikinta ƙasa, ɓata fuska nayi nace “yaya” zuciyata cike da tsoro domin ban manta azabar danaciba wancan karon, shiru ya mata be amsaba sedai yabar ƙoƙarin sauke mata hannun rigar ya koma shafa damtsen hannunta, a shagwabe na ƙara cewa, “yaya kamun shiru” yace “mene ne?” kamar zanyi kuka nace “bakomai tunda kaki kulani da farko” lips ɗinsa na ƙasa ya lasa bece komaiba, dan ya gane rigimar dabe sha kwana 2 biyu bace za’a masa yanzu, dama kullum se sun kwanta bacci take masa duk dan kar ya mata wani abun, yana sane kawai kyaleta yake, jin yamun shiru na fara mutsu_mutsu a jikinsa ina ƙoƙarin tashi daga jikinnasa, ƙara lumshe idonsa yayi yana sakin wani numfashi saboda yadda yakejin breast ɗinta na goguwa a kirjinsa kasancewar babu bra a jikinta, Bakinsa ya ɗora akan kunnenta yace, “me yafaru wai?” nace “ba kaki kulani ba” cikin sexy voice yace “am sorry my angel bari na miki hira me daɗi kina so ko?” nace “ehh, kamun da yawa har nayi barci” dannasan idan nayi bacci bazai tasheni ba, balle ya mun abunda nake tsoro ba, wani munafukin Murmushi yayi ya fara mata kalaman soyayya masu daɗin saurare, da sanya mutum cikin nishaɗi, lumshe idona nayi ina ƙara mannewa ajikinsa cikin tsananin jin daɗin kalamansa, kamar a mafarki haka nakejin abun, wai yau nice kwance a kirjin hearbeat ɗina yana rattabomun kalaman soyayya haka, wani irin farin ciki da sanyin daɗi ne ke ratsa zuciyata, jina nake kamar a ƙololuwar sama saboda nishaɗi, a hankali yake yin ƙasa da rigar jikinta still bakinsa na cikin kunnenta yana jero mata tsadaddun kalam kauna, ina jinshi amma banyi yunkurin hana shiba, saboda daɗin kalamansa da nakeji, ciremun rigar yayi gabadaya daga jikina ya fara yawo da hannunshi a sassan jikina cikin tsananin zaƙuwa, luf nayi ina karɓar sakonsa duk da a matuƙar tsorace nake, a hankali ya ɗago da fuskarta ya haɗe bakinsu guri ɗaya ya fara kissing ɗinta a zafafe, while yana cigaba da sarrafata cikin wani salo me tsayawa arai da wuyar fassaruwa.(duk wayon amarya…..????????). Rungume take a jikinsa yana lallabata bayan sun fito daga wanka, har lokacin kuka take ƙasa_ƙasa, bayanta yake bubbugawa a hankali yana hura mata iskar bakinsa a cikin kunnenta da haka ya samu bacci me nauyi ya ɗauke ta, ajiyar zuciya ya sauke ya gyara mata kwanciya a jikinshi, ba jimawa shima baccin ya ɗaukeshi. washegari, a hankali na buɗe idona, akan kyakkyawar fuskarsa, lumshe idona nayi na ƙara budewa ina sauke numfashi, hannuna na kai a hankali na shafi kwantaccen sajen gefen fuskarshi, ɗan motsawa yayi kaɗan nayi sauri na ɗauke hannuna daga fuskarshi dan kar naje ya farka, zare jikina nayi daga jikinsa a hankali na tashi zaune, addu’ar tashi daga bacci na karanto a raina, kallon fuskarshi nayi, nayi murmushi cikin jin daɗi da farin cikin kasancewarmu tare, hannunshi dake jikina na zare a hankali, ƙara maido hannunshi yayi yana matsowa jikina sosai, lallausar kwantacciyar sumar kansa na shafa cikin kaunarsa, ina kallon fuskarsa, ɗauke hannuna nayi daga kansa na janyo filo nasa masa a kirjinsa, rungume filon yayi, ajiyar zuciya na sauke na sakko daga kan gadon, falo na fita, kamar dare haka falon yake saboda duhu, kunna light din falon nayi haske ya gauraye, agogon bango na kalla naga har 8 ta wuce, window naje na yaye labule na leka, garin yayi duhu dindum, haɗari ya hado bana wasa ba, iska me ƙarfi ce take kadawa, jiya da daddare ba’ayi ruwan sosai ba yayyafi akayi kaɗan,sakin labulen nayi na nufi ɗakina, ina jin jikina babu daɗi dan jiyama naci kwakwa a hannun yaya sedai ba kamar wancan karon ba,yau Jikinane kawai yake mun ciwo, gashin kaina na fara busawar sannan na shiga toilet na tara ruwan zafi na shiga ciki, naji daɗin jikina kuwa sosai da nayi haka, kaya na canza na koma ɗakinshi, yana kwance yana baccinshi yanda na barshi, toilet na shiga na kwaso kayanmu da muka cire jiya dana bacci na dawo ɗakina na wanke, kafin na gama wankin ruwa ya sakko me ƙarfin gaske kamar ba farkon damuna ba, bayan nagama wankin na share ɗakina da falo, dan bazan iya mopping ba, wankin danayi naji duk nagaji. ɗakinshi na ƙara komawa, har lokacin be tashi ba, zama nayi akan locker na janyo ledar daya kawo mun jiya na dakko choculate guda ɗaya na fara sha, yana jin shigowarta yayi shiru kamar bacci yake tashinsa kenan daga baccin, a hankali ya buɗe lumshashshun idanunsa ya zuba mata, yanda takeshan choculate ɗin kamar wata yar baby, yarintarta ta fito sosai ga wani kyau data masa, a jikina naji ana kallona juyowa nayi na kalli gadon muka haɗa ido, waro idona nayi da alamun mamakin ganin ya tashi, wani kayataccen murmushi ya sakarmun, da hannu yamun alama naje gurinshi, a hankali na tashi na hau kan gadon na zauna a gabansa, kaina a ƙasa nace “ina kwana” lumshe idonsa yayi ya buɗe a hankali batare daya amsa mata ba, se ido daya kafeta dashi, turo bakina nayi gaba nacigaba da shan choculate ɗina, yunkurawa yayi ya tashi zaunen shima yana salati a hankali, kwantar da kanshi akan kafadarta yana leken fuskarta a ƙoƙarin sa na san su haɗa ido yace “kin tashi lafiya” na gyada masa kai alamun eh, yace “yanzu ba ciwon jikin?” ƙara gyada masa kai nayi, yace “dama jiyanma duk raki ne” kawar da zancen nayi da faɗin, “yaya ruwa akeyi sosai” window ya kalla yace “ai shine ya tashe ni” nace “amma dai yau bazaka fita ba?” yace “why?” nace “ruwa mana” yace “idan ya tsaya zan fita ai” na ɗan ɓata fuska nace “ka bari gobe ka fita, kaga jiya ka dawo baka gama hutawa ba” yana gogamun sajen fuskarsa a kuncina yace “gobenma haka zaki ce karna fitan” nace “Allah bazanceba, ka huta yau kaji, kaga ruwa ma ake” yace “to dama nace miki zan fita ne” nace “ai nasan zaka ce zaka fitanne” murmushi yayi yace “bakyaso in fita” na gyada masa kai alamar eh, ɗayan hannunshi yasa ya kwantar da ita a jikinshi yace “nima banason na fita, na fiso in zauna inta kallonki ina jin daɗi” lumshe idona ina shaƙar kamshinsa bance komaiba, ragowar choculate ɗin hannuna ya karba yace “daga tashi se shan zaƙi? shan zaƙin ki yayi yawa Ummu, shiyasa kike ciwon ciki, zan kwashe sauran na ledan ce na bayar kin gama shan rabonki” ɗago kaina nayi daga jikinshi cikin shagwaba nace “to bakai ka siyomun ba?” yace “ai ba siyo miki nayi ki shanye a lokaci ɗaya ba, kaɗan_kaɗan zaki dinga sha, kuma shima ba kullum ba, amma ke jiya kinsha da yawa, yauma daga tashi tun dira akansu” cikin marairaicewa nace “to kayi hakuri karka kwashe sauran zan dinga sha kaɗan_kaɗan ɗin” yace “to na barmiki, amma idan kika shanye kafin 1 month bazan ƙara siyo miki ba” nace “to na yarda, yanzu bani wannan na ƙarasa shanyewa” yace “A’a kingama shan na yau” nace “Please daga wannan fa shikenan se gobe zan ƙara” yace “to anjima sai kisha” badon naso ba na haƙura, amma na ɓata fuska sosai, murmushi yayi yace “muje muyi wanka” nace “ni nayi ai” yace “sai kimun ni” waro manyan idanunta tayi waje sosai tana kallonshi, daga mata gira yayi yana jifanta da wani irin da kallo daya kashe mata jiki, barin jikinshi nayi na koma gefe na kwanta nace “bacci nakeji” bace mata komaiba ya miƙe ya sauka kan gadon ya shige toilet, ajiyar zuciya ta sauke tare da lumshe ido cikin jin daɗin ya shige wankansa shi kaɗai, dan batasan zatayiba daya takura se sun shiga tare, jiyama da sukayi taren kuka ta dinga masa, kuma har sukayi suka fito idanunta a rufe suke, batasan ya dawo ɗakin ba, sai ji kawai tayi an ɗauketa, be direta a ko inaba se a cikin ruwa tajita, yanzunma idanunta a rufe sukayi wankan tana ta aikin turo baki gaba, shikuma yanata tsokanarta.. Tsaye yake a gaban madubi yana shafa mai da towel daure a ƙugunsa, Maryam kuma tana kan kado ta ƙudundune jikinta tunda suka fito daga wankan ta kasa kwakkwaran motsi, kunyarsa take ji sosai kamar ƙasa ta zage ta shige cikinta haka take ji, juyowa yayi a hankali ya dubeta, da sauri ta juya masa baya, murmushi yayi ya ƙasara bakin gadon ya tsugunna a gabanta, ƙara yunkurin juya masa baya tayi towel din jikinta ya kunce ya ɗanyi ƙasa, rabin Brest ɗinta ya fito waje, “saurin riƙe towel din tayi tana hawaye tace “kadena kallo na” idanunsa akan kirjinta yace “dama Ni ba kallon ki nake ba, ko kinga mun haɗa ido?” tana ƙara volume ɗin kukanta tace “gashinan kana kallar mun….” se kuma tayi shiru ta fashe da kuka, dama kaɗan take jira akan tsokarta da yay tayi da suna wanka, tashi yayi ya zauna a gefenta ya janyota jikinsa ya rungume yana murmushi yace “nifa ban kallar miki komai ba” cikin kuka tace “amma ai kagani a toilet” yace “shima ban kalla ba fa” ya ƙarashe zancen yana share mata hawayen fuskarta, shiru tayi jinta ajikinsa tana sauke ajiyar zuciya, gashin kanta ya shafa yace “to tashi muje in shiryaki, kinga time yana tafiya ba muyi break ba” barin jikinshi nayi nace “zan shirya da kaina” yace “shikenan jeki ki shirya” nace “toh rufe idanka, karka kalleni” ya rufe idon yace “na rufe” kallon fuskarshi nayi naga idanunshi a rufe, ta bayanshi na sauka daga kan gadon ina faɗin “karka juyo sai nace nagama” ya gyadamun kai, na ƙarasa gaban mudubi na fara shafa mai, inayi ina kallonshi ta cikin mudubi, harna gama shafe_shafe na be jiyoba, sai dai kuma ba kayan da zansa a jikina, tunda nawan ya jiƙasu suna toilet a shanye………✍️

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button