Uncategorized

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE HAUSA NOVEL

Lokacin damuka koma part din duka yaran gidan,suna zaune a falo,bakuwar mommynma ta tatafi,yaya musty ne kawai babu a falon se suhailat da aunty. Aliyama zama tayi sukasha hira, dan jiya bata samu damar hira dasuba,nidai daki na wuce nayi sallah ta, sedaga baya aliya tashigo itama tayi. Haka muka karasa wunin yau cikin farin ciki nida aliya. nidai zuwansu aliya gidan yamun dadi,aunty ma data dawo part dinmu, ta kirani tamun tambayoyi akan rayuwata, tare da mun nasiha. Godiya na mata sosai,seta tunamun da ummansu salima. Dan itama kullum cikin yimun nasiha takeyi. Yau kam kwata_kwata banga ogaba, kuma kosaudaya mommy bata aikeni part dinsaba,senaji dadin hakan saboda maganar rigarsa tananan daram araina. Amma kuma a wani bangaren na zuciyata,senaji ina kwadayin ganinsa.????????

Washegari tun asuba dana tashi,bankoma bacciba nayi ayyukana,saboda yaya sadiq yacemun kafin yawuce office zamuje school, kamar yadda yamun alkawarin. murna da farincikin danake ciki yau baze misaltuba, waiyau nice zankoma makaranta da sunan cigaba da karatu, gaskiya yaya sadiq yataimakeni, Allah ya biyasa kawai. Kafin 8 munje makarantar office din principal mukaje, akamun tambayoyi akan karatuna. Alhamdulillah na amsa yanda yakamata, Matsalata kawai rashin iya turanci,hakan yasa yaya sadiq yace zedaukar mini me lesson yadingamun da yamma. Kudin duk da aka bukata yaya sadiq, yabiya. Atake aka bani, uniform da littafan karatu. Ss2, aka kaini, amma bazan fara zuwa yauba, se gobe idan Allah yakaimu, nace zanfara zuwa.

Da murnata nashigo daki, bayan yaya sadiq ya saukeni agida ya wuce aiki, aikuwa yau yasha addu’a da godiya me tarin yawa agurina. Rukunkume, aliya nayi saboda murna. Itama tayani tayi mukayi tayin murnar tare. Seda muka gama murna sannan na dubeta nace, “Aliya gaskiya yau ina cikin farin ciki sosai, gashi makarantar ta burgeni da’alama kuma ana karatu sosai” “ai gaskiya makaranta da dadi maryam, zaman gidan haka badadi, seki dage kiyi karatu karkibawa yaya sadiq kunya” murmushi nayi cikin jindadi nace, “insha Allah aliya zanyi karatu sosai” “haka akeso Allah yataimaka.” “Ameen” auntyma tatayani murna sosai, takuma mun addu’ar nasara. Hakama baaba talatu danaje nasanar mata. Mommy kam, danaje nanunamata karba tayi itama tasamun albarka, dana mata maganar aikin gidan, seta kafin natafi nayi abunda zan iya kawai, idannadawo na karasa, godiya na mata, nakoma naciga da shirye_shiryen fara zuwa school gobe……..

__
MUSTAPHA
__

Tunda yadawo daga sallar asuba shima be koma bacciba,abubuwansa ya karasa ya shirya cikin kananun kaya,wadanda suka matukar amsarsa. Yayi kyau sosai,kamalarsa da cikar zatinsa sunkara fitowa. Karfe 7/15 kamar kodayaushe yagama shirinsa tsaf, ko breakfast beyiba, yadau briefcase dinsa, seda yabiya part din mommy yaymata sallama ita da aunty, sanna yafito. Direbensa yana tsaye abakin mota yana jiransa, yana hangoshi ya taho cikin girmamawa yana gaisheshi tare da amsar briefcase din hannunsa, ya bude masa mota yashiga,shima yazagaya ya shige, yatada motar suka fice, bayan ya gaisa damasu gadin gidan.

Yau kam ma’akaitar duk ma’aikatan sunzo da wuri,sabanin sati dayan dabayanan kowa kashin kansa yakeci. Cikin takunsa nakasaita ya fito daga motar,direbansa na biye dashi abaya rike da briefcase dinsa. Ma’aikatan dake kaikawo,aharabar ma’aikatar se kwasar gaisuwa sukeyi. Mikewa sakatariyarsa tayi cikin girmamawa tana kwasar gaisuwa,tare da amsar briefcase dinsa daga hannu direba takai masa cikin office dinsa. Bayan yazauna akan kujerane yatura sakatariyarsa ta kira masa P.A. tare suka dawo office din. P.A sewata karairaya takeyi da yauki, amma kobitakanta beyiba,bayan sallamar daya amsa mata. hankalinsa yana kan duba wani files dayakeyi. Tari P.A takamayi ba kakkautawa, dagowa yayi yana kallonta, tare da yimata sannu. Kanta kawai ta iya daga masa, har tarin ya lafa, sekuma yakara turniketa ba kakkautawa. Hankali atashe mustapha ya mike zaune, atunaninsa asmartace tatashi, nuni take masa da hannu ga fridge din dake office din, alamun yabata ruwa. Dasauri cikin tausayawa ya nufi fridge din, ya dakko mata ruwan yabude yakawo mata ya kafa mata abaki. Seda tasha kusan Rabin, robar sannan ta janye bakinta tana sauke ajiyar zuciya, tare da maida numfashi. Yunkurin tashi tayi, sekuma tayi luuu zata fadi kasa, dasauri mustapha yatarota jikinsa, cikin azama,yana jera mata sannu. wal_wal haske ya bayyana a office din, nadaukar hoto……✍️

wlh banajin dadi sosai, mura na damuna,kuyi hakuri da wannan guntun page din, gashi ina fama da matsalar ido, amma zakujini gobe insha Allah. Your du’a is needed????????

BY
Zeey kumurya

ABUNDA KA SHUKA………
(shizaka girba)

MALLAKIN
????
ZAINAB USMAN KUMURYA

FARIN JINI WRITERS ASSO…..????

~Free novel~

Bismillahirrahmanirrahim

1️⃣7️⃣

………..Hankalin mustapha gaba daya yana kan P.A, hakan yasa be lura da abunda ke faruwaba. bubbuga bayanta yahauyi ahankali,saboda tarin daya kara sarketa harta samu ta dawo nutsuwarta,tarin ya tsaya. Taimaka mata yayi takoma kan kujera, se lumshe ido takeyi, tanajin dama su dawwama tana kwance a kirjinsa, tana shakar daddadan kamshinsa. wani sonsa da kaunarsane yakara ninkuwa aranta, harzuciyarta ta fara kokwanto akan anya kuwa ta kyauta masa, mutumin daya tsamota daga duhun talauci, daga rana zuwa inuwa, amma yau da ita aka haka baki domin cutar dashi, anya kuwa tayi wa kanta adalci….daddadar muryarsa me cike da kasaita takatse mata tunaninta. “Dama kinsan bakida lafiya kika fito aiki,?” Ya fadi haka yana kallonta. Cikin muryarta data dan dashe tace, “lafiya kalau natashi, yanzune kawai naji tarin” “ohk, bari nakira doctor yadubaki” “no, sir, base kakira doctor ba, yamatsayamun tarin” ta fadi haka cikin sauri. Kallonta yayi nawasu sakanni, yadan tabe baki yace, “Alright, Allah yakara sauki” “Ameen, thank u so much sir” be’amsa mataba sewata takarda daya mika mata, karba tayi taduba, sannan ta mike ta masa sallama ta fice, tana tafe tana waigensa………

Kafin yamma nagama shirina tsaf na zuwan school gobe, nagoge uniform dina, najera books dina a school bag dita. Jinake kamar na zuko gobe tadawo yau saboda zumudi, aliya se dariya takemun tana tsokanata. Tunda nazo gidannan babu abunda yasani farin ciki kamar wannan, yanzu saurana islamiyya, itama inason komawa. Allah sarki, yar’uwata salima,nasan itama idan taji wannan labarin zatayi farin ciki sosai, umma ma haka. Kewarsu naji tacikamun zuciya, masoyan kwarai kenan. Kaina dake tsefe, aliya tasani wankewa, aunty ta rangadamin kitso, dama nayi kwanaki dakan atsefe. Godiya nayiwa aunty sosai bayan tagamamun. “Wow mairo, kinga yanda kitsonnan yayi kyau, gaskiya kina da kyan kitso gaki da gashi, ga tsawo da cika,gashi baki sidik, kedai kinji dadinki komai naki mekyaune.” Cewar aliya tana shafa kitson. Murmushi nayi kawai mekama dana yake, kamar yadda aliya take yabona haka kullum salima ma takemun. Tabbas nikaina nasan Allah yayimun baiwa ta kyawu, amma idannatuna bani da kyawun nasaba, senaji wani kunci da daci yaziyarci zuciyata. kyau ko dukiya bashine cikar kamalar mutumba, ASALI shine abun tunkaho da alfahari ga kowanne dan Adam, amma ni bansan nawa asalinba, banmasan ina zannemesuba. Kwalla ce ta jikamun ido, kasa nayi da kaina ina kokarin mayar da ita dan karsu aunty sugani, Amma hakan beyiyuba seda wani hawaye ne dumi ya ziraromun. arikice aliya ta hau tambayata “lafiya maryam, meyafaru meya saki kuka, ko baki da lafiya ne?” shiru namata ina share hawayen fuskata, nikadai nasan halin danake shiga idannatuna wacece ni. Cike da tausayawa aunty take kallon maryam, daga ganin yarinyar akwai abunda ke damunta acikin zuciyarta. Ganin aliya ta matsamata da tambaya, ita kuma tayi shiru se aunty ta dubi aliya tace, “Aliya kowanne dan’adam yanada sirri nasa nakansa arayuwa, sanin abunda kedamunta ayanzu bashine abun bukataba, addu’a kawai zaki tayata da ita, akan Allah yayaye mata koma menene” gyadawa aunty kai, aliya tayi cikin gamsuwa. dafa kafadar maryam aunty tayi tace, “kiyi hakuri maryam da rayuwa, a duk yadda tazo miki, kikuma godewa Allah. kowadakika ganshi datasa irin kaddarar, kuma komai me wuce wane arayuwa, na dadine kona wuya.” Nasiha sosai, aunty tayiwa maryam me kwantar da hankali dasanya nutsuwa. sosai naji dadin tunasarwar da aunty tamun, har radadin da zuciyata kemun naji ya ragu,sakar jikina nayi muka koma kamar da, muka cigaba da nishadinmu nida aliya……..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button