Uncategorized

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE HAUSA NOVEL

Dakin hajiya na nufa,domin gyarawa,bayan nagama shan kukana adaki,na yadda mutanen gidan suke nunamun kyama a fili.duk yanda nake ganin kyan dakin Dana sauka,amma kokama kafar wannan beyiba,bansan yazan fasalta kyau da tsaruwar dakinba. “Aljannar duniya na furta afili,wannan daki haka sekace baza’a mutuba.babu wani datti adaakin sosai,gadon nafara gyarawa….seda nagama gyaran dakin duka sannan koma toilet.bayan nagama da dakin hajiya na koma dakin suhailat,alokacin duk sun fashe Daga falon se hajiya kadai tana kallo. Itama dakin suhailat din tamkar na hajiya,kalar kayan dakinne kawai kowa danasa,seda nagama kare masa kallo sannan na fara gyarawa,amma ita suhailat,dakinta da datti sosai,tamkar ba maceba, duk yayi kaca kaca kayan data cirema gasunan akasa,dakin gaba daya ba kintsi komai a hargitse.toilet dintama duk datti…………

             ********************

Kwance yake akan makeken royar bed dinsa,se juyi yakeyi yakasa tashi.hannunsa dafe da mararsa,saboda wani ciwo datake masa,ga muguwar sha’awar data addabesa,lumshe idonsa yayi cikin jin azabar ciwo,tare da taune lips dinsa na kasa……….✍️

Kuyi hakuri da wannan,zanje dubiyane amma insha Allah gobema zakujini da daddadan page????????????

BY
Zeey kumurya
ABUNDA KA SHUKA………
(shizaka girba)

MALLAKIN
????
ZAINAB USMAN KUMURYA

FARIN JINI WRITERS ASSO…..????

~Free novel~

Bismillahirrahmanirrahim

0️⃣9️⃣

…………sosai yakejin azabar ciwon marar,Addu’a yafara karantowa yana neman taimakon ubangiji,cikin ikon Allah yasamu ciwon yafara lafa masa.daurewa yayi ya yunƙura, ya tashi zaune,agogon bangon dake ɗakin ya kalla, “yasalam” ya furta tare da dafe kansa,saboda ganin lokaci yana Neman ƙure masa,ga wadanda zasu kawo kaya suna jiransa.miƙewa tsaye yayi ya nufi toilet ya sakarwa kansa ruwa,kozeji sanyi ajikinsa.yakai 20 minutes yana wankan,kafin yafito daure da towel a ƙugunsa,sedan karami dayake goge jikinsa dashi.cikin mintuna ƙalilan ya shirya,cikin wasu tsadaddun ƙananan kaya,Wanda suka ƙarbi jikinsa.fuskarsa tayi fayau alamun ba ƙlu yakeba.batare da yayi tunanin cin abinciba ya kwashi wayoyinsa ya zira a pocket dinsa,ya fice daga ɗakin………

        ***********

Seda na gyara mata ɗakin tsaf,gwanin sha’awa.se’alokacin kyawu da tsaruwar dakin ya ƙara fitowa,tsayawa nayi ina ƙara kallon ɗakin,araina nace dakin suhailat haryaso yafi na hajiya haɗuwa.ga kamshin room freshener, Dana turaren wuta dake tashi adakin.seda nagaji dan kaina da kallon,sannan na fito naja mata kofar.babu kowa yanzu a falon, se TV daketa aikinta ita kaɗai,har nazo zanshiga ɗakina naji wata sassanyar murya ta kira sunana.”maryam!” Juyowa nayi ina kallon me kirannawa cikin mamaki,batare Dana amsaba. Fuskarsa ɗauke da murmushi yazauna,akan kujera. Me kirkin gidanne,kamar yadda nasa masa suna. “Kiƙaraso mana maryam,ya faɗi haka yana dakko wayarsa yafara latsawa,ƙarasa nayi gabansa cikin sanyin jiki na durƙusa aƙasa. ɗagowa yayi yana kallona,sunkuyar dakaina nayi kasa saboda kallon danaga yana bina dashi. ” haba maryam,kisaki jikinki dani mana,ki zauna akan kujera ki tashi daga kasannan. “A’a nanma ya isa na furta masa hakan saboda bugun da zuciyata takemun.duk yadda yaso na zauna akan kujera amma naƙi,dole ya haƙura yace.”kinsan meyasa na kiraki,girgiza kaina nayi alamun a’a.cigaba yayi da magana. ” inason na baki haƙuri,akan abunda aka miki a gidannan,banji dadiba,amma babu yanda zanyi, haka halin ƴan’uwana yake se..katsesa nayi dacewa “babu komai,yaya kokaɗan banji haushiba kokuma na damu.”murmushi yayi cikin jin daɗin kiransa da yaya datayi yace.”shikenan ƙanwata ga wannan ya miko mun ledar dake hannunsa,ɗagowa nayi ina kallonsa cike dason ƙarin bayani. “Kayan kwalliyane nasiyo miki,nasan Ku mata dason kayan ƙyale_ƙyale. Murmushi nayi cikin jin daɗin nuna kulawarsa agareni “nagode sosai,Allah yasaka da alkhairi Allah yakara buɗi. “Ameen,amma babu godiya atsakaninmu maryam,tunda naganki naga kin burgeni saboda nutsuwarki,da kamalarki,daga ganinki daga gidan tarbiyya kika fito.inason kuma kimun wata alfarma guda ɗaya.! “Ni kuma,har inada wata alfarma dazan iya maka.na tambayeshi cikin Saudi ina nuna kaina da hannuna. Murmushi yayi me sauti yace. “Ke mana,maryam ai kowanne dan’adam yanada alfarmar dazeyiwa wani arayuwarsa,komai kudinsa kuwa, kuma komai talaucinsa.nasan kina tunanin matsayina da naki kamar baza ki iyamun alfarmaba,to ni agurina da talaka da me kudi duk ɗayane,tunda duk Allah ne ya halicci kowa kuma ya’ajiyesa a inda yaso.jinjina kaina nayi cikin gamsuwa da bayanansa. Alfarma danakeso kimun maryam itace,inaso kiɗaukeni tamkar yayanki dakuke ciki ɗaya,Wanda zaki iya fadamun kowacce irin matsalarki,da damuwarki.dasauri na kallesa jin furucinsa,amma bance komaiba. “Shiyasa nace miki kimun alfarma,yanzudai kifaɗamun me kike da buƙata da baki tararba agidannan. Numfashi naja,nace.”babu komai danake da buƙata,akwai komai na amfani agidannan. “Um,um maryam kidaiyi tunani,kada kiji kunya ko nauyin sanar dani.shiru nayi nayan sakanni,sannan nace hijabaine,kawai abunda zance ina bukata.murmushi yayi, “Ashe ƙanwar tawa malamace,tom shikenan insha Allah zansiyo miki. Inashirin yin magana hajiya ta shigo falon.gabanane yayanke ya fadi,tsoro me tsanani ya kamani,ina tunanin kozatamun fada akan ganina tare da ɗanta.Amma ko kallona batayiba, sema fara’a data fara yiwa ɗanta. “A’a my son,bakatafi aikiba har yanzu. Shafa kansa yayi yace. “mommy yanzu nake shirin ƙarasawa.” ya faɗi hakan yana mikewa. “Sekadawo ɗan Albarka,adawo lafiya, Allah ya bada sa’a.” “Ameen” ya’amsa yana fice daga falon.kamar batasan dani agurinba ko kallon inda nake batayiba,ta maida hankalinta akan kallon television. Gajiya dayi da zaman na mike dankaina,cikin sanyin jiki na nufi ɗakina.ledar daya bani,na ajiye a kan mudubi,na fito nafara kwashe kayan kan dinning ɗin da sukaci abinci,na kai kitchen nafara wanke_wanke. Zuciyata cike da tunanin maganarmu da me kirkin gidannan……….

A department dinsu,driver yayi parking motar.da sauri ya fito ya buɗe mata bayan motar. Cikin izzarta ta fito daga motar, tana yamutsa fuska,tana kallon kowa ɗai_ɗai,wani kallon banza tayiwa drivern,tace”saura kuma idannatashi nayita jiranka. Rankwafar da kansa yayi,insha Allah hajiya baza’ayi hakaba.wata uwar harara ta wurga masa,tana Jan dogon tsaki.tayi wucewarta.duk inda ta gifta se’ankalleta.masu Neman suna se magana suke mata.Wanda ya mata tadaga masa hannu,Wanda be mataba kuma ko kallonsa batayi. Wani guri ta ɗan samu ta tsaya ta dakko wayarta ta danna kiran kamal. “Hello kamal ina school fa.kamal daya gama shirinsa tsaf,ita kawai yake jira yace. “ohk babbar yarinya ganinan just 5 minutes. Abokinsa dake gefensa yadubesa yace. “Kamal kardai kacemun haryanzu kuna tare da babbar yarinya ƴar gidan alh.menasara. dariya kamal yayi irinta yan duniya yace,muna tare abokina, yarinyar taki barina,sedaifa shegen wayone da ita,har yanzu taki bari inshiga gidan dadinta.sedai kawai mu taɓe juna tatashi tayi gaba. “Kai abokina amma karako iskanci duniya,yanzu kai duk duniyancinka amma kakasa yimata dabara,dalla malam ko reaping dintane kayi. Waro ido kamal yayi, “kai sokake a daureni kenan,kamanta waye ubanta akasarnar,kabarni da ita,nikadai nasan gadar zaren danake hada mata da kanta zata bukaci inyi sex da ita. Dariya abokinsa yayi yabasa hannu suka tafa. “Kaimafa kamal baka da dama, nasan dama bazaka ƙyaleta haka kawaiba. “kaidai bari kawai abokina,bari naje karta gaji da jirana,kasanta yar rainin hankalice.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button