
Karfe 5 saura gaba ɗaya ƴan gidan sun hallara domin zuwa taro babban yaya,suhailat anci kwalliya kamar ba gobe,cikin wata red gawn me adon black,wadda ta matuƙar kamata jikinta se rawa yakeyi acikinta,tayane kanta da wani Dan karamin veil black,tayi kyau sosai tamkar ka saceta.farin ciki da murnar datakeyi yau baze misaltuba,kwana 4 dinnan dabayanan jitake tamkar sati 4. Tayi matuƙar kewarsa. Haidar da zannurain kuwa bawani farin ciki sukeyi da dawowarsaba,saboda ze katse musu jin daɗi.dan fitar nan dasukeyi ta ɗare ze katse musu ita.mota biyu sukayi,ɗaya mommy da suhailat ne abaya,se kuma driver a gaba.ɗayar kuma,haydar ne yake driving se zannurain a front seat,baya kuma faruq da sadiq. 4:55 pm,a filin saukar jirgi na malam aminu kano,ta musu.
Dafe zuciyarsa yayi saboda tsananta bugu datake masa,Wanda besan daliliba, ahankali yake sakkowa daga matattakalar jirgin janye fa trolly ɗinsa,idanuwansa ya lumshe saboda shakar iskar garin mahaifarsa da yayi,yana jin farin ciki sosai aransa,na dawowarsa gida kano ta dabo tumbin gwiwa tafiya ya farayi cikin gentle dinsa,fuskarsa babu fara’a kamar koda yaushe.su mommy suna tsaye suna baza ido ganin anata fitowa.suhailat ce ta fara hangoshi. Taɓo mommy tayi,”laaa mommy kinganshi ya fito.” Kamar yaji metace shima ya kalli inda suke,bazasu iya jira yaƙarasoba,hakan yasasu nufar inda yake.tunda yafito yan matan dake gurin suke binsa da kallo,cike da burgewa kowacce tanaji aranta dama wannan hadaddan guy din yazama mallakinta.murmushi yasaki kadan,saboda hango yan’uwansa kuma guɗan jininsa sun nufo garesa.da gudu suhailat ta karasa garesa ta fada ƙirjinsa,cikin tsananin murna da doki.shima beyi ƙasa a gwiwaba,ya mata masauki a faffadan kirjinsa,tare dasa tausasan hannayesan yazagane bayanta. Wata nannauyar ajiyar zuciya suhailat ta sauke,lumshe idanuwanta tayi Tana shakar daddadan kamshinsa. Saboda tsabar jaraba,har yanayinta ya fara sauyawa,shafa bayansa tafarayi tama manta a inda suke. Daidai lokacin su mommy suka karaso,raba suhailat yayi daga jikinsa wadda ta kasa magana, da hannu yake amsawa yan uwansa,welcoming din dasuke masa,hugging dinsa sukayi one,by one. Mommy kamar ta maidashi ciki,haka takeji. Duk da baifaɗaba,amma fuskarsa ta bayyana yana cikin farin ciki,sadiq ne ya karbi trolly dinsa suka nufi mota.hannun suhailat ya kama,wadda taketa kallonsa tamkar zata cinyesa,ya matukar yi mata kyau,ya kara wani fresh. duk da fuskarsa tayi fayau alamun ya ɗan ji jiki.Hannunta ya murza,tare da ɗage mata gira,yayi mata alama da hannunsa alamun yadai yaga tayi shiru. Lumshe idanta taƙari tare da lasar lips dinta. Kwantar da kanta tayi ajikinsa,batare da tayi maganaba.saboda itakaɗai tasan metakeji jinta datayi,ajikinsa.ahaka suka ƙarasa motar, front seat yashiga sukuma suna baya kamar yadda sukazo.mommy se tambayoyi take masa,akan ciwonsa,da’abunda yake damunsa. Atakaice yace mata zazzabine….
Direct part ɗinsa ya nufa,duk da mommy taso yaje part ɗinta amma yace mata seya huta zezo.dole haka tasa ƴan aiki suka kwashi kayan data shirya masa zuwa part ɗinsa. Mommy dakanta ta haɗa masa ruwan wanka yashiga.kafin ya fito duk sun fice daga part ɗin,domin sunsan halinsa bayason hayaniya,musammanma daya kasance yau ya dawo.bayan ya ɗauki wasu mintuna ya fito,shiryawa yayi cikin ƙananan kaya,wayarsa ya dauka ya fito falonsa. dinning ya nufa koze samu abunda yake buƙata,amma beganshiba.tsaki yaja,kobi takan liyafar da aka shiryamasa beyiba,ya koma ɗakinsa,text yayiwa mommy akan yana bukatar coffee….
Wata mahaukaciyar yunwace tatasheni ɗaga bacci,toilet na shiga na wanke bakina sannan na fito zuwa kitchen, ina addu’ar Allah yasa babu kowa a falo. Amma kash!,addu’ata bata karɓuba dukansu suna falon amma banda mommy. Suhailat tana ta tsokanar su yahaydar akan yayanta ya dawo, su kuma sunata kukkumbura. Kamar na juya na koma,sekuma naga rashin dacewar hakan tunda sun Riga dasun ganni. Kaina akasa na fara tafiya cikina na kiran chiroma.sannu na musu,amma ko kallo ban ishesuba,yayasadiq ne kawai ya amsamun. Ina shiga kitchen mommy tana fitowa hannunta ɗauke da wani basket me matuƙar kyau,ban kalli mene acikiba,saboda hankalina yanaga aɗɗa’ami. Kafin nayi magana,mommy tarigani. “Yawwa maryam dan kaiwa my son wannan,part dinshi yana gaban namu daga right side dinki,idan kin fita.kiyi sauri dan Allah Dan bayason jira, dama tunanin me kaimasa nakeyi su salame duk sunyi part ɗinsu, su suhailat kuma duk sun gaji……✍️
BY
zeey kumurya
ABUNDA KA SHUKA………
(shizaka girba)
MALLAKIN
????
ZAINAB USMAN KUMURYA
FARIN JINI WRITERS ASSO…..????
~Free novel~
Bismillahirrahmanirrahim
1️⃣1️⃣
………….Wani magidancine Wanda zekai kimanin shekara 40. zaune a wani hadaddan restaurent,waya yakeyi.daga bisani kuma yasauke wayar yana wani munafukin murmushi.wata matashiyar budurwace ta shigo restaurant din tana sanye da wani red din Less,da adon baki ajikinsa.ta yafa mayafi black,hang bag din hannuntama black ce.black beauty ce tana dan kiba.gurin magidancinnan ta nufa,sallama ta masa tare da zama akujerar dake fuskantarsa.murmushi dauke a fuskarta. “Barka da zuwa P.A “barkanka da warhaka me girma MD dadina dake P.A bakya jinkiri idan ankiraki shiyasa nakeson aiki dake.dariya P.A tayi,ai dole kaganni da hanzari me girma,MD. Kasan ance idan kaji kira samune. mikewa tsaye yayi tare da zura hannunsa duka acikin aljihunsa. Maimunatu! Yakira ainihin sunanta. “Na’am MD” kinsan meyasa na kiraki wajannan,girgiza masa kai tayi alamun a’a. Murmushi yakarayi yace” ayanzu kiran gaggawa ya riskeni oga mustapha yadawo garinnan,ayau sabanin da dayace zeyi sati biyu.bamusan dalilin dawowarsaba amma munsa a bincika mana.matsowa yayi daf da ita,wani aiki mukeso ki mana akan oga mustapha,maimuna karki sake wannan damar ta wuceki idan kika yarda zaki yimana wannan aikin,kinada babban rabo na makudan muliyoyin kudi,idan kuwa akayi nasara a aikin,zaki samu ninkin abunda muka baki a farko. Cikin Neman Karin bayani tace”wanne irin aikine wannan me girma MD. dariya yayi yace. “P.A kenan bazan fada miki aikinba sekin yarjemun zakiyi. Shiru P.A tayi na wasu mintuna kafin ta numfasa ta fara magana. “Me girma MD,bazan ki tatakaba,amma a gaskiya banason nayi abunda ze cutar da oga mustapha, saboda tsananin son da nake masa,da kuma halaccinsa agareni. Kafin yazo wannan ma’aikatar lokacin mu yarane na can kasa,kuma shuwagabannin wannan kamfanin alokacin azzalumaine,mun azabtu a wajensu. Amma zuwan oga mustapha, yacanza mana matuka,mutum ne shi me adalci,dakuma tsaiwa akan aikinsa.tasanadinsa yanzu gani a matsayin P.A dinsa. Dariya MD,ya kyalkyale da ita. “Haba P.A, kada garin Neman gira kirasa ido,kada kizo daga baya kiyi bawan ba kanin. Sanin kankine oga mustapha yana da mata agida,yar uwarsace kuma kowa yasan ita ze aura.sannan kuma duk bayanin da kikeyi na oga,ya miki halacci karki manta duk tare yamana,amma ki sani a rayuwar nan ta yanzu kowa kansa yasani,dan haka kibar batun wani oga,kawai ki kama aiki,Wanda ta sanadinsa zakiyi arziki Mara yankewa. Aikinnan ba nawa bane shima nasakani akai. Kallonsa takeyi tamkar meson karanto wani Abu a fuskarsa. “Nima MD banason tufkar dana dade inayi shekara da shekaru nayi kuskuren dazata warware gaba daya. Gashi kuma naji na kwadaitu da son wadannan makudan kudi daka ambata. Zama yayi ya tsiyaya lemon dake kan table din gabansa. Kurba yayi yace. “Ina mai tabbatar miki bazakitaba dana saniba a wanna aikin,aikine daya kunshi manyan kasarnan,dayan kasuw.,kekuma naga ke amintacciyar oga ce shiyasa nasakoki aciki.kedaice zaki mana abunda muke bukata. Kada kiyiwa kanki azanci,idan kingama shawara ki sameni gobe a office idan antashi,sena jiki. Yana gama fadar haka ya mike ya dauki mukullin motarsa da wayarsa yayi gaba.binsa kawai P.A tayi da kallo harya bacewa ganinta…….