Uncategorized

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE HAUSA NOVEL

By
Zeey kumurya
7️⃣9️⃣

………..Wani wawan burki suhailat taja tare da waro idanuwanta duka waje, Mustapha yaga Suhailat sarai amma yayi kamar bai san da wanzuwar halittarta a gurin ba, ya kama hannun Maryam ɗinsa, tare rufe murfin motar. Suhailat ta haɗiye wani yawu mai ɗaci, ilahirin jikinta rawa yakeyi hannunta ta ɗaga da ƙyar ta nuna Mustapha cikin ƙara da rawar murya tace “yaya! wacece wannan?” gabanane ya yanke ya faɗi da naji muryar suhailat, domin bansan da ita a garin bama balle nayi tunanin ganin ta a gidan, riƙe hannun yaya nayi gam, ina kallonsa. Ya shafi gefen fuskata yana murmushi ba tare da yace komai ba, ya jani muka fara tafiya, Suhailat data sandare a gurin ta bisu da kallo, cikin tsananin tashin hankali mara misaltuwa, wani irin juyawa kanta yayi, lokacin da tayi katarin ganin Mustapha ya ɗauki Maryam cak a hannunsa kamar wata y’ar baby, lokacin da zasu haura kan step ɗin bakin part ɗinsa, dafe kanta tayi kirjinta na wani irin bugu, “mafarki nakeyi ko gaske my life ne tare da wata mace, macen ma house girl ɗinmu, to me hakan yake nufi?” ta faɗi haka a fili cikin ƙaraji tana yarfe hannu, juyawa tayi tamkar mahaukaciya ta nufi part ɗinnasa, amma kafin ta kai har sun shige ya rufe kofarsa. bubbuga ƙofar ta hauyi tana faɗin “wlh bazan yadda ba, bazai yiyu ba, ina duniyar inganka da wata mace ba niba, wlh sai na kasheta!” ihu take tayi tana zuba surutanta, data gaji kuma sai ta bar bakin k’ofar ta kwasa da gudu ko nauyin cikin jikinta bata jiba ta nufi part din Daddy, a hanya suka ci karo da Aunty zata koma part din mommy, cikin tsawa Aunty tace “ke, baki da hankali kike gudu haka? kina lafiyar ki kuwa?” Suhailat ta tsaya tana zuba uban haki tare da fashewa da kuka tace “Yaya ne” Aunty tace “Muhammad?” Suhailat tace “Eh shine” Aunty bata ƙara cewa komai ba tayi gaba abinta, Suhailat ta bita a baya tana cigaba da kukanta, a falon Mommy aunty ta zauna tana faɗin “ke banason shirme, uban me Muhammad ɗin ya miki kika sani a gaba kina mun ihu haka, kuma me ya kaiki gurinsa ma?” Suhailat taja majina tace “Aunty tare fa naganshi da waccan kujakar yarinyar sun sauka a mota, kuma harda kama mata hannun” Aunty tace “ke mene naki a ciki to?” Suhailat da bata taɓa tunanin aure ne tsakanin Maryam da Mustapha cikin kuka tace “Aunty dole na damu mana, yaya fa shine wanda zan aura, kuma naganshi tare da wata, nasan duk dan ya k’untatamun yayi haka, Aunty dan Allah ki bashi haƙuri, nasan duk akan cikinnan yake mun haka” Aunty ta kalleta ta tabe baki kawai, Suhailat taci gaba da kukanta zuciyar na mata zafi da kuna, musamman idan ta tuna yanda mustapha ya ɗauki Maryam, a haukanta ita ta ɗauka duk abunda Mustapha yayi dan ya k’untata mata yayi dan tasan babu abunda zai haɗa Mustapha da Maryam wanda ya wuce aikatau, tasan abunda yayiwa Maryam ɗinma dan taji haushi yayi.

A kan gadon ɗakinsa ya dire Maryam, lumshe idona nayi inajin ba daɗi sosai a cikin raina ganin Suhailat da nayi, takalmin kafarshi ya cire tare da zare mata na ƙafar ta itama, hawa kan gadon yayi ya zauna tare da ɗora kanta akan cinyarshi, a hankali ya zare mata hijabin jikinta gami da hular kanta ya shiga shafa kitson kanta yana sakin ajiyar zuciya. Buɗe idona nayi a hankali cikin jin daɗin yanda yake shafamun kan nace “yaya” ya ɗan fesar da numfashi yana bin jikinta da kallo yace “uhm” shiru nayi bance komai ba, yace “menene?” na ɗan turo baki gaba nace “ba komai” tattaremun rigata ya farayi ta ƙasa, na riƙe hannunsa zuciyata na ɗan bugawa, cikin cool voice yace “ciremun zanyi, kisha iska naga ana zafi” na tashi zaune da sauri nace “banajin zafi ni” ya janyoni jikinsa ya rungumeni a kirjinshi, a jiyar zuciya na sauke me ƙarfi tare da kwantar da kaina a ƙirjinshi, hannunsa yasa ya zagaye bayanta yana sakin ajiyar zuciya, yana jin yanda ɗumin jikinta yake ratsashi ga wani ni’imtaccen ƙamshi da take mai daɗi da kwantar da zuciya, bai yi yunƙurin yi mata komai ba, duk da yanda yake cikin tsananin buk’atuwa da ita. kiran sallar magriba ya sashi zare ta daga jikinsa a hankali yana sauke numfashi, komawa jikinsa nayi dan bangajiba, yayi murmushi tare da ƙara zareta daga jikinsa, na kwabe fuska tare da turo baki gaba, kissing lips ɗinta yayi yace “sorry, muje muyi sallah” ya ƙarashe zancen tare da sauka daga kan gadon, na bishi da kallo kawai har ya shige toilet, alawala ya dauro ya fito, na sauko daga kan nima ina kallonshi nace “ka tahomun da alawa Please bakina ɗaci” ya dagamun kai kawai ya fice. Bayan an idar da Sallah ina kwance akan gado ina game a wayata ya shigo ɗakin, bakinsa ɗauke da sallama, na amsa masa ina dubansa, tun da muka shigo na fuskanci yanayinsa gaba-d’aya ya sauya kamar na me ɓacin rai, tashi zaune nayi nace “sannu da zuwa” yace “yawwa” tare da mikomun hannu, sakkowa nayi na kama hannunnasa, gyara mata hijabin jikinta yayi ya jata suka fice, part ɗin Mommy ya nufa dasu domin su gaida Aunty, na ɗan shagwabe fuska nace “yaya ina alawata?” yay mun banza, shikam tunda yaga suhailat yaji ransa yayi wani mugun ɓaci, yaso yayi control ɗin kanshi gurin boye ɓacin rannasa dan kar Maryam ɗin ta gane, amma ya kasa boyewa, ga abunda ya gani a jikin suhailat ɗin ya dugunzuma masa hankali, yana fatan Allah yasa idonshi gizo ya masa, dan har yanzu yana kallon suhailat a matsayin ƴar uwarsa ta jini, a sanin da yayiwa suhailat ko tumbi bata dashi cikinta a shafe yake, amma yau duk da hijabi a jikinta ya ga cikinta ya ɗan turo irin na masu ciki, runste idonsa yayi tare da matse hannun Maryam yana jin wani irin ɗaci a ransa, ƴar ƙara na saki ya buɗe idonsa da suka fara kadawa sukayi ja tare da sassautawa mata riƙon hannun. Aunty na zaune a falo ita kaɗai, Suhailat kuma tana ɗaki ta kulle kanta tana kuka da bori kamar sabuwar kamu, sai yanzu take takaici da bata damk’o Maryam ta mata dukan mutuwa ba, amma ta kudirce a ranta indai suka ƙara haɗuwa sai ta yabawa aya zak’inta. Inayin sallama na hango Aunty kwace hannuna nayi na ruga da gudu na rungume Aunty cikin murnar ganin ta ina gaisheta, Aunty na murmushi tace “Lafiya kalau Maryam, ya biki” nace “Alhamdulillah” Aunty tace “Allah ya sanya Alkhairi” na amsa da “ameen” Aunty ta dubi Mustapha suka gaisa, bayan sun gama gaisawar ya tashi ya fice, binshi nayi da kallo harya fice, sosai na hango damuwa a tattare dashi, sai naji zuciyata duk babu daɗi, na sauke numfashi kaɗan na dubi Aunty nace “Aunty baki zo da Aliya ba?” Aunty tace “Ehh, basuyi hutun school ba” nace “shiyasa da mukayi waya batacemun zaku zo ba” Aunty tace “ai bazata faɗa miki ba, tanata fushin nace bazan zo da ita ba” nayi murmushi kawai, muka ɗanyi shiru na wasu mintuna, ni inata baza su ido inga ta inda suhailat zata bullo, can dai na dubi Aunty nace “Aunty ina baaba Talatu kuwa?” Aunty tace “tana garinsu, kinsan masu aikin gidannan duk sun tafi, sai masu mazaje masu aiki a gidanne kawai suka rage, tun da babu mace a gidan” nayi shiru ina tuna Mommy da yanda ta zuba iko a gidannan, amma yanzu kamar ba’ayi ba, “ko tana inama oho?” Sai bayan sallar isha’i yaya yazo muka koma part d’insa, har na taho banga ko da gifatawar Suhailat ba, shikuma har lokacin fuskarsa babu walwala, a falo ya zauna nima na zauna a kusa dashi, cikin lallami da karyar murya nace “yaya nah” ya juyo ya kalleta yana jin ɓacin ransa na raguwa, nace “meke damunka?” ya girgizamun kai alamar ba komai, na marairaice sosai nace “dan Allah kayi haƙuri ka faɗamun, ko ni na maka wani laifin?” na ƙarashe zancen idona na kawo ruwa, janyota jikinsa yayi yace “karki kuka Please” na turo baki nace “to ka faɗamun meke damunka, tun ɗazu sai bata rai kake kuma kaki kulani” yayi murmushi yana kallon fuskarta yace “dagaske babu komai, ina tare da ke mai zai dameni” ganin ya saki fuskarsa sai naji daɗi sosai a raina ina kallon cikin idonshi nace “banason naga kana damuwa ko kaɗan” ya lumshe idonsa cikin jin daɗin maganarta yace “dagaske” nace “dagaske mana yaya” ya ƙara rungumeni a jikinsa, knocking din da akeyi yasashi sauketa ya tashi yaje ya buɗe Kofar, faruq ne hannunsa ɗauke da leda da yayi musu take a way na abinci da drinks, Mustapha ya karba ya dawo ciki, yunwa nakeji sosai dan rabona da abinci tun safe shima kaɗan naci, shiyasa yana kawo wa ba musu na zuba mana muka fara ci, da kanshi yake bani a baki, kuma duk lauma ɗaya idan naci sai yamun kiss a saman lips ɗina, wai dan nafi cin abincin da yawa, aiko naci sosai dan abincin yamun daɗi. Bayan mungama mukaje part din Daddy muka gaisheshi, Daddy ya dubi Mustapha yace “yaushe zaku koma gida?” Yace “Gobe insha Allah” Daddy yace “yaushe zaku dawo Kanon gaba-daya da zama?” yace “Bayan sallah kamar da sati biyu haka” Daddy yace “Allah ya kaimu, itama ammin taku zata dawo Kanon da zama insha Allah” Mustapha ya murmusa kawai baice komai ba, bamu jima sosai ba muka dawo part ɗinsa, wanka kawai mukayi muka kwanta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button