
Galala su lukman suka tsaya suna kallonsa, shikuwa yawani maze tamkar bashi yayi maganarba yacigaba da latsawayarsa hankalinsa kwance. “Haba musty bayan muguntar daka mana, kaki fadamana kanada kanwa kamar wannan,sannan yanzu kuma naganta dakaina shine zaka korarmun ita, bamugama magana da itaba” cewar fahad yana hararar mustapha, a tunaninsa maryam cousin din mustapha ce, danbata masa kala da me aikiba,kuma harwata kama yaga sunayi. Banza mustapha yamasa danyasan halin fahad dama, shiyasa ya kora maryam, danyanzu seyace yana sonta. “To namamajo, aidama tunda naga kallonta nagane inda kadosa” cewar lukman yana dariya, suma sauran dariya sukasa ganin yanda fahad ya wani kebe fuska. “Ah, karna kalleta tamunne ai, idan kasamu wannan amata ai kagama dacewa, ga kyau ga nutsuwa da kamala ga hankali, nidai gaskiya tamun zanje nasamu mommy mugana,aknta” “irinkune maso jawa mutum raini, yanzu wannan yarinyar karama zakace kanaso, to tun wurima kacireta daga ranka dan ammata miji” mustapha yafadi haka batare daya dagoba. Kallonsa suke gabadayansu yanda ya wani maze tamkar bashi yayi maganarba. Faruq ne ya amshe zancen dacewa, “mene abun raini aciki, ai irin wadannan matan inkasamesu kagama morewa” “bari kaidai abokina, katayani da addu’a kawai Allah yasa nadace agurinta, koma wane mijin da’aka mata kwaf daya zanmasa na kwacemasa ita, yan bakin ciki kuma sedai suga anayi ehe!” cewar fahad yana mikewa zuwa dinning danya debo kayan da kansa. Banza musty yamasa bece kalaba, shifa dagaske yake har cikin zuciyarsa gani yake rainine kace kanason mata kananu kamar maryam, mema zasu iya yimaka, sedai suta maka shirme,da shiririta.????????
Ina tafe ina gulmarsa acikin zuciyata, haushi duk ya isheni nikadai nasan dadin danaji sanda abokinshi yakirani, ko banza zanta kallonsa amma yanzu yamun bukulu ya koroni. A kofar part dinmu naga yaya sadiq tsaye yazubamun ido kawai yana kallona harna karaso kusa dashi. “Yaya sadiq barka da warhaka” muryar maryam ta katse masa tunanin daya tafi akanta, firgigit yadawo daga duniyar daya lula yace, “yawwa maryam ya gida ya weekend?” “Lafiya kalau yaya” “to masha Allah, anjimafa bayan la’asar me lesson dinnaki zefara zuwa” “eh yaya banmantaba aina zamuyine?” Juyawa yaya sadiq yayi yanunamun wata yar rumfa dake dan nesa damu, yace, “acan zakuyi” “toh yaya nagode sosai da dawainiyar da kakemun, Allah yakara budi yabiyaka da aljannah” “ameen, maryam,kinyi kyaufa” rufe fuskata nayi cikin jin kunya nace, “nagode” murmusawa yayi yana binta da kallo. Maryam tana matukar burgesa komai tayi kyau take masa, gawani bakon al’amari dayakeji akanta. sallama namasa na wuce ciki,bin bayanta da kallo sadiq yayi harta shige, ajiyar zuciya yasauke ya juya yatafi. A falo natarar da mommy da suhailat, araina nace, “seyanzu tatashi kenan” gaisheta nayi bata amsamunba sedai uwar harara tare da mugun kallo data bini dashi, dama jiya kafin natafi school bamu rabu ta dadiba, masifa tayitayi akan ina tafiya ina barin aiki, wai dole sedai idannagama aikin natafi makarantar ko karfe nawane, mommy ce ta tausheta shine ta hakura da kyar. Ko dakina banshigaba nanufi dakinta, na gyara mata. Gyaran dakinta yana daukarmun lokaci saboda kodayaushe kaca_kaca yake, kamar me yara kanana dabata gyara dakin. Bata kintsa komai, komai taci kota cire atsakar dakin zata barbarzar, kuma haryanzu ninake wanke mata kayan unders dinta. Bayan nagama na koma dakina nayi sallar la’asar sannan na tattara duk abunda zan bukata nanufi gurin lesson dinmu. Me lesson din haryazo, gaisawa mukayi babu bata lokaci, yafaramun. Me lesson din yana da kirki sosai, gashi da faran faran, kuma alhamdulillah nagane sosai, da kananun sentence na turanci yafaramun, yakuma rubutamun sunan wasu littattafai yace nabawa yaya sadiq yasiyomun, se wajen magriba muka gama yatafi. Danayi sallahma nayita bitar abunda yakoyamun harya zauna daram akaina.
Washegari, tun kiran farko mommy tazo tatasheni da kanta, dayake yau natashi nayi sallar dare, ina kan dadduma naji ana knocking kofata, cike da mamaki da tsoro nace, “waye?” Sai naji muryar mommy ce ta amsa, shine hankalina ya kwanta naje na bude. Sanarmun tayi na fito aikine damu yau megidan ze dawo, babu bata lokaci nabita zuwa kitchen. Aiki muka kama bakama kafar yaro, nifa har yanzu nadena mamaki, wai duk wannan kayan ciye_ciyen duk akan mutum daya akeyi, sukuma haka masu kudi suke, ina mutum zekai wannan abincin. Har gyaran gida ranar na musamman akayi, komai ankara tsaftaceshi na wanki an wanke, na gogewa an goge, gabadaya part din mommy ya kaure da kamshi, saboda turarukan da’aketa sanyawa, duk da ba’a part din ze saukaba, dannaji sanda mommy tatura aje agyara masa part dinsa. Gabadaya yan gidan kowa kaga fuskarsa cike da annuri da farin ciki take, hatta masu aiki kuwa, saboda dawowar megidan. Fara’ar dabantaba ganiba yau naganta a fuskar mommy da suhailat, se buge_bugen waya sukeyi suna fada alh. zedawo. Gaskiya mahaifi akwai dadi, yanda suke murna da rawar jiki,banga lefinsuba akan dawowarsa, inama nima zanga mahaifina, inama nima nawa mahaifin zedawo gareni, da kuwa duk wani bakin cikin dake zuciyata nasan seya yaye. Gaskiya masu iyaye araye kuma atare dasu sunji dadinsu.(Allah kabarmu da iyayenmu, kakuma rabamu dasu lafiya, Wanda suka rigamu gidan gaskiya kuma, Allah yagafarta musu. Ameen).
Se bayan azhar nasamu kaina, jikina duk yayi tubus da gajiya, ko karyawa banyiba yau,yunwa se nukurkusata takeyi, abinci nadiba naci, kadannema yasamu yashiga cikinnawa, kamshi duk yagama cikamun ciki, ruwa na watsa nafito nayi sallah, lafiyar gado nabi domin rama bashin baccin dake kaina……..
Gabadaya ahalin gidan alh.menasara yau suna cike da murna da farincikin dawowarsa gida, dan gaskiya ya jima a tafiyar dayayi. Ma’aikatan gidanma ba’abarsu abayaba wajen taya murna, domin sunsan idanyadawo kakarsu ta yanke saka. Mutum ne shi me kirki, baya kyamar talaka ko kadan, gashi da kyauta sabanin mommy dabata kyauta kokadan, shiyasa yayanta duk ita suka gado, mustapha ne kadai me wannan kyautar irintashi, se sadiq dake bimasa baya. Karfe uku jirginsu ze sauka, tun karfe 2 kowa nagidan ya shirya dan tarboshi, harda mustapha dake cike da farinciki shima, sekuma abokan alh. Menasaran dasuma zasuje tarbar tasa. 2/40 a filin airport din ta musu suna jiran saukarsa……
Cikin farin ciki yake sakkowa daga matattakalar jirgin fuskarsa dauke da annuri, lumshe idonsa yayi cikin Jin dadin shakar iskar kasarsa me albarka dayayi. Alh. Menasara kenan, mutum me cikar zati da kamala hadi da kwarjini, kamarsa daya sak da sadiq kamartasu harta baci, hatta duhun fatarsu dayane. Masha Allah kyakkyawane shima, dan har yafi mommy kyau sedai kawai ta nuna masa hasken fata. Fuskarsa dauke da fara’a yake tafiya cikin nutsuwa,iyalansa da abokanansa suna ganinsa suka karaso garesa, da gudu haidar da zannurain suka fada jikinsa cikin tsananin murna. Rungumesu yayi tsam ajikinsa shima yana shafa kawunansu. “Welcome dad” suka fada atare. “Thank u dears” yabasu amsa, daidai nan su mommy suka karaso garesa, kowa narige_rigen hugging daddy. Daya bayan daya yake rungumesu suna gaisawa, mustapha ne na karshe daya tsaya kawai yana kallonsu cike da sha’awa, fuskarsa cike da annuri. Takawa daddy yayi har daf dashi yayi hugging dinsa yana fadin, “Muhammad dina, I really missed u” lumshe idonsa yayi cikin kaunar mahaifinnasa yace, “missed u too dad” shafa kansa daddy yayi cike da matsananciyar kaunarsa. Sannan yasakesa suka shiga gaisawa da abokanansa kuma amininansa. Dunguma sukayi duka zuwa mota…….