
Tura baki gaba,Aliya tayi tafara cin abinta. (Hajiya saudart kanwar alh menarasace,uwarsu daya ubansu daya,dama su uku iyayensu suka haifa,daga alh menasara,se baban suhailat sekuma auta hajiya saudart,wadda suke kiranta da aunty. ) ita kanta aunty,maryam ta burgeta, gani daya data mata tagane yarinyar tana da nutsuwa, da hankali. ina cikin shanya kayana najitashigo dakin da sallama,dama abude nabar kofar. Har bakin toilet din takaraso rike haba tayi tace, “sannunki da aiki, dakanki kike wankin,bada masu wanki agidanba kidinga basu mana” “ai wankin babu yawa,kayan dana cirenefa” “lallai agaisheki,nikuwa kinganninan na tsani wanki da wanke wanke arayuwata.” Murmurshi na mata kawai,ina mopping toilet din bayan nagama shanyar. Aliya bata damu da shirun da maryam tamataba, tace. “Nikuma. Maryam aunty suhailat tananan tunda mukazo banji duriyartaba” “tananandai dazuma kafin kuzo tana falo,ammadai yanzu bansaniba kota fita” nabata amsa ina fitowa daga toilet din. Zama mukayi abakin gado,tabe baki aliya tayi tace, “hmmm,kilanma tana jinmu taki fitowa,shiyasafa dakyar na biyo aunty gidannan, saboda kwata_kwata bama shiri da ita, kingadai babanta da auntynmu uwarsu daya ubansu daya,amma seta dinga daddaga mun kai,gata da masifa,amma ina zuwa naganki senaji dadi dannasamu abokiyar hira.” Dariya nayi danyadda take magana ta matukar bani dariya,”wow kinga yadda kika kara kyau kuwa,dakikayi dariyar nan,ga dimples dinki sunkara lotsawa,dama nice ke.” Murmushi kawai namata, nace. “Kemafa kyakkyawace amma.kindage seyabon kyauna kikeyi” “hmm,mekyau inda babu kyawawa irinkuba.” nanma murmusawa kawai nayi.Hira tashiga yimun tana bani labarai, harta fadamun daga kaduna suke,tanata bani labarin kawayenta dana school, lokaci daya naji tashiga raina, baburuwanta gaskiya, tamkar wadda muka Dade da sanin juna, nalura daga ganinta bazatayi wulakanciba,bata duba matsayina agidanba,tasaki jikinta dani tanatamun hira,nima naji dadin haka,kobakomai zata debemun kewa kafin suntafi…….
_______
MUSTAPHA
_______
Har sallar azhar yanata faman aiki, sallah ce tasheshi dama kuma ya kammala, abunda yakeyi. Yunwace yaji tana nukurkusarsa,dinning ya nufa inda maryam tajere masa abinci, yahada tea yasha sannan yatsakuri sauran kayan break din,dahar time din dazafinsu basuyi sanyiba,saboda flaks din dasuke ciki masu rikon zafine sosai, yaci. Sedayaje sallah yadawo sannan yayi wanka ya shirya cikin kananun kaya, Wanda suka matukar yimasa kyau. Direbansa yakira,yazo ya daukesa zuwa kamfanin dayake aiki,domin yanason yaduba wasu ayyukane. Time din da mommy takirashima yanacan,shiyasa beyi picking call dintaba, sedaga baya yaga missed call dinta,text ya turamata,akan yaje office ne,yana sauri shiyasa beshigo yamata sallamaba sedai idan yadawo. Dama ka’idane kullum idan yadawo daga sallar asuba,baya komawa part dinsa seya fara zuwa yagaida mommy,yaga kuma yatatashi,sannan yakoma part dinsa. Yanaganin text din da suhailat ta masa kala_kala naban hakuri,karantawa kawai yayi amma bemata reply ba. Shifa Sam bayajin son suhailat aransa,bayan na yan’uwantaka, saboda shi sam bakalar macen dayakeso bace suhailat. Suhailat tanada rawar kai,da hayaniya. Shikuma yafison mace silent Mara hayaniya. Kawai yana tausayin suhailat ne yanda take tsananin sonsa, shiya shima yake nunamata yana sonta, kuma sannan iyayensuma suna farin ciki da soyayyartasu. A’da Sometimes yana tunanin anya kuwa yanada lafiya,kamar kowanne namiji, saboda bayajin wani feeling kokadan ajikinsa, amma kuma segashi yanzu harciwo feeling yake samasa,tundaga ranar da accident yahadasu da yarinyar dabesan ina zegantaba, gashi asanadiyyarta komai nasa yana kokarin canzawa,danma yadage da shan magunguna yanzu, dabesan halin dazeshigaba. Watsar da tunanin komai yayi daga ransa yacigaba da abunda yakawosa. Se kusan magriba yabaro office din,sanda ya shigo gida ana kiraye_kirayen sallar magriba, beko shiga cikin gidanba,ya nufi masallaci.
Part din mommy yanufa bayan an idar da sallah,shida sauran yan’uwansa dasuka hadu a masallaci. Babu kowa a falon duk suna daki, aunty ce tafito daga dakin dake jikin na mommy,Wanda ana take sauka idan tazo gidan. Da mamaki mustapha yake kallonta,danbesan tazoba. Shikuma su sadiq sunsan tazo harsun gaisama. Fadada fara’a aunty tayi tace, “sannunka boy seyanzu kadawo kenan agogo sarkin aiki,tunda nazo nake cikiyarka aunty atika tacemun katafi office, kai weekend dinma bazaka hutaba” shagawabe fuska yayi yace, “wai auntynah haryanzu boy dinnan baze fita daga bakinkiba, nifa bansan sunan” karasawa aunty tayi kusa dashi ta kamo hannunsa tana fadin, “sorry my son,nariga nasabane,zomuje kazauna kahuta dannasan ka kwaso gajiya” su haidar kuwa dasuke kallonsu se guntse dariya sukeyi, indai aunty tazo gidan seta tsokanesa tace masa boy, saboda dayana yaro haka akecemasa,daya girmane yayi cancel din sunan. Zama sukayi akan kujera,yana gaisheta. Aunty macece,me kirki da saukin hali,gashi tana jansu ajiki,musammanma mustapha, haka kawai takejin wani Abu agame dashi me kamar tausayi,Wanda batasan dalilin hakanba. Mommy ce tadawo falon itama. Daga baya kuma suhailat tashigo, se satar kallon mustapha takeyi, shikuma daga gaisuwar daya amsa mata,bekara mata maganaba, cigaba da hirarsu sukayi da aunty.
Adakina mukayi sallah,da muka idarma hira Aliya tacigaba damun, araina mamakinta kawai nakeyi yanda bata gajiya da magana,gaskiya Allah yahore mata baiwar surutu. Aunty ce dakanta tashigo dakin da sallama, amsa mata mukayi ta Dora da fadin, “sannu Aliya,kinzo kincikata da surutu, narasa irinki aliya kogajiya da magana bakyayi” murmushi nayi nace, “babu komai aunty hirafa mukeyi” “kai aunty, nifa bani da surutu,kawaidai banaso inga nazauna shirune” “naji nidai,kitaso kigaisa da yan’uwanki kowa ya hallara afalo.” Zunbur aliya ta mike tayi bakin kofa, nikuma ina zaune ko motsawa banyiba. Juyowa aliya tayi tana kallona, “kitaso muje mana tare maryam” “A’a aliya kije kawai zanfito anjima” takuramun aliya tayi,dole na mike muka fita tare. dashi nafarayin tozali,hakan yahaddasamun wata faduwar gaba,bantaba ganinshi yana murmushi ba seyau naga yanayiwa aunty,dimples dinsa duka kumatu biyu sun lotsa abun sha’awa,akodayaushe idan na kallesa karamun kyau yakeyi,yanzumma hakance ta kasance. “Oyoyo yaya…..muryar aliya ta katsemun tunani, sekuma naji itama tayi shiru,kallonta nayi naga ta wani nutsu harta da tafiyartama ta canza. Dariya naga su yaya sadiq sunsaka mata,ashesu sunsan dawar garin, ganin mustapha ne yasata nutsuwa ba jiri,ta wani koma salihar gaske,dantasan halinsa farinsani. Shikuwa ya wani tsare gida, yana latsa waya. Akasa muka zauna,kusa da aunty muka gaishesu.
Daga gaisuwar bankara cewa komaiba,na sunkuyar da kaina kasa, zuciyata na luguden bugu kamar kodayaushe idan mukayi close dashi,ga daddadan mayen kamshinsa gaba daya ya mamaye falon,se lumshe ido nakeyi ina sauke ajiyar zuciya akai_akai saboda dadin kamshinnasa .itama Aliya duk shegen surutunta shiru tayi,su yaya sadiq ne suketa hirarsu shidasu aunty,shima ogan shiru yayi yacigaba da latsa waya. Suhailat se kallonsa takeyi tamkar zata hadiyesa. Kiran sallar isha’ine ya tarwatsa taron,dama a takure nake da zaman,nina fara mikewa nashige daki,ina kallon suhailat tana bina da wani mugun kallo. Aliyama biyo bayana tayi tana fadin, “nida dodo” dariya na tsuntsire mata saboda yanda tayi maganar tamkar taga dodon gaske. “Allah kuwa maryam,bakiga nayi tsitba aitun watarana a gidannan Inata zuba,shikuma yana zaune kawai yana kallona, sedaga bayane yakirani gabansa ya murdemun baki,harkuka nayi saboda azaba,tundaga ranar idan yana guri kodogon numfashi banasonyi” murmushi nayi ina nufar toilet nace, “maganinki yayi ai” “hmmm,danshirunnan danayi bakina haryafaramun tsami yasin” “kai aliya banda sharri” “bawani sharri gaskiyace, ai gaskiya aunty suhailat zatayi kokari, danzama da yaya musty se hakuri, kodayake shine maganinta ai,tunda itama bata da kirki” alwalata nafara ina fadin,”kekadai dai”.