
Murmushi kawai na mata, cike da mamakinta ko gajiya batayi da waya. cire hijabin jikina nayi, na dakko karamun na makarantar nasaka. “Wow maryam, wlh bakiga yadda uniform dinnan ya miki kyauaba” “aike dama komai kyau yake mun” nabata amsa ina rataya jakata. “Allah dagaske nake maryam, yamiki bala’in kyau, karkijefa ki tadawa malaman makarantar hankali” hararta nayi na dauki hijab din dana cire nakara mayarwa, dangaskiya bazan iya fita hakaba, inajin kunya. Idannaje bakin get nacire naninke nasa ajaka. “Yaya sadiq nefa yakirani yanzu shinema yatasheni daga bacci, yace yana waje yana kiranki,tun dazu.” “Ohk,bari nakarasa, sena dawo, bye” “Allah yakiyaye I will miss u wlh” cewar aliya tana marairaicewa. murmushi namata nace, “nima zanyi kewarki sosai da surutunki” dariya mukasa dukanmu namata sallama, na tafi. A bakin part dinmu, naci karo da yaya sadiq, yana kokarin shiga. Cikin mutuntawa mukagaisa, yana sanarmun dama yanzu yake shirin shiga yakirani yaji shiru. Duk da hijabin dake jikina,amma seda yaya sadiq yace kayan sunmun kyau sosai. Godiya na masa cikin jin kunya. Muna tafe muna hirarmu akan makarantar, harmuka karasa parking space. Damuka shiga motane yake kara bani hakuri, akan abunda yafaru jiya, nuna masa nayi bakomai ninama manta. Duk da abun yana raina, musammanma yanayin dana baro yaya mustapha, haka kawai tun jiyan naji badadi saboda fushin dayayi, yauma da kwadayin son ganinsa natashi, inason naganshi naga halin dayake ciki. Harmukaje makarantar tunaninshi kawai nakeyi. Seda muka fara zuwa office din principle sannan akasa wata tarakani class dinmu. Yaya sadiq ma yabani kudi,tun a mota. Duk dagewar danayi bazan karbaba, nakuma sanar masa aunty tabani, amma yabata rai yace dole sena karba. Ganin ransa ya baci sena karba namasa godiya. Bansan yazan misaltamuku yanda nakejin zuciyataba ahalin yanzu, wani irin yanayi take ciki kamar nadamuwa. Amma hakan behanani yin farin cikiba, saboda ganina a makaranta a kuma aji. Ajin yankadan natarar time din dana shiga, kuma mata da mazane a ajin, duk senaji kunya ta lullubeni danni nasaba makarantarmu matane zalla,gashi nacire hijab dina, sekarami na makarantar kawai. Sallama naiwa matan dana tarar a ajin, se bina sukeyi da kallo, duk senaji na tsargu. Watace tamun magana da fara’arta ta kuma nunamun kusa da ita, tace nazo na zauna. Godiya na mata nazauna, tambayata tayi sunana nafada mata. MARYAM AHMAD ita kuma tacemun sunanta, ZAINAB ILYAS MIJINYAWA banfi 5 minutes dazamaba, malami yashigo ajin……….
Gaskiya makarantar ana karatu sosai, gashi ajin babu yawa. Wani abunnagane wani kuma banganeba, saboda matsalar turanci daba komai nake jiba. Zee mijinyawa tana da kirki sosai, da’aka fito break duk abunda banganeba ita takaramun bayaninsa da hausa,nakuwa gane sosai. Ban fita ko’inaba cake dindanazo dashi naci, itadai zee tafita. Naji dadin makarantar sosai gaskiya, banfuskanci wata matsalaba kodaga gurin sauran yan aji. Malamaima kowa yashigo seya tambayeni sunana, tare damun welcoming. Karfe 2/15 ake tashi daga makarantar. Da’aka tashi tare muka fito da zee da wasu kawayenta, bayan tabani aron books dinta nayi copy note a gida. Kamar yadda yaya sadiq yacemun direba zezo yadaukeni, hakance ta kasance kuwa. Ta gurin number motar nagane shi, saboda duka motocin gidan anrubuta MENASARA .yana bakin gate yana jirana kuwa, sallama naiwa su zee nashige muka tafi gida, zuciyata cike da farincikin yau gani na koma karatu,da yardar Allah zancika burina,dana innata.
Mintuna kalililan muka karasa gidan,dama makarantar babu nisa,koda kafama zan iya dawowa. A parking space nakara maida hijabina, danga masu aikin gidan sunata kaikawo, a makarantar ma dan babu yanda zanyine. Aunty da mommy da aliyane, zaune a falon sama. Da sallama nashiga. Atare duk suka amsamun suna kallona, dagudu aliya tataho ta rungume ni, aunty na mata fadan kardai ta kadani. Nima rungumeta nayi cikin murnar ganinta. Jakata ta karba, sannu da gida naiwa su aunty, aunty tamun sannu da zuwa da tambayata ya karatun, mommy kuwa sedai kallonnanta muka shige daki. Aliya kamar ta lasheni, dan murnar dawowata waidama tagaji da zaman kadaici. Kozama banba nashige toilet na watsa ruwa tare da dauro alwala nafito nayi sallah. Kafin na idar aliya harta kawomun abinci,da ruwa. Allah sarki aliya masoyiyar asali, komai nata idan tayi tana tunamun da salimat ne, itama haka take nunamun irin wannan kaunar. Ina cin abinci ina bata labarin school din. Bayan nagama cin abincin na dakko jakata, kudin da aunty da yaya sadiq suka bani nanunawa aliya, cewa tayi na ajiye watara zasumun amfani. Rabawa nayi nabata rabi, amma tacemun wlh bazata karbaba. Cikin jin haushinta na’ajiye kudin, na dakko littafaina na fara kwafar note, itama aliya wani ta dakko tana tayani. Rubutun dayawa, dan anyi nisa a term din. Har bayan magriba muna note din, sallah ce kawai ketadamu. Badon mungamaba,sedon hannunmu dasuka gaji muka bar note din haka gobe nakarasa. Tun dayamma yaya sadiq yakira aliya, wai yaji kona dawo gida. Banima wayartayi mukayi magana, ya tambayeni ya school din da kuma karatu. Nace masa komai lpy klu,sai godiyar Allah…..
Suhailat yau bata dawo gidaba se daf da magriba, kuma tun 9 ta fice. Saboda tabiya ta gurin kamal sunyi badakalarsu, ahakanma daurewa tayi tadawo badon sungaji,dajunaba. Tanata yamutsa fuska tashigo gidan ita adole ta gaji. Mommy sewani lallabata takeyi ita kuma tana wani narkewa. Aunty datun yamma tafara mitar dadewar suhailat din, batayi shiruba data dawo seda tatambayeta dalilin dadewarta. Cemata tayi practical suka tsayayi. Seda tayi wanka ta shirya, da nufin zuwa part din mustapha, amma aunty tahanata zuwa. Aganin aunty hakan bedaceba,yarinya budurwa taringa zuwa part din namiji, aiko uwa daya uba daya kuke bedaceba, balle su da’akwai soyayya atsakaninsu. Ran,suhailat a matukar bace ta koma dakinta, ita tamatsu aunty ta tafi saboda tagaji da takurarta, dama ita takurane da ita, a cewar suhailat fa……✍️
kuyi hakuri da jina shiru, school ce ta boyeni, se’adarennan nasamu na muku, gashinan bayawa kuma ba editing????
BY
zeey kumurya
ABUNDA KA SHUKA………
(shizaka girba)
MALLAKIN
????
ZAINAB USMAN KUMURYA
FARIN JINI WRITERS ASSO…..????
~Free novel~
Bismillahirrahmanirrahim
2️⃣0️⃣
…………Zama tayi abakin gadonta cike da takaicin hanata zuwa ganin masoyinta da aunty tayi, gashi tun tana school takirashi bedagaba kuma bebiyo bayan kirannataba, datace bazata kara kiransaba itama zatayi zuciya dashi, amma takasa zuciyarta bazata iyaba. Wayarta dake hannunta ta kunna ta kara dialing number sa akaro naba adadi,daga jiya zuwa yau. Mustapha yana zaune a falonsa yana kallon news a TV, kiran waya yashigo wayarsa, dakko wayar yayi yaga suhailat ce, dafe kansa yayi, yaga missed calls dinta dayawa kuma yace zekirata amma shaf yamanta. Rejecting yayi ya kirata. Cikin zumudi suhailat tadaga wayar danda tayi tunanin rejecting yayi badon yakirataba. Wata doguwar ajiyar zuciya ta sauke jin daddadar muryarsa ta doki kunnenta da sallama. Maimakon ta amsa sallamartasa seta samasa kukan shagwaba, lumshe idonsa yayi tare da taune lips dinsa, bayason kuka kokadan arayuwarsa kona yara bayasonji balle na mace, kukan mace yana taba masa zuciya. Fesar da iska yayi daga bakinsa yace, “autar mommyyyy”! Yanda yaja sunannata seda taji wani yarrrr ajikinta, itafa ko muryarsa taji tada mata da sha’awa take, balle kuma taganta agabansa,ita kadai tasan metakeji. Cikin kukan tace, “na’am” “menene?” Yatambayeta cikin sigar rarrashi,tausayinta gabadaya yacika masa zuciya, shima ba’asonranta yake mata abubuwa kodan tsananin sonda take masa, amma suhailat dince idan baya mata haka bazatana shiga taitayintaba. Cikin shagwaba ta fara masa korafin kira da texts datayita masa,ganin ya sakko,haryana mata magana cikin sanyin rai. Rarrashinta yafarayi, tare da mata nasiha akan abunda tayi. Hakuri tabashi tace masa tadena. Cigaba ta masa da surutu cikin jin dadi, da farincikin sun shirya, shikuma sedai kawai yabita da um, ko um’um. Hakan baya damun suhailat danta riga tasaba da wannan halinnasa. Itadai burinta yacika tundadai yasakko daga fushin dayake da ita. Damashi haka yake, wani lokacin yanada saurin sauka, wani lokacin kuma seda kyar…….