Uncategorized

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE HAUSA NOVEL

        *************

Ai Jinayi tamkar nadora hannu aka na kurma ihu,saboda yunwar danakeji harwani jiri_jiri nake gani.gashi kuma mommy ta hadani da aiki,kuma bani da damar bijirewa.cikin sanyin jiki na karba basket din,na juya nayi waje.suhailat na ganina ta mike,”mommy yazakibawa wannan abar ta kaiwa yaya coffee,kinsanfa yaya da kyankyami,idan takai masa dakyar idan zesha.kuma kinsanshi befiyason karikican kowanne irin mutaneba,balle ita dabata san tsarinsaba.bari na kaimasa da kaina.mommy dake bina abaya tace. “Kiyi zamanki my daughter nasan ze karba,banason kina wahala da yawa yanzufa kika gama korafin kingaji.badan tasoba ta koma ta zauna.tana zabgamun uwar harara. Cigaba nayi da tafiya zuciyata na kuna,kafata har hardewa takeyi,se hada hanya nakeyi.tunda nazo gidan yaune nafara fitowa farfajiyar gidan.tsayawa nayi ina bawa idanuwa abinci,nama manta da wani sauri da’akace inyi.wasu shuke_shuke da fulawoyi da suka zagane gidan sunfi komai burgeni.ahankali nake tafiya ina kallon ko’ina,nayi tafiyar 5 minutes na iso wani part kamar yadda hajiya tace daga part dinta seshi. “Ya Allahu” na furta a fili saboda tunkafin na shiga part din nasan ankashe masa dukiya,yaci uwar na hajiya a kyau da tsaruwa. Tamkar da zinare aka ginasa,saboda wani sheki da gininsa yakeyi. Kamar part din hajiya,shima seda nahau step me matattakala 4. Nanfa ake yinta,wata irin koface wadda bantaba ganin irintaba,banmasan ta ina zan budeba.in komane in sanar da hajiya kokuma inyi yaya? Na tambayi kaina.kusan 2 minutes,ina tsaye ina sakawa da kwancewa. se Allah yajehomun da wani bawan Allah,danaga ya tunkaro inda nake.dama tunda nazo gurin naganshi zaune akan kujerar roba daga gefen part din.

Murmushi yamun nima na mayar masa. “Yan mata da alama gurin oga kikazo ko? “Ehhh na amsa masa. “Ohk,nine babba acikin yaransa na gidannan,bejira mezanceba kawai naga yatsaya agaban kofar,kawai gani nayi kofar ta bude da kanta,bin bayansa nayi da sauri nima nashige,muna shiga falon naga ta rufe kanta. “Yawwa yanmata,nasan abunda ya tsayar dake kenan daga yanzu idan kikazo haka zaki dingayi zakiga ta bude,ki hau kan steps dinnan zakiga falo yana ciki,idan kuma bayanan kiyi knocking dakin dakika gani na farko a falon.godiya na masa sosai yasakai ya fice. Suman tsaye nayi saboda se lokacin nagama karewa falon kallo. Banyasan yazan misalta muku tsaruwa da kyawun falonba,kokuma kayan ciki,kawai Ku kissima da kanku.wannan wane irin mutum ne da komai nasa na dabanne a gidannan, wani kugi da cikina yayi yasani yin azamar hawa benen domin nayi sauri na kaimasa sakon nakoma naci abinci,ga lokacin sallar magriba ya gabato. Tasbihi kawai nafarayi araina lokacin dana shiga falon saman,ga wani sassanyan kamshi dayake tashi,Wanda ya mun kamar nasanshi,ko kuma na taba jinsa. Aradu aka barni a falonnan akace in zauna,ko abinci bazan nema,kallonsa zantayi yana debemun kewa,saboda tsaruwarsa. Wani lumtsumeman center carpet na taka,Wanda ya mamaye tsakiyar falon.baya cikin falon hakan yasa nanufi dakin da Adam yace na kwankwasa.tunda natashi daga bacci naji zuciyata tana dan harbawa,amma ina kusantar dakinnasa senaji bugun ya tsananta.

Tunda yayiwa mommy text ya koma bakin gado ya zauna,zaman jira. 5 minutes yajira yaji shiru, dafe mararsa yayi datake dan masa ciwo kadan_kadan.shiru shiru bega ankawo masa coffee dinma,gashi yariga ya saba idan beshaba bayajinsa daidai.har mintuna ashirin suka shude baga ankawo masa.shi mutum ne dabaya maimaita Abu idan yafada yafada kenan,hakan yasa be kira mommy ma, yaji dalilin dayasa ba’akawo masaba. Ammafa ransa harya fara baci.lumshe idonsa yayi tare da cize lips dinsa na kasa. Ahankali nafara knocking kofar dakin. Tsaki yaji jin ana knocking, abunda abude yabar kofar,kuma kofar idan tana key mutum yana ganewa.(????????????sorry guy,ta babangidan batasan wannan tsarinba,tukunna dai senan gaba) ko motsawa beyiba balle yayi tunanin tashi,saitin zuciyarsa datake ta bugawa kawai ya dafe. Tun inayi kadan_kadan harna farayi da karfi,saboda nafara gajiya ga yunwa na kwakular cikina.ga wannan bugun da zuciyata takemun, Wanda na alakantashi da na tsorone kawai,domin ni kaina nasanni da shegen tsoro tamkar farar kura,ga kuma abunda akacemun akansa.dafe kansa yayi cikin tsananin bacin ran,wanne shashashanne yake buga masa kofa haka,tamkar ze ballata,ko kuma yasa masa ciwon kai. Cikin zafin rai ya mike ya nufi kofar,jin anki dena bugun,zuciyarsa na bugawa tamkar zata fasa kirjinsa ta fito. Bude kofar yayi. “Hasbunallu wanimal wakil, ya hayyu ya kayyumu. t nafara karantowa a fili saboda arba danayi da wani kyakkyawan halitta,bugun zuciyatane ya tsananta,runtse idanuwana nayi atunanina gamo nayi,amma ina kara budewa nakara ganinshi,ya kuramun wasu fitinannun idanuwansa wadanda sukasa jinin jikina tsinkewa.kasa nayi da idona,ina tasbihi ga ubangijin dayayi wannan kyakkyawar halitta. Nandanan jikina yafara rawa,basket din dake hannunane ya subuce ya fadi kasa,jikake tasss! flaks din ya fashe ruwan coffee din ya fara malala akasa,se turiri yakeyi,da sauri yayi baya saboda jin ruwan coffee din akafarsa………✍️

kuyi manage da wannan, na shiga shagalin bukukuwa ne,wannanma dakyar nasamu na muku,ko editing banyiba.kuyi hakuri please.????????????

BY
Zeey kumurya

ABUNDA KA SHUKA………
(shizaka girba)

MALLAKIN
????
ZAINAB USMAN KUMURYA

FARIN JINI WRITERS ASSO…..????

~Free novel~

Bismillahirrahmanirrahim

1️⃣2️⃣

…………..Tashin hankali da rudani da matsanancin tsorone suka ziyarceni a lokaci guda. “Nashiga uku, na furta a fili saboda ganin ya kone bayan zubar masa da coofee harda konasa nayi,nasan yau mommy idan ta kamani sedai wata baniba.ganin yanda ya zauna abakin gado,amma kunar tamkar ba’ajikinsaba kawai dai ya lumshe idansa.tunanin inda zan samu ruwa na farayi.dan karamin fridge me kyau na hango a dakin,da sauri na nufeshi na dakko ruwan roba me sanyi a ciki. Kafin na karasa garesa kawai naga cikin azama ya janyoni na fado saman gadon,duk da kan gado na fada amma naji jiki.saboda yanda ya warbar dani.wani matsanancin tsorene ya kara rufeni,nandanan jikina ya kama rawa.da sauri na mike daga kwancen danake,saboda tunawa da inda nake.kokarin sakkowa nayi,senaga Ashe kwalbar flaks dince data tarwatse a gabana na kusa takawa shiyasa ya janyoni. Ajiyar zuciya na sauke nadan saci kallonsa.kokarin zuba masa ruwan nayi a kafarsa,amma wata uwar harara ya jefomun. Dasauri nayi kasa da idona,cikin rauni na fara magana,kwalla harta taru a idona. “Dan Allah,kayi hakuri wlh bansan haka zata faruba kayi hakuri dan Allah.nakarasa maganar da fashewa da wani matsanancin kuka,saboda na rasa mafita,bansan hukuncin daze dauka akainaba.

Dafe kansa yayi cikin tsananin takaicin wannan yar kauyen yarinyar.tazo ta dameshi,sannan kuma ta zubar masa da cofee harda konasa.yanzu kuma tazo ta dameshi da wani banzan kukanta.ita kuwa mommy ina ta samu wannan yar shilar yarinyar. duk maganar dana masa kodagowa beyi ya kalleniba,balle nasakaran zemun magana,araina nace kodai kurmane,babu shakka ma kurmane, afili nace,” Allah sarki ga kyau ga kudi amma Allah ya tauyeshi ta wani fannin.cikin sanyin jiki na tashi,na dakko abun share daki,domin su bada tsintsiya suke amfaniba nikuma bansan sunan abunba. Flaks din daya tarwatse na fara sharewa,a wani Dan basket me kyau na zuba,Wanda nake kyautata zaton shine na zuba sharar dakin,saboda kowanne daki na gidan da akwaisa. Hadadden toilet dinsa na nufa Wanda kyawunsa da tsaruwarsa ya zarce duk wani toilet dana gani agidan. moffer na dakko na goge coffee din daya zube Tass,na kara yayyafa ruwa na goge. Ajiyar zuciya na sauke bayan naga dakin ya koma need kamar da.satar kallonsa nayi,naga shima niyake kallo,Wanda na kasa fassara kallon kona menene.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button