Uncategorized

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE HAUSA NOVEL

Aunty ce zaune a falon Daddy ita da Suhailat data taso ta da ƙyar, Daddy kawai ido ya zubawa Suhailat gumi na yanko masa ta ko’ina a jikinsa, idanunshi sun kada sunyi jajur saboda tsananin ɓacin rai da kunar zuciya bayan Aunty ta gama rattabo masa jawabi akan cikin dake jikin Suhailat, Aunty ta kwantar da murya ganin yanayinsa tace “kayi haƙuri yaya, kada ka sanya damuwa a ranka har wani ciwon ya kamaka, bawa baya taɓa kaucewa ƙaddararsa, wlh nima ba ƙaramin tashin hankali na shiga ba a lokacin dana gane tana da cikin, na kulle kaina a daki ni kaɗai naci kuka na, daga baya kuma na fawwala wa Allah komai.” Daddy ya sauke numfashi kawai baice komai ba, tsana da danasanin auran Mommy suka ƙara cika masa zuciya, domin duk lalacewar da suhailat tayi ita ta ɗora ta akan hanya, itace silar lalacewar tata, ya dubi Aunty yace “nama rasa me zance sauda, jin abunnake kamar almara ƴar ɗan’uwa guda ɗaya jal da ya barmun amanar ta itace take ɗauke da cikin shege” sai kuma yayi shiru yana maida numfashi, itadai Suhailat tana durk’ushe tana kuka, Aunty ta danne tata damuwar cikin kwantar da murya ta shiga bawa Daddy baki, ganin yanda ya damu matuƙa fiye da yanda tayi tunani, da ƙyar ta samu Daddy’n ya sassauta damuwarsa yace “shikenan Sauda, babu yadda zanyi nasan wannan wata jarrabawar ce daban, kuma zanyi ƙoƙari wajen ganin na cinyeta, Allah ya bata lafiya ita da abunda ke cikinnata ya kuma raba lafiya” Aunty tace “ameen” Daddy ya dubi Suhailat yace “kafin ku koma kadunan, ki turomun wanda ya miki cikin zamuyi magana” yana gama faɗar haka ya tashi ya shige ɗakinsa, dan Kaɗaici kawai yake buƙata a halin yanzu, Aunty taja Suhailat suka koma part ɗin Mommy, Suhailat ta tambayi Aunty ina Mustapha ya kai sau biyar amma Aunty ko sau ɗaya bata ganka mata ba, ta mata banza.

Washegari misalin ƙarfe goma da ƴan mintuna na safe, mustapha ne kwance akan doguwar kujera yana kallon Maryam data ke ta ɓata rai tana turo baki, tun bayan da suka karya tace ya kaita gurin Aunty shikuma yaki, saboda yasan bacci takeji dan jiya be barta tayi wani baccin kirki ba, ya rarrasheta akan tayi baccin yanzu kona 1 hour ne amma taki, shikuma yaƙi barinta taje gurin Aunty’n, shine ta kwace wayarsa ta matsa daga kusa dashi ta koma wata kujerar ta zauna, shikuma ya tasata a gaba da kallo yana murmushi, dan kallonta kaɗai ma ya isa sanyaya masa zuciya, wayarsa dake hannuna nace ta fara ƙara, dubawa nayi naga number ce babu suna, k’in bashi nayi harta katse aka sake kira, ya tashi zaune tare da faɗin “a bani wayata mana, tunda ana kira na ko” na turo baki gaba na tashi na kai masa, ya karbi wayar tare da janyota ta faɗa jikinsa ya matse gam yanda baza ta iya tashi ba, nima banyi yunƙurin tashin ba nayi luf a jikinsa, d’aga wayar yayi ya kara a kunne, Muryar mace yaji kuma kamar yasan muryar, daga ɗaya ɓangaren aka ce “Ranka ya daɗe, dafatan ka tashi lafiya” yace “lafiya” a taƙaice, ta ƙara cewa “nasan har yanzu baka gane da wa kake magana ba, kana magana da P.A dinka ce” yayi shiru kamar yadda nayi shiru ina sauraren sautin muryar mace da naji, can yace “Ok nagane” P.A tayi murmushi cikin jin daɗi tace “na kira in gaishe kane, in maka ya jiki da kuma jajen abubuwan da suka faru” cikin mamakin yanda akai P.A tasan abubuwan yace “Ok thank” tare da kashe wayarshi. na d’ago kaina nace “dawa kayi waya?” yayi wani munafukin murmushi yana kashemun ido yace “budurwatace” nace “wacece ita?” yace “nace miki budurwa tace, kuma kinsan me?” nayi shiru ina ɓata fuska sosai, ya ƙara kashemun ido yace “tana sona sosai, kullum tana cemun I LOVE YOU” na fashe da kuka ganin da gaske yake, har wani nishaɗi yake yi yana faɗamun wai tana sonshi” yace “menene kuma na kuka, tambayata fa kikai na faɗa miki” cikin kuka nace “to sai ka faɗamun kuma, ba sai kacemun watace da banba amma ba budurwa kaba harda wai….” na kasa ƙarasawa naci gaba da kuka na yace “sai nai ƙarya kuma, a’a gwara dana faɗa miki gaskiya, budurwace tana sona sosai kamar ranta, ko da yaushe tana cemin I LOVE YOU” ya ƙarashe zancen da kissing lips ɗinta yana murmushi, kuka nasa sosai na shiga dukan kirjinsa ina kukan nace “ai nima ina faɗa maka” yace “baki taɓa faɗa mun ba ni” na masa banza na cigaba da kukana, ganin yanda take kukan bil haqqi ya shiga rarrashin ta, taƙi saurarensa, bakinta ya buɗe a hankali ya zira mata lips ɗinsa, da sauri na cafka na fara tsotsa kamar jariri na shan nonon uwarsa ina sauke ajiyar zuciya, inajin daɗin sucking lips ɗinsa sosai yanzu, sai inji kamar na samu sweet, ya sauke ajiyar zuciya jin tayi shiru ya shiga shafa bayanta a hankali, sai da na tsotse masa lips ɗin son raina sannan na cizeshi kaɗan, ya zare bakinsa da sauri daga nata yana sauke numfashi, na kwantar da kaina a ƙirjinshi ina turo baki gaba, ya leko da kansa wajen fuskata yace “sweetheart harda cizo kuma” nace “um” yace “da zafi fa” nakai finger na kan lips ɗinnasa nace “sannu” yace “yawwa” tare da sharemun hawayen fuskata, ya dagoni daga jikinsa yace “muje mu gaida Daddy da Aunty, tunda kinki yin baccin” na tashi na shiga ɗaki na dakkona hijabina na fito, ya mikomun hannunsa na mak’e kafada naƙi riƙe masa, ya matso kusa dani yace “to zo in ɗaukeki” na ƙara maƙe kafad’a, yace “goyo fa” da sauri na d’aga masa kai, yayi murmushi ya tsugunna yace “hau” na haye bayansa ina dariya yace “shikenan” nace “Ehh” ya tashi tsaye yana faɗin “wash kina da nauyi fa” na masa gwalo ina dariya, a bakin k’ofar part d’in ya sauke ni yana maida numfashi, yace “kin sagarmun da baya” nace “sannu, amma goyon da daɗi zaka kuma mun?” ya murmusa yace “zan dinga miki kullum ma” cikin jin daɗi nace “Nagode” ya kama hannuna muka fice, part ɗin Mommy muka fara zuwa muka gaida Aunty, aunty kallon Maryam kawai take yanda taga ta ƙara dashewa tayi fari ga nishi da takeyi kaɗan_kaɗan irin na masu ciki. Bayan sun gaida Daddy ya ɗauketa suka nufi gidan gwaggo.

Mommy Tasha cinya sosai, daga ciwon kannan ya koma mata cuta mai tsanani, Binta kawartace ta samo mata mai kula da ita tana biyanta, Mommy kamar bazata rayu ba, sai a satinnan ta fara samun sauƙi, ta rame sosai tayi baƙi ga wasu kurashe manya duk sun fito mata a jikinta, yau ta tashi da jikinnata da kwari babu laifi, tun safe ta shirya zasu fita ita da Binta, duk da har yanzu ba wai lafiyar ta isheta bane amma tsabar masifa zata fita, tana ciwonne amma hankalinta gaba-d’aya yana kan Daddy da Mustapha akan mummunan kudirinta akansu, yanzu fitar daza tayima zataje tayi visa ne na zuwanta London neman Mustapha, tana ta jiran Binta zata rakata amma shiru_shiru bata zoba, gashi tana ta kiran wayarta bata shiga, ganin har 12 ta wuce ta ɗauki mukullin motarta tayiwa mai jinyarta sallama ta fice dan zuwa gidan Binta. Mustapha suna zuwa gidan gwaggo basu wani jimaba Maryam ta kwaso kayan ta ta musu sallama, Mustaphama ya shiga yayi wa gwaggo sallama shima, har gidan umman saleemat ma ya shiga ya mata Allah ya sanya Alkhairi, sannan suka tafi. A titin commissioner road Mommy tazo zata karya kwana, su sukuma su Mustapha suna ɗayan hannun an tsaidasu, kamar ance Mommy ta juya, tana juyawa tayi katarin ganin Mustapha kasancewar glass din motar tasu a zuge yake……..✍️

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button