
Mustapha yau bedawo dawuriba daga office, saboda meeting din dasukayi bayan antashi daga aiki. A matukar gajiye, yadawo ga kuma yunwa datake nukurkusarsa, dan yau dabinone kawai acikinsa dayaci a office, sekuma coffee dayasha. Yana dawowa wanka kawai yayi, yaje yayi sallar magriba, seyanzu kuma daya dawo, shine yakira mommy tasa akawo masa abinci. Yana zaune a kujerar dake pacing kofar shigowa falon, suhailat tana gefensa, wai tazo ganinsa yau gaba daya bata ganshiba, tayi kewarsa. Da sallama dauke a bakina nashiga, ina sauke wata boyayyiyar ajiyar zuciyata, saboda daddadan kamshinsa daya ziyarci hancina. wata irin bugawa zuciyata tayi saboda ganin suhailat a falon, tawani kura masa ido se kallonsa take. Sekace ta samu TV, shikuma yanata sana’ar tasa latsa waya. Tunda nazo gidan nasan da labarin auransu, amma bantaba ganinsu tare irin hakaba, wani Abu naji yaziyarci zuciyata. Karasawa nayi cikin falon, gaishesu nayi, shidai naga sanda ya amsamun, ta hanyar motsin da kyawawan labbansa sukai, lokacin dana saci kallonsa. ita kuwa suhailat wani banzan kallo ta bini dashi. Ajiye kayan nayi, akan dinning da Sauri, na juyo da niyyar fita, haka kawai naji banji dadin ganinsu tareba, komeyasa oho?, kumama banmanta da rikicinmu na riga dashiba.. Se’a lokacin na lura Ashe aliya bata shigo falonba, makalewa tayi a corridor. “Ke!” Naji muryar aunty suhailat, nasan dani take dan haka natsaya cak. “Ke wacce irin mahaukaciyace, kuma dabba, jaka Mara lissafi.” Cikin jin zafin kalamanta na juyo ina kallonta amma bance mata komaiba. Kawai jinayi ta tsinkamun mari, batare dana mata lefin komaiba, dafe kuncina nayi, idona na cikowa da kwalla dama kwana 2, bansha wulakancintaba. Cigaba da magana tayi cikin karaji, “matsiyacin ubanki ne zezo yazuba masa abincin, dazaki fice baki zuba masaba, banza me kamada alade, har ina miki magana kinamun shiru, kinwani tsareni da wadannan idanunnaki tamkar na mujiya” muryana na rawa ina shirin fashewa da kuka, nace, “kiyi hakuri aunty suhailat, bansan yanzu zeci abincinbane, shiyasa banzuba masaba” “aidama tunda ke jakace baki da kwakwalwa, kwakwalwarki ta kifice,bazaki saniba, stupid kawai idiot,m”……..Marin da mustapha yasakarmata a kuncine, yasata hadiye maganarta, batare data shiryaba ba………✍️
jiya nace zanmuku posting,bansamu dama bane, mura ta addabamun sosai, seyau nasamu na muku. Nagode da addu’oinku. JUMA’AT MUBARAK
BY
zeey kumurya
ABUNDA KA SHUKA………
(shizaka girba)
MALLAKIN
????
ZAINAB USMAN KUMURYA
FARIN JINI WRITERS ASSO…..????
~Free novel~
Bismillahirrahmanirrahim
1️⃣8️⃣
………Ba suhailat kadaiba, nikaina na matukar firgita da Marin daya mata. Cike da tsantsar mamaki tare da al’ajabi suhailat ta dafe kuncinta, tare da dago kanta ta zuba masa idanuwanta cikin son tabbatar da shidinne take gani agabanta, kuma haryadaga hannu ya mareta, abunda koda tana karama betaba mataba, anya kuwa ba mafarki takeba. Mustapha dake tsaye yana jifanta da wani kallo shima cikin tsantasar bacin rai, jikinsa har tsuma yakeyi, idanunnan sunkada sunyi jajur. Yariga yasan halin suhailat na rashin da’a da mutunci, amma betaba tunanin abunnata yakai hakaba. cikin tsananin bakin da takaici suhailat tace, “yanzu yaya akan wannan…… “shut up!, stupid. Get out”!!!!!! Yafadi haka cikin tsawa da karaji, tare da nuna mata kofa da hannunsa. baya naja dasauri saboda matukar tsorata jikina harya fara tsuma,tsawar tasa har cikin tsakiyar kaina najita. Juyawa tayi tafara tafiya fuuuu tamkar zata tashi sama har bangaje maryam tayi, ta fice daga falon,hawayen bakin ciki nazirara daga idonta,tasan halinsa idan taki fita,seyayimata abunda yafi mari agaban wannan banzar yarinyar. Maida kallonsa yayi ga maryam, ya galla mata wata uwar harara. Cikin kakkausar murya yacemata. “what are you waiting for?” Aikafinma yakarasa najuya nafice dagudu, zuciyata na luguden bugu. Komawa kan kujera yayi yazauna, yana maida numfashi. Kansa dake saramasa, saboda yar hayaniyarnan yadafe, zuciyarsa na masa zafi. Kokadan bayason yaga anacin zarafin dan’adam da Allah yabasa daraja, da kima,irin haka. Lumshe kyawawan idanunsa yayi tare da kwantar da kansa ajikin kujera,cikin kunar zuci……
A corridor mukayi kicibus da aliya,kankameta nayi inasakin kuka me tsuma zuciya,Wanda bansan dalilinsaba,kalaman suhailat dai,nasaba dajinsu,marinma bayau tafara munba,kawaidai hoton yanda nashigo nagansu yaki bacemun daga idona. Rungumeta aliya tayi tsam ajikinta tana dan bubbuga bayanta, cikin tsananin tausayawa, duk da batasan meyafaruba, amma tasan halin suhailat, gashi kuma taga itama ta fito a fusace tana hawaye. Kusan 2 minutes sannan tazareta daga jikinta, tare da kama hannunta suka fara tafiya batare datacemata komaiba.
Mommy da aunty dasu haidar ne zaune a falo, amma banda yaya sadiq. Tamkar ancillota sukaga tafado falon dagudu tana kuka. Dasauri mommy ta mike tatareta cikin rudewa take tambayar, “lafiya,meyafaru?” Kowa na falon zuba mata ido yayi yana kallonta. Bata bata amsaba, se kankameta datayi tana sakin kukan banza. Girgizata mommy tahauyi, cikin dimuwa tana fadin, “daughter wai menene, kinsa hankalina yatashi kowani abunne yasamu my son,pls tell me what happen?” Cikin kuka suhailat tace, “mommy wlh yau sewaccan bakar yarinyar yar matsiyata tabar gidannan,tunda bagidan ubanta bane.” “Wacce yarinyar kenan daughter?” Mommy tatambayi suhailat tana dagota daga jikinta. Gabadaya hankalin mommy idan yayi dubu yatashi, saboda ganin yartata na kuka, Wanda tamanta rabon dataga tana kuka irin haka, ba mommy kadaiba sukansu su haidar hankalinsu atashe yake, duk sunyo kanta suna mata tambayoyi,cikin rudewa. Aunty dai kawai tsayawa tayi tana kallon ikon Allah,duk da itama hankalinnata yadan tashi,danda farko da suhailat tashigo tadauka wani mummunan abunne yafaru. tsagaita kukan suhailat tayi cikin shan majina tace, “mommy yaya nefa yamareni akan na mari waccan banzar me aikin” zaro ido waje mommy tayi tace, “shi son dinne ya mareki dakansa, akanme to, akan wanne dalili?” hada karya da gaskiya suhailat tayi tafadawa mommy, wai maryam dince tamata rashin kunya,kuma tahada mata makirci har yayan ya mareta. Jinjina kai mommy tahauyi cikin bacin rai, tace. “Aidama talaka be iya samun guriba, tana gidan ubanki tanacin arziki shine zata miki haka, lallai kan mage yawaye.” Haidar ne ya amshe zancen dacewa, “kyaleta mommy, zata shigo tasameni, zatasan akanta aka mari suhailat, sena rama mata Marin akanta” zama mommy tayi tare da dora suhailat akan cinyarta, tafara rarrashinta tare da share mata hawaye.
Adaidai lokacin mukashigo falon, wata mahaukaciyar faduwar gabace ta ziyarceni, ganinsu duka a falon, zannurain da haidar sunyi tsaye cirko_cirko, fuskarsu na nuna tsantsar bacin rai. yaya faruq kuma yana zaune, yana latsa wayar sa, tamkarma besan abunda ke faruwaba. Idonane yasauka akan mommy, tsantsar bacin rai da fushi na hango afuskarta, Wanda tunda nazo gidan bantaba ganiba, wani mugun kallo take jehomun. Kasa nayi dakaina dasauri zuciyata na bugawa da sauri_sauri dama nasan alhakalin marinnan akaina ze kare. Aunty kuwa kallonsu kawai takeyi baki bude, yanda duk suka wani rude, suna tada jijiyoyin wuya akan anmari suhailat. Tasan mustapha, tasan halinsa akan dan karamin Abu baze mari suhailat ba. Cikin sanyin jiki nake taka kafata har tsakiyar falon a matukar tsorace. aliya dake gaba tsayawa tayi ganinsu ahaka, tamkar Wanda aka aiko musu sakon mutuwa. Cikin zafin rai haidar yayi kan maryam danufin yarufeta da duka.