Uncategorized

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE HAUSA NOVEL

Koda muka idar da sallah bamukoma faloba, aliya tamakure akarshen gado sekashe murya take tana waya da saurinta,kamar ba itace me karadinnanba. Nidai kayana nahau kwasowa daga toilet na dinke nasasu a cikin cover. Ganin har 9 tayi nafita domin musu serving abinci,dannaga wayar aliya bata kare bace. Aikuwa Ina fita kuku,nata jera abincin akan dinning,sukuma dukansu kamar dazu suna zaune a falon.

Yana gamawa mommy ta umarci kowa dayataso suci abincin. Dukansu suka hallara amma banda oga dayaketa aikin latsa waya, aunty ce ta dubeshi tace, “Muhammad yanaga baka tasoba” satar kallonsa nayi,tasowa yayi kawai becemata komaiba. Ajiyar zuciya nasauke,nafara serving dinsu,dauriya kawai nakeyi amma nikadai nasan halin da zuciyata take ciki, gawani mahaukacin bugu da takemun. Aliyace tafito daga daki, tayani serving din tayi mukarasa,aunty da yaya sadiq ne kawai suke mana sannu. Juyawa nayi zantafi,aliya dake kokarin zama tace,”A’a maryam ina zakije kuma?” “daki zankoma” “wanne irin daki kuma maryam,kizo kici abinci” cewar aunty data karbe zancen. Babu Wanda yayi ko tari acikinsu,harnadawo na zauna,se suhailat daketa kallonmu tana tabe baki nida aliya. zuba abincinnayi,jujjayashi kawai nakeyi amma nakasa ci, saboda bansababa duk senaji natakura,gashi duk dagowar dazanyi idon yaya sadiq nakaina. Aunty ce tamun magana akan naci abincin mana,dole nadaure nafara tura abincin tamkar inacin magani. Mustapha ne yafara tashi aunty namasa tsiyar haryanzu yananandai da rashin son cin abincinsa. Murmushi kawai yamata yafice,daga falon gabadaya. Daya bayan daya suka dinga tashi,nikuma atare muka tashi nida aliya. Dakina nakoma toilet nashiga nayi fitsari nadawo na kwanta,dan yanayin danakejin kaina baze misaltuba,inajin aliya ta shigo tanamun magana,wai ita anan zata kwana,shiru na mata dan ina fama da zuciyatane, har gwanin iya sata yasaceni bansan sanda ta kwantaba……..

Washegari gari lahadi,yau ma basu tashi da wuriba,nima danayi sallah komawa bacci nayi,se wajen 10 natashi,aikina nayi kamar kullum danasaba tare da taimakon aliya. Yanayin dana kwana dashi yabarni,sedaifa duk abunda nakeyi tunanin mustapha ne,manne acikin raina. Yauma acikinsu nayi Karin kumallo,bisa umarnin aunty kamar jiya,amma yau naga ogan bezoba. Abunda yake bani mamaki,duk abunda aunty tace,mommy bata musu kota hana,balle sauran yayangidan. Suhailat kam na lura tafi kowa jin haushin hakan,danbanda harara babu abunda take aikamun dashi harmuka tashi. Namaci sa’a banmaci zagiba,itama naga kwana 2 duk tayi wani sukuku da ita. Munagamawa na tattara kayan,nakai kitchen mukayi wanke_wanke sannan mukayi wanka. Bayan munshirya aliya tatakuramun wai dole senazo munje garden din gidan,hijabina na zunbula muka fito. Mommy ce zaune afalo tayi bakuwa,bakuwar irin manyan matannanne, masu ji da gayu kamar mommy, taci kwalliya da gwalagwalai se tashin kamshi takeyi. tunda muka fito takafeni da ido,gaisuwar damuke matama seda mommy ta tabota sannan ta amsa,mudai ficewarmu mukayi. Maida kallonta bakuwar tayi akan mommy tana zauke ajiyar zuciya bayan su maryam su fita, gyara zama tayi tace. “Kekuwa atika ina kika samo wannan dankwaleliyar yarinya haka,gaskiya yarinyarnan tamun wlh, nidazakimun wani taimakoma dakin bani ita natafi da ita,tamun koda 2 weeks ne namaida maitata……..✍️

kuyi hakuri da dogon jira, amma yanzu insha Allah zakudinga jina yanda ya kamata

BY
zeey kumurya
ABUNDA KA SHUKA………
(shizaka girba)

MALLAKIN
????
ZAINAB USMAN KUMURYA

FARIN JINI WRITERS ASSO…..????

~Free novel~

Bismillahirrahmanirrahim

1️⃣6️⃣

………..Bata fuska mommy tayi tace,”haba baraka wannan yar yarinyar nawa take, kedai wlh maitarki tacika yawa.” Murmushi bakuwar da mommy takira da baraka tayi tace, “hmmm,ninasan menagani atika,irin wadannan yaran,sunfi dadin harka” tabe baki mommy tayi ta kawar da kanta gefe batace komaiba. Ganin haka yasa baraka sako wata hirar daban, amma ta kudirce aranta kotayayane seta lashi zumar maryama,dan yarinyar ta mata, daga ganin farko data mata….

Garden din gidan da tafiya, danni gurin dayakema bantaba zuwaba,banmasan dashi agidanma. Gurin ya matukar yimun kyau, da burgeni. Ga wata ni’imar iska dake kadawa ahankali,me kwantar da zuciya. Kujerun roba, aliya ta kwaso mana, domin mu zauna. Amma kafin na zaune seda nadan zagaya naga gurin, gaskiya masu kudi sun huta,iya kanshi gurinma ya isa yadaukewa mutum kewa. Zama nayi ina sauke ajiyar zuciya. “Kyan zaman gurinnan ace mutum yana tare da masoyinsa, susha soyayyarsu seyafi dadi.” Cewar aliya. Murmushi namata,kawai na lumshe idona, narasa meyasa fuskar mustapha takemun gizo a acikin idona,hotonta kuma yayi tsaye kyam acikin zuciyata. Cikin dariyar keta aliya tace, “um’um,kaga su maryam manya kintafi tunanin naki masoyinkenan” numfashi na sauke tare da bude idona,ahankali ina hararar aliya nace, “banson iskanci,ni ina naga wani masoyi” dariya takara kwashewa da ita tace, “fadanma ko kyau bemikiba, gwaramadai hararar” banza na mata. Ita kuma tashiga bani labarin saurayinta, korar duk wani tunani nayi daga zuciyata mukasha hirarmu da aliya. Kiran sallar azharne yatadamu muka koma cikin gida…

Suhailat ce, zaune a falon sama na part din mustapha, shima yana zaune, se latse_latsen waya yakeyi. yauda kanta ta kaimasa breakfast dinsa. tazone ta kara bashi hakuri, dan har yanzu be sakko mataba.yanuna mata dai ya hakura,amma yaki sakar mata fuska. Se satar kallonsa takeyi tana hadiyar yawu, sotake tajita kwance akan faffadan kirjinnasa tana shafa lallausar fatarsa amma ba dama, danbataga fuskar hakanba. Kwana biyunnan duk atakure take, sotakema ta fita anjima gurin kamal amma kuma tana tsoron wani sabon fushinnasa. “Pls my love am sorry again” ta fadi haka cikin marairaicewa, tamkar zata fashe da kuka. kallonta yayi, sekuma ta bashi tausayi. Sakin fuskarsa yayi daga dauren datake. Amma bece mata komaiba. Ajiyar zuciya suhailat ta sauke, ganin ya hakura duk da bece mata komaiba amma tasan ya hakura. Hira tashiga yimasa, irinta masoya tare da kalailameshi da kalaman soyayya,hardai tasamu suka shirya suka koma kamar da…..

Aunty kuwa bayan sungama breakfast part din masu aiki ta wuce gurin talatu,domin itace abokiyar hirarta idan tazo gidan, amma basa wata doguwar hira da mommy. Bayan sungaisa aunty ta dubi talatu tace, “talatu,naga wata sabuwar yarinya a gidannan ita kuma daga ina, aka samota,naga batayi kala da sauran masu aikin gidannanba?” gyara zama talatu tayi,tabawa aunty labarin maryam atakaice. Cike da tausayawa aunty tace, “kai wasu mutanen son zuciyarsu yayi yawa, bandahaka aikamata yayi ace kamar wannan yarinyar tana makaranta tana karatu yanzu,amma shine aka turota aikatau,gata yarinya me hankali da nutsuwa, itama aunty atika narasa meyasa take kaunar yara kananu a aikatau, dan wani abu yataba faruwa dakai can abaya, shikenan kuma yanzuma seyakara faruwa, gata da yara samari bafata dai akeba amma bata tunanin wani Abu ya faru, musamman yanzu da zamani ya lalace ga kuma sharrin shedan” “Allah dai ya kyauta” kawai baba talatu tace, Aranta kuma cewa tayi, “danma bakisan meyake faruwa agidan bane” wata hirar suka kama daban…

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button