
MALLAKIN
????
ZAINAB USMAN KUMURYA
FARIN JINI WRITERS ASSO…..????
~Free novel~
Bismillahirrahmanirrahim
1️⃣0️⃣
…………Ajiye wayar tayi jikinta har rawa yakeyi tsabar murna,araina nace gaskiya hajiya Tana ji da wannan baƙonnata dazezo,tunda nazo,gidannan bantaɓa ganinta cikin farin ciki makamancin wannan…..katsemun tunani tayi ta hanyar kiran sunana.da sauri na’amsa mata tare da bata dukkan hankalina. “Zo ki ɗan tayani wani aiki a kitchen, ta faɗi hakan tare da miƙewa.nima miƙewar nayi nabi bayanta….
Hajiya gwaggo,tunda maryam tatafi taketa murna ta kusa zama hajiya, ko,kewartama batayiba.200,000 duk wata banda kuɗin da zata ɗinga sakata tana sato mata.ai ita kam taji daɗin wannan abu. Tunɗaga soron gidan zaka tabbatar gidan yayi babban rashin me kula dashi,saboda yanda zakaci karo da datti da uban tilin wanke_wanke a tsakar gida.gwaggo bata komai tunda maryam tatafi,tasa ayi mata cikiyar me aiki har yanzu shiru.
Yauma kamar kullum,se wajen goma na safe tatashi daga bacci,ba sallah balle salati,bakinta kawai ta kuskure.ta dawo ta haɗa shayinta,dama tana da ruwan zafi a flaks, da bredi ta fara ƙasuma,Tana cikin ci taji ana sallama. Da sauri ta mikƙ ta boye biredin harda lullubewa Tana goge bakinta dan kar agane tanacin wani Abu.Amsa sallamar tayi Tana fitowa tsakar gidan,wata ƙawartace ta suka Daɗe basu haɗuba.waro micimicin idanta gwaggo tayi waje,cikin mamaki tace. “Amina yau kece agidannawa. Amina data tsaya kawai Tana ƙarewa gidan kallo tace. “Nice ladi. “maraba,marabanki shigo mana kika tsaya daga waje kamar wata baƙuwa.
Bayan sun gaisa Amina ta dubi gwaggo tace, “ladi,naga gidannaki kamar bashiba,nasaba idannashigo gida inganshi fess,gwanin sha’awa, har sha’awar gidannan nakeyi, idannazo.amma yau naganshi kaca_kaca nayi zatonma kin tashine,wasune a gidan.dariya gwaggo tayi tace. “Ai bake kaɗai bama duk Wanda ya shigo gidannan,haka yake cewa. Memun aikince batanan. “Allah sarki,ni ina shirin tambayarkima ina maryam ɗin,Dana shigo bangantaba.nan gwaggo ta kwashe labarin komai tabawa Amina. Baki buɗe take kallon gwaggo,yanda taga ko’ajikinta. “Ke yanzu ladi,maryam ɗin kika bayar aikatau,Bakya tunanin abunda zeje ya dawo,bakisan inda aka kaitaba,kedai kawai kinbayar da ita.ta mutu ko tayi rai badamuwarki bace.dariya gwaggo ta ƙarayi, “ke Amina,sana’afa takemun ai ni banki maryam tayi shekara 20 Tana wannan aikinba,har addu’a nakeyi Allah yasa karta samu miji nan kusa,ballema tayi aure,tabar aikinnan…..
***********
“Saleemat,wai bazakici abincinnanba seyayi sanyi,numfashi saleemat ta sauke tace. “Umma banajin wata yunwa a halin yanzu,kewar maryam ta cikamun zuciya,hankalina yakasa kwanciya da tafiyarta aikinnan. Kujerar tsugunno,umma ta dakko ta dawo gaban saleemat ta zauna. “Haba saleemat tunda maryam tatafi kin kasa kwantar da hankalinki,addu’a yakamata kiyi mata bawai kiyita damuwaba. “umma ai dolene indamu,kinsanfa maryam da zurfin ciki,gata da haƙuri kodama Tana fuskantar wata matsala bazata faɗa manaba,ni kuma jikina yana bani bata jin daɗi aduk inda take. “A’a saleemat,banason kina cewa haka insha Allah maryam Tana cikin kwanciyar hankali.daƙyar umma ta samo kan saleemat taci abinci,domin tun ranar data dawo tatarar da mummunan labarin,tafiyar maryam shikenan taketa damuwa. Itama umman daurewa kawai takeyi amma zuciyarta cike take da zullumi……
**************
Aiki sosai mommy tasakamu,domin kuwa bani kadai bace ta karo wasu mata guda 2 Wanda bansan subama a gidan.Amma karfin aikin ita takeyin kayanta.Abinciccikane kala_kala,da kuma kayan snacks. Duk akan mutum ɗaya.sekace Wanda mutum 20 zasuzo. Hajiya ta fita naji masu aikin suna gulma. ɗayace ta dubi daya tace.”Al_mustapha ikon Allah,ai ina ganin yanda hajiya taketa hidimarnan nasan shine zedawo domin ko alh.ze dawo bata masa irin wannan hidimar. “Hmmm,kedai bari salame hajiya Tana matukar ji da wannan ɗannata,tamkar shikadai ta haifa. “Ai ni naji daɗin dawowarsa,yanzu zakiga yaran gidannan sun nutsu,mundena kwana da kidaden banzan da suke samana. Nidai kawai spring ross ɗin,da hajiya ta barmun naci gaba soyawa,gaba ɗaya maganganunsu baganewa nakeba.
Tun wajen 11,muke aiki se daf da la’asar muka gama.sosai nagaji tubus.sonake kawai na watsa ruwa na kwanta na huta.duk da inajin yunwa amma nayi matukar gajiya.
Ina fitowa ɗaga kitchen suhailat na shigowa falon, seda zuciyata ta buga saboda tsoronta,amma ko kallona batayiba ta nufin gurin mommy ta rungumeta Tana tsallen murnar dawowar yayanta.ƙara rungumeta itama mommy tayi Tana dariya.ɗakina na wuce ina mamakin wannan murna da mommy da suhailat sukeyi akan dawowar wannan bawan Allah,kai zanso naganshi.hijab din jikina na cire,na fara zuge zip din rigata.daƙarfi aka buɗe kofar ɗakina.Dasauri na kalli bakin ƙofar suhailat ce ta shigo,babu sallama. Atare zuciyoyinsu suka buga.saboda nidai nasan ba alkhairi ne ya kawotaba. Ita kuma suhailat saboda tsananin mamakin ganin dirin jikin da Allah yayiwa maryam. “Kutmar haka yarinyarnan take da surar jiki me kyau.suhailat ta faɗi hakan aranta.wani baƙin ciki,da hassadane ya mamaye zuciyarta.yanzu duk yadda takeji da kanta,amma wannan ƴar matsiyatan ta fita kyan ƙira.jibi wani uban shap tamkar ita tayiwa kanta,ga manya_manyan nonuwa tsayayyu.munafuka shiyasa kullum take fama da hijabi,wata tsanar maryam ce ta ƙara lulluɓeta.ni kuwa rigata na fara kokarin mayarwa cikin sauri saboda har takai ƙasa,dan ma da under wear da vest ajikina,amma duk da haka banjo daɗiba data ganni ahaka.wani mugun kallo ta wurgomun Tana hararata. “Ke dabba! Kije ga kayana can ki wankemun.cikin ladami na’amsa mata da “toh”.duk da Kalmar dabba,data kirani dashi ya matukar bakantamun rai,nakasa sabawa da muzantanin datakeyi.idanuwanane ya cicciko da kwalla,kokarin mayar da ita nayi,na juya na nufi toilet,bayan ta fice ɗaga ɗakin.
Cikin 10 minutes nayi wankan, shiryayawa nayi,sallar la’asar na tayar.seda na idar na nufi ɗakin suhailat. Itama time din fitowarta kenan ɗaga toilet Tana daure da towel iya Rabin cinyarta ya tsaya,da’alama wanka tayo. kunyar ganinta nayi ahaka,duk kasancewarta mace ƴar uwata,amma aganina hakan bedaceba.juyawa nayi zan fice naji muryarta ta dakamun tsawa.”gidan uwar waz aki? Juyowa nayi kaina akasa ina wasa da yatsun hannuna. Cigaba tayi da maganarta cikin faɗa. “Tun yaushe naje na kiraki amma se yanzu zaki zomun,saboda tsabar iskanci kema kin waye kinzo kinfara cin daula,dama shi talaka be iya samun guriba. “Kiyi hakuri aunty suhailat,wanka nayine.nafaɗi hakan cikin sanyin murya. Dariya naga takamayi tamkar wata sabon kamu,da mamaki nake kallonta. Karasowa gabana tayi tanamun wani kallon wulakanci. “Wanka,wankafa kikace,ahakan kikai wanka kina fama da tsami da warin dauda,ke dama dena wankan kikayi dan ba fita kikeba.”Dall,ni wuce kimun abunda nasaki wawiya kawai nonsense. Jikina a matukar sanyaye na wuce zuwa toilet dinnata,zuciyata cunkushe da baƙin cikin kalamanta. Aƙasa na hango pants dinta da bra dinta,girgiza kaina nayi cikin takaici, ga gurin saƙale kaya amma bazata saƙaleba,sedai ta zubar a ƙasa tsabar sakarci,daga yanayin suhailat irin matannanne da babu abunda suka iya. Kwashe kayan na farayi ina zubawa a bucket. Saboda nafi ganewa wankin bucket akan na washing machine. Ina ɗaga wai pant dinta naga jini,da sauri na yardashi cikin ƙyanƙyami,araina nace kobatasan ta hadamun dashiba,domin wannan abun ai sirrin mutum ne,ina ƙara daga wani shima naga jinin harma ya fara bushewa. Matsar dasu nayi gefe zuciyata harta fara tashi,na wanke mata bra din na shanya,na fito.har lokacin Tana gaban mudubi,tanata shafe_shafe towel din jikinta ya kunce ya kusa faɗuwa,amma ko’ajikinta. “Aunty suhailat nagama” batare data kalleniba tace. “Barina na duba nagani koya fita,dan idan befitaba sekin sake.tsayawa nayi kawai bance komaiba. Kusan 5 minutes sannan tatashi ta nufi toilet ɗin. dasauri naga ta fito ta ƙaraso gabana”Kan ubannan,kagamun matsiyaciyar yarinya ahakan kikecemun Kingama,shikuma wancan dakika warefa uwarkice zata wankemun.runtse idona nayi,wlh harga Allah nagaji da zagin da takemun. “kiyi haƙuri aunty naga da najasa ajikinsu ne,kuma…wani wawan mari ta tsinkamun. “Lallaima yarinyarnan harni kike faɗawa da najasa,nufinki dai bazaki wankemunba.to meye marabarki da najasar,to bari kiji shi abunda kike cewa nasaja yafimun ke daraja agurina domin shi daga jikina yafito.dan haka kiyi sauri ki shiga ki wankemun,kafin na saɓa miki kamanni. Hawayene kawai yake bin kuncina,duk kuwa da yanda naso mayar dasu amma seda suka zubo.Marin datamun bemun zafiba kamar yadda ta dangantani da najasa.inaji ina gani haka nakoma nafara wanke mata,gani Allah yayini da ƙyanƙyamin wannan abun.nawama ƙyanƙyaminsa nakeyi balle na wani.ina wankewa ina kuka,kukan abubuwa da yawa.ga wani mahaukacin tashi da zuciyata takemun.Allah,Allah nakeyi nagama karnayi mata amai a toilet. nakara jawa kaina wata masifar. Ina gamawa na fito ko kallon inda take banyiba,saboda raina yayi matukar baci,muzantar tayi yawa. Dan kawai ubangiji ya halittoka a talaka,seka zama wulakattacce da kai da banza duk ɗayane a wurin mutane. Da gudu nakarasa ɗakina saboda aman dayaketa tasomun,Allah ma yaso babu kowa a falon.sosai nayi aman,duk da bawani abun kirki acikina,tunda rabona da abinci tun breakfast.kuskure bakina nayi,na fito na kwanta.ina maida numfashin wahala.tare da takaicin wannan wahalalliyar rayuwar danakeyi ta ƙasƙanci,bansan sanda wani baccin wahala ya kwasheniba dama da tarin gajiya ajikina…….