Uncategorized

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE HAUSA NOVEL

Falo muka fito nida aliya, yau kam tanacemun mu fita muyi hira bamusu nafito. dukansu samarin gidan da aunty da mommy suna zaune a falon, amma banda oga da suhailat,da yaya sadiq. Wani tunanine ya darsu a zuciyata, na maybe suna tare a part dinsa, wani iri naji, zuciyata babu dadi, Tambayar kaina nayi araina. “Wai ma mene ruwana acikin rayuwarsu danake damunkaina?” Musammanma shi mustapha danake yawan tunaninshi, kuma aduk lokacin dana tunashi se gaba ya fadi. Nakan alakanta hakan da matsanancin tsoronsa danakeji, danshi mutum ne me kwarjini, kuma ni a sanin dana masa masifaffene, gashi ya iya daka tsawa,me hautsina yayan cikin mutum. Lumshe idona nayi ina fasalto kyakkyawar fuskarshi acikin zuciyata, Wanda bansan yazan fasalta muku shiba azahiri. Narasa ina yagado wannan kyawun nasa, dan mommy dai da sauran yan gidan duka basu kaishi kyauba, amma nafi inatunanin a wurin mahaifinsa yagada, tunda shikadaine bantaba ganiba agidan. Wata doguwar ajiyar zuciya nasauke, aliya dake gefena suna hirarsu ta juyo ta kalleni da Sauri, ahankali naji tace, “lafiyarki kuwa maryam?” Bude idona nayi nakalleta nace, “lafiya ta kalau,me kika gani” girgizamun kai tayi alamun ba komai, ta juya sukacigaba da hirarsu. Hira sukeyi amma hankalina gabadaya baya kan hirar tasu, addu’a kawai nakeyi araina. Allah yakawo abunda zesa mommy ta aikeni part din yaya mustapha, dalilin fitowatama daga daki kenan,amma naji shiru yau bata aikeniba. Har ka kira sallar isha’i muna falon, ayanda nakeji araina jinake kamar nacewa mommy bata da aikene yau gurin yaya mustapha, wani irin azalzala zuciyata takemun nason ganinsa. Cikin sanyin jiki natashi nanufi dakina donyin sallah, adakinma seda aliya tatambayeni wai meke damuna,nace mata babu komai domin ni kaina bansan mezance mataba, banmasan abunda ke damuna dinba. Haka nakarasa daren yau jikina duk asanyaye, gashi bansamu damar ganinnasaba. Abincima kadan natsakura naci, yaya sadiq ma harkiran aliya yakarayi awaya ta bani, yahau tambayata wai meke damuna yaganni kamar mara lafiya, amasar dai dayace bakomai, gajiyar school ce kawai, nace masa. yanzu yaya sadiq yaragemun magana acikin yan’uwansa,tsakanina dashi gaisuwace kawai, tunda aliya tazo gidan sedai yakirata awaya Muyi magana.

Bayan mungama dinner na kwashi kayan da’aka bata na wanke. Aliya yau bata tayaniba tana dakin aunty time din danayima. Ina gamawa nadawo dakina nashiga toilet fitsari nayi tare da dauro alwala nadawo nahaye gadona nakwanta, bajimawa bacci yadaukeni dan gaskiya banajin dadin jikina, kuma jikinnawa da yar gajiya. Wajen 11 saura aliya tadawo dakin, kallon maryam tayi cikin jimami da tausayinta, danyanda ta lura da maryam irin mutanennanne da damuwa take wahalar dasu sosai. Gobe zasu koma k.d shine dalilinma dayasa ta dade adakin aunty har wannan lokacin suna hada kayansu, dukda kayannasu bawani yawane dasuba, tsabaracema meyawa saboda kowa nagidan yakawowa aunty tasa shine suka tsaya shirya kayan,dama da niyyar kwana uku sukazo, aunty tazone kawai taga yanda suke. Aliya jitayi kamar tafasa bin aunty gobe, setaji batason barin maryam ita kadai,jikinta gabadaya yayi la’asar. Cikin sanyin jiki ta tattara duk wani nata dake dakin maryam ta hade guri guda, a hang bag dinta. Dama su agogontane da abun hannunta. Kashemusu light din dakin tayi ta kwanta agefen maryam,zuciyarta babu dadi…….

Washegari tare mukayi aiki da aliya yau itama bata koma bacciba. Dayake mu biyune kafin 7 mungama komai, wanka nayi nashirya cikin uniform dina sabo, dan set biyu aka bani a makarantar. Kamar jiya yauma hijabi nadora akai nanufi dakin aunty,danna gaisheta.

Bayan mungaisa aunty tace, “toh maryam sedai ince Allah yakaddara saduwarmu,dan yau zamu tafi, kafin kidawo daga school ma muntafi” cikin matsananciyar faduwar gaba nake kallon aunty, zuciyata na bugawa, yanxu su auntyn danake kallo nakejin dadi agidannan suma tafiya zasuyi. Cikin rawar murya nace, “aunty tun yau zaku tafi naga baku dade da zuwaba?” Murmushi aunty tayi tace, “Abbansu aliya yanata kirana indawo, ga kuma makarantar aliya,nima banso tafiyarba naso jiran dawowar yaya, danyacemun yakusa dawowa amma tafiyar tazamarmun dolene” shiru nayi bance komaiba. Janyoni aunty tayi ta kwantar da kaina akan kafadarta, cikin lallami ta fara mun magana. “Karki damu kanki maryam, nanbada jimawaba zakiga nadawo, bana jimawa nake dawowa, kinji maryam tah” gyada mata kai nayi ina kokarin maida kwallar data cikamun idona nace, “shikenan aunty kugaida gida, Allah yakiyaye hanya, amma zanyi kewarku sosai” shafa fuskata aunty tayi tace, “ameen maryama muma zamuyi kewarki, kedai kawai abunda nakeso dake kidage da karatunki kikuma kula da kanki, kikara hakuri akan Wanda kikeyi agidannan, duk abunda kike bukata kuma kitambayi sadiq kinji” “tom aunty nagode sosai da kulawarki agareni.” Bakomai maryam, Allah yamiki albarka, kije kikarasa shirinki karkiyi latti, kafin kitafi kibiyo tanan zan baki sako, karki bari aliya ta tsaidaki da surutunta dannasan halinta,sarai.,seta makarantar dake” Murmushi nayi na mike nafice, zuciyata babu dadi kokadan.

Aliya nazaune a bakin hado ta rafka tagumi nashigo dakin da sallama ciki_ciki, tsayawa nayi kawai ina kallonta daga ganinta itama jikinta yayi week. Ahankali tadago da kanta ta zubamun ido, karasawa nayi bakin gadon nazauna agefenta dafa kafardarta nayi nace, “aliya Ashe yau zakutafi shine baki sanarmunba, seyanzu aunty take sanarmun” numfashi aliya tasauke tace, “kiyi hakuri maryam,aunty ce tace karna fada miki seyau,dantasan seki tashi hankalinki kikasa bacci.” “Yanxu idan kuka tafi seyaushe?” Natambayeta idona nacikowa da kwalla, kwanaki ukunnan damukayi tare dasu jinta nake tamkar mundau wasu shekaru tare, yanzu idan suka tafi shikenan rayuwar kuncin danake agidannan zata dawo,tunda sukazo ko kallon banza babu Wanda yamun agidan se ranar da abunnan yafaru saboda ganin idon aunty. Na lura duka yaran gidan suna Shakkar aunty. Banmasan hawaye yafara zuba daga idonaba seda naji hannun aliya tana sharemun, itama idonta duk yayi kwal_kwal kamar zatayi kukan. gabadaya tausayin maryam yacika mata zuciya,tasan halin yan’uwanta sarai ba kirkine dasuba,tasan maryam zaman hakuri kawai takeyi agidannan. Rungumeta tayi tsam ajikinta ganin taki dena kukan, cikin rarrashi take bubbuga bayanta. Magana tafara mata cikin rarrashi da lallami akan tayi hakuri, insha Allahu dazarar anmusu hutun school zatazonan tayi hutunnata gabadaya tare da ita. Dakyar aliya tasamu maryam ta hakura tadena kukan. Toilet nashiga nakara wanke fuskata,sannan nadawo nakarasa shirina, aliya nata bani labaran bandariya duk dan nasaki jikina. Nikuma se nuku_nuku nakeyi naki tafiya, harseda yaya sadiq yakira wayar aliya akan yana waje yana jirana. Dakin mommy naje, namata sallama,yau dakantama tace intafi karnayi latti base nayi serving dinsu ba. Kuku harya gama hada breakfast yau da wuri, diddibarmun aliya tayi na tafi dashi, dakin aunty na koma kamar yadda tace. Wani littafin addu’oi ta dakko ta bani har guda biyu, tace nadaure nadinga karantawa arana koda saudayane. Godiya na kara mata sosai, itakuma tanata kwararamun addu’oi. Har bakin motar da yaya sadiq yake ciki aliya ta rakani. Abincin dake hannunta ta mikomun tare da fadin, “to maryam segani nabiyu” karba nayi cikin sanyin jiki nace, “nagode aliya,kugaida gida Allah yakiyaye hanya” “ameen” cewar aliya tana maida hankalinta akan yaya sadiq dake zaune acikin mota amma ya bude murfin, kafafunsama suna waje. yatsaya kawai yana kallonmu da sauraronmu. “Yaya sadiq ga maryam nan, dan Allah kakularmun da ita amana karka bari ko kuda yatabata, balle kuma wani Abu yabata mata rai.” Murmushi mukayi nidashi saboda yanda aliya take maganar, yace, “baki da damuwa yarkanwata indai maryam ce zankula miki da ita fiye da yanda kike tunani.” “Yawwa yayana, maryam bye bye, semunyi waya, insha Allah zandinga kiran wayar yaya sadiq muna gaisawa, I will miss u over” da kai kawai nabata amsa, saboda ina bude baki tsaf zan iya saka kuka, daurewa kawai nakeyi. Zagayawa nayi na shige cikin motar, daga mun hannu aliya tayi ta juya tatafi,ina binta da kallo. Tada motar danaji yaya sadiq yayi yasani dauke ido daga kanta,ina sauke ajiyar zuciya. Kallona yayi dasauri sekuma yadauke kansa yayi yaja motar muka tafi. Hawayen dake makale a idonane yasamu damar zirarowa, nikuma haka kaddarata take arayuwa, duk Wanda nakejin dadin zama dashi, sena rabu dashi….. “Yasalam, maryam! Kuka kuma, kiyi hakuri pls nasan kunyi sabo da aliya Wanda dole zakiji zafin rabuwarku, amma kukan bashine mafitaba, kidena kinji” murya yaya sadiq ta katsemun tunani. Daga masa kainayi ina share hawayena. “Yawwa kokefa, duk sanda kikeson ganin aliya na miki alkawari zankaiki, ammafa idan kindena kuka” dasauri nace, “nadena yaya sadiq Allah” murmushi yayi yace toh shikenan kyakkyawa” shiru nayi bance masa komaiba, shima yaya sadiq shirun yayi har muka karasa school din. Yau kam sukuku nayi a makarantar har zee seda tatambayeni ko bani da lafiya, nace mata lpy ta klu. Koda aka tashi nadawo gida, duk senaji gidan babu dadi, saboda su aliya suntafi kamar yadda aunty tace, zama nayi bayan nayi sallah na rafka tagumi ina tunanin rayuwata, ganin tunanin babu abunda ze karamun se damuna sena tashi na dakko littafin addu’ar da aunty ta bani, na karanta, cikin ikon Allah se zuciyata tayi sanyi,damuwata duk ta ragu. Haka rayuwa take Allah baya barin wani Dan wani yaji dadi. Bayan na gama karantawa na tashi naci gaba da ayyukana………

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button