Uncategorized

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE HAUSA NOVEL

Da yamma ina kwance a falonmu akan doguwar kujera, daga zuwa ajiye tsarabar da Aunty tamun na ɓige da kwanciya, da sallama ya shigo falon duk da beyi tunanin ze sameta ba, tashi zaune nayi da sauri ina amsa masa, tattausan murmushi ya sakarmun tare da ware mun hannayenshi, tashi nayi nima ina murmushi duk da banason tashin na ƙarasa gurinshi na faɗa jikinshi, hannunsa yasa ya zagaye bayanta suka saki ajiyar zuciya a tare, lumshe idona nayi ina shaƙar daddaɗan kamshinsa da nake jin daɗin sa fiye da koyaushe a yanzu, a hankali nace “sannu da zuwa” sai da ya rabani da jikinsa tare mun kiss a goshi sannan yace, “yawwa, yana ganki anan, nayi zaton kina can wurin Aunty” nace “yanzu na dawo, na ajiye abu ne, kuma na kwanta na kasa tashi.” bece komai ba ya kama hannuna muka shiga ɗakinshi, muna shiga na hau kan gado na kwanta shikuma ya shiga cire takalmanshi, bayan ya gama ya cire har kayan jikinsa ze shiga toilet ya dube ni, yace “ba tayi” lumshe idonana nayi kawai na girgiza masa kai alamun a’a, bece komai ba ya shige toilet din, harya fito ina nan yanda ya barni ko kwakkwaran motsi banyi ba, ya gama shirinsa tsaf cikin ƙananun kaya da suka matukar yi masa kyau, sai tashin daddaɗan kamshinsa yake. kan gadon ya hau ya janyota ya ɗora kanta akan cinyarsa wuyanta ya taɓa yace “anya Ummu lafiyar ki kalau kuwa?” nace “meka gani?” yace “nidai kawai kalar me cuta kika mun” nace “toni babu inda yake mun ciwo a jikina, lafiya kalau nake” yace “zan kaiki dai hospital gobe, a dubaki” nace “ba sai mun jeba, Allah ni lafiya kalau nake” shiru yayi kawai yana kallonta, nace “kayi kyau” yayi murmushi yace “amma bankai kiba ai” nace “kama fini, wama ze haɗa” yace “ba kya kallon kanki a mudubi amma, kin ƙara kyau sosai, jikinki kamar madara” nayi dariya nace “kai kuma naka kamar nono” yayi dariya kawai tare da tashina zaune yace “muje ingaida Aunty” tashi nayi badannaso ba, muka fita, yana kulle Kofar part ɗinmu yace, “yawwa naga anmun wani text me daɗi ana zubamun godiya” nace “ohhh sorry, yanzuma na manta daka dawo ban maka ba, thank you so much, kuma akwai tukuici me tsada” yace “thank for what?” nace “komai ma” ba ƙara cewa komai ba ya kama hannuna muka nufi part ɗin ammi. Mustapha yayi farin ciki da mamaki sosai dayaga kayan da Aunty ta haɗo, shiya ma manta ana wani lefe a aure, wato shine dalilin kuɗin da Aunty ta karba a hannunsa, yana duba kayan kamar yadda Aunty ta umarceshi yace “amma Aunty, wannan kayan ai sun fi ƙarfin kuɗin da kika karɓa” Aunty tayi murmushi kawai, dan ita da ita zatayi lefen duka, wani dalili ne kawai ya sata karɓar kuɗinnasa, tace “to ai shikenan tunda dai an haɗa” yace “a’a Aunty ki….” Aunty ta katseshi da faɗin “ka kalli kaya kawai, amma baruwanka da nawa aka kashe” godiya sosai shima Mustapha yayiwa Aunty, shiyasa a kodayaushe yake ƙara kaunarta da ganin girmanta, domin Aunty mutum ce. washegari tun safe su Aunty suka koma, ammi tayi_tayi su ƙara kwana suka ce a’a, dama kawo kayan kawai suka zo.

Yau Laraba, ana ie gobe zan tafi Kano bikin saleemat, tun safe ammi ta kira aka zo har gida aka mun kunshi da kitso me kyau, zaman kitson da lallen da nayi duk sai naji jikina babu daɗi, dama ta bakin yayan kwana 2 banajin daɗin jikina, kawai naki faɗa masa ne, dan nasan tsaf sai ya hanani zuwa bikin, jiyama yayi_yayi muje asibiti nak’i yarda, gashi yau ko abinci na kasa ci. Da daddare ina kwance akan gado a ɗakina, shikuma yaya yana haɗamun kayan da zan tafi da su, a cikin ɗinkakkun kayan lefena na ɗauka wanda zanyi fitar biki dasu, ya ɗauko wani less zai sa a cikin jakar dayake haɗa kayan nace, “karka sakashi, na fasa zuwa dashi” bai kulata ba, ya cigaba da haɗa kayan, ya lura rigimartata yau tafi ta kullum, tun jiya da daddare ya haɗa mata kayan tafiyar, amma yau da safe sai tace ta fasa zuwa dasu, ta sake zab’ar wasu ya haɗa mata, yanzu ma a darennan tace sai ya sake haɗa mata suma ba zata da su ba, gashi yau yana dawowa ta tareshi da rigimar an mata kitso mai zafi harda masa kuka kamar shi ya aiketa, ya rarrashe ta, anzo cin abinci kuma taƙi ci, tabarshi yaji da kewarta ta 1 week da zeyi mana. na bata fuska kamar zanyi kuka nace “yaya meyasa kasamun shi? ka cire Please nifa na fasa zuwa dashi, banason kalarshi” bai ko kalletaba balle tasa ran ze amsa mata, yana gama haɗa kayan ya fice daga ɗakin abinsa…….✍️

saura ƙiris mu huta gabadaya????

By
zeey kumurya
7️⃣8️⃣

………Tashi zaune nayi inajin ba daɗi a zuciya ganin yanda ya fita kamar ransa a b’ace, ni kaina banajin daɗi akan abin da nake masa, amma haka kawai nake tsintar kaina indai ina tare da shi, sai inta neman fitina,a kasalance na tashi na bi bayanshi, baya falo hakan yasa na nufi ɗakin shi, yana kwance akan gado yana latsa wayarsa, sallama nayi cikin sanyin murya, ajiyar zuciya ya sauke, a can ƙasan makoshi ya amsa mun, ban damu ba na haye kan gadon na kwanta a jikinsa ta baya, cikin shagwab’a nace “yaya” yay mun banza, na ƙara cewa “yaya” ya ƙara mun banza, sai na saka masa kukan shagwaba, lumshe idonsa yayi cikin rashin sanin abunyi, ganin yaƙi kulani sai na ƙara volume din kukan, juyowa yayi cikin faɗa yace “idan na ƙara jin uhm ɗinki, kin fasa zuwa bikin, idan kuma ba kijiba, ki cigaba” tsit nayi na kwantar da kaina a ƙirjinshi ina turo baki, yace “ɗaga mun jikina” ƙara riƙe shi nayi nace “kayi hakuri na dena” yace “ko d’igon hawaye karki bari ya ƙara fitowa daga idonki, idan kina so na haƙura” nace “bazan ƙara ba” ya shafa kitson kanta, yace “ki dena kuka baby tah, banajin daɗi idan kinayi” nace “to ba kai bane kake mun abunda nake kukan ba” yace “yanzu mena miki, kika zo kika cikamun kunne” nace “ba kace ƙunshi na yayi kyau ba, kuma nazo ina maka magana kak’i kulani” ya kamo hannuna yana shafa gurin ƙunshin yace “yayi kyau sosai” nace “bakaga na ƙafar ba” ya tashi zaune ya matsa gurin ƙafata ya duba lallen, yayi kissing ƙafar yace “shima yayi kyau sosai” nace “bakamun a hannun ba” murmushi yayi ya kama hannunnawa yayi kissing ɗinshi shima, nace “thanks” ina murmushi, yace “kitson ya dena zafin?” na ɗan shagwabe fuska nace “yanayi kaɗan_kaɗan” yace “sorry, zai dena duka insha Allah” nace “Allah yasa, kazo muyi bacci, bacci nakeji” yace “wanka fa” tashi nayi zaune nace “muje muyi to”

Washegari tun safe Maryam aka gama shiri, sai murna take zataje Kano, mustapha kallonta kawai yake yana jin kamar yace ta fasa tafiyar, dan ma tare zasu tafi, amma tun yanzu ya fara kewarta. Sai kusan 11 suka yiwa su  ammi sallama suka tafi, dayake a Jet din Daddy zasu tafi, mustapha yayi waya anzo a ɗaukesu, dan baya son dogowar tafiya a mota, kuma  maryam ɗinsa ma bayason ta wahala a zaman Mota, cikin wasu mintuna suka sauka a Kano, Daddy ya turo direba ya ɗaukosu zuwa gidansa, muna shigowa layin su Daddy, na tuna rayuwata gidan, gabana ne ya faɗi dana tuno yaya Sadiq da mommy, lumshe idona nayi kaina kwance akan kafadar yaya ina tuna rayuwar gidan, kamar banyiba yanzu gashi komai ya wuce, shafa gefen fuskata da yaya yayi shiya dawo dani daga duniyar tunanin dana lula, d’ago kaina nayi ina bin gidan kallo dan har mun ƙaraso ciki, becemata komai ba dan bayajin daɗin zucuyarshi ko kaɗan, buɗe murfin motar yayi ya fita, ajiyar zuciya na sauke nima nabiyo bayansa, kama hannunta yayi suka nufi cikin gidan, a part din Daddy suka yada zango, dan daddy’n yana gida bai fita ba, Daddy kallon Maryam da mustapha kawai yakeyi cikin tsananin farincikin ganinsu, canzawar da Maryam tayi da ƙara gogewar datayi ya ƙara fito da kamar da mustapha da Maryam suke masa. Maryam tasha kararramawa da girmamawa a gidan Daddy, kamar ba ita ce da abar wulakantawa ba a da, su haidar suma sai nan_nan suke da ita, sai bayan magriba suka nufi gidan gwaggo, Maryam bata ga Sadiq ba, kamar zata tambayeshi kawai sai ta fasa, amma tayiwa Daddy da su haidar yame jiki. Mustapha da kansa yake driving ɗin su zuwa gidan gwaggo, Maryam na nuna masa hanya dan ba wani gane gidan yayi ba, yana yin parking baikai ga kashe motar ba, Maryam ta buɗe ta fita da gudunta ko handbag ɗinta bata ɗauka ba, ta shige gidan gwaggo tana kwala mata kira, gwaggo tana banɗaki taji muryar Maryam ta dogaro ƴar sandarta ta fito da sauri tana faɗin, “Muryar wa na keji haka kamar ta mutanen Jos” Maryam ta ƙarasa gareta ta rungumeta tare da faɗin “nice gwaggo, oyoyo gwaggo ta” gwaggo tace “oh ni ladi, zaki kadani” na saketa ina turo baki nace “gwaggo duk murnar ganin ki cefa” gwaggo tayi dariya tace”to ai kinsan ƙafartawa lallaɓawa nake” na  marairaice fuska nace “gwaggo wai har yanzu ƙafar batayi sauƙi ba?” gwaggo tace “sauƙi sai na Allah Maryama, inanan ina amsar magani dai” na kama hannunta muka fara tafiya nace “Allah ya karo sauƙi gwaggo,  sannu” gwaggo tace “Ameen, sannunki sannunki da zuwa, ya hanya, kunsha hanya” nace “Alhamdulillah” gwaggo ta miko mun dadduma na shimfida a ƙasan ɗakinta, muka zauna muka ƙara gaisawa, yaro ne ya shigo ɗauke da kayana, nace “Laa gwaggo tare fa muke dashi” gwaggo tace “mai gidannaki?” nace “Ehh” tace “kuma shine kika barshi a waje?” bata jira amsataba ta kalli yaron daya shigo da kayan tace “maza kacewa wanda ya baka kayan ya shigo” yaron ya amsa mata ya fice, nace “gwaggo ke kaɗai ce agidanne?” tace “asabe ta fita, na aiketa nan bayan layi yanzu zaki ganta ta dawo” miƙewa nayi na matsar da kayannawa na gyarawa yaya shimfudar daddumar, Ni kuma na koma bakin gado  kusa da gwaggo na zauna.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button