
Kwanaki nata tafiya rayuwa tana shudewa dadadi babu dadi ga kowanne dan Adam,hakance ta kasance ga maryam. Yau gashi har alh, menasara yayi sati biyu da dawowa. Rayuwata natafiya acikin gidansa, cikin rashin jin dadi, saboda kyara da kyamar danake fuskanta ga suhailat yafi nada. Dadina daya yanzu kawai ina zuwa makaranta ko zama bana samu sosai, danyanzu nafara zuwa islamiyya ta safe 9_11, asabar da lahadi. Yaya sadiq ne yakaini, anan bayan layinmu take babu nisa da kafatama nake zuwa. Kulawa da kaunar da yaya sadiq yake nunamun bazata misaltuba, harna rasa dame zansaka masa arayuwa. Yayimun abunda bazantaba mantawa dashiba akullum cikin yimasa addu’a nakeyi Allah yabiya masa bukatunsa na duniya da lahira. Bani da matsala da megidan kokadan, danshima tamkar aunty yake, gashi da barkwanci da ban dariya, tamkar bame kudiba. Duk da ba kullum nake ganinsaba amma na fuskanci hakan daga gareshi, danseyayi kwana 3 kafin yazo part din mommy,sedai kullum su sunacan. A kowanni sakanni dayake wucewa tunanin mustapha na karuwa a zuciyar maryam, yanzu kam abunna bani tsoro matuka,gashi duk ranar daban ganshiba hankalina atashe yake, nayitabin duk wata hanya kenan danasan zangansa konaji dadi araina. Gashi banasamun ganinnasa kullum senayi kwana 3 ko 4 bamu haduba, sedai idan Allah yataimakeni mommy ta aikeni wani lokacin. Alhamdulillah ina maida hankalina sosai akan karatu danyanzu muna gabda fara jarrabawa. Wani satin zamu fara da yardar Allah. Abangaren sadiq kuwa, yagama tabbatarwa da kansa da zuciyarsa son maryam yashigesa,amma yakasa tunkararta yasanar mata seyayi niyyar fada mata sekuma yakasa, saboda besan yazata dauki al’amarinba, kuma yana ganin kamar tayi kankanta amata zancen soyayya yanzu. Aunty tayiwa daddy zancen yin auransu suhailat da mustapha, amma koda yatuntubi mommy da maganar, setace Sam bata lamuntaba se yarta takarasa karatu tunda saura shekara daya da watanni sugama. Hakuri daddy yabawa aunty akan tabari suhailat din takarasa karatunnata, badon aunty tasoba ta hakura tabisu addu’a kawai. Su mustapha kuwa kai yayi caji sunata shirye_shiryen bikin lukman, ga aikin office gashi kuma komai na bikin dashi akeyi, dukda yaso turjewa akan hidimar bikin amma abokansa sukace be’isaba yana aminin ango dole ayi komai tare dashi.
Cike da tsananin murna natashi yau saboda zanje unguwarmu ganin gida, tun jiya na tambayi mommy kuma tabarni bata hananiba. Dama biki sukeyi tun ran laraba suka fara haryau lahadi, kullum da yamma sesun fita se dare suke dawowa, kuma dukansu har samarin gidan. Sedai naje part din su baaba talatu musha hira kafin su dawo. Yaya sadiq jiya yace nashirya muje bikin, nace masa a’a yayiyayi amma naki zuwa anannema naji labarin Ashe bikin abokin yaya mustapha akeyi shiyasa kwana biyu bangansaba,kewar ganinsa duk tacikamun zuciya. Da wuri nagama duka ayyukana kafin 12 nashirya tsaf cikin wani less dinkin riga da zanine, yamun dass ajikina. Tunda nazo gidan bantaba saka mayafiba seyaudai nace bara nasaka. Banyi wata kwalliyaba powder kawai na mutstsika nasa lipstick fari a lebena se kwalli. Simple dauri nayi nadora mayafina kalar kayan. Tsayawa nayi ina kallon kaina a madubi senaga nayi kyau hasken fatata yafara dawowa zamana a gidannan na wata daya da kwanaki. Duk Wanda yasanni ada kafin nazo gidan yaganni yanzu zega tabbas nacanza. Takalmi da jaka nasa kalar kayan na fesa sassanyan turaren danake sawa, Wanda duk acikin siyayyar yaya sadiq suke,ledar dana kwasarwa saleemat,da gwaggo turaruka da mayuka nashafawa nadauka nafito. Seda nafara zuwa dakin mommy namata sallama tukun, itama shiryawa natarar tanayi zata gidan biki. Ina kokarin fita daga falon suhailat tafito daga dakinta, cikin shirinta tayi kyau sosai itama. Cike da mamaki suhailat take satar kallon maryam, setaga yarinyar ta wani kara kyau da haske, ga wani sassayan kamshin dake tashi ajikinta. “Sannu da fitowa aunty suhailat” maryam ta katse mata tunani da fadar haka. Bata amsaba sema yatsina fuska datayi tace, “kekuma inazaki?” cike da doki da zumudi nace, “zanje ganin gida ne” tabe baki suhailat tayi batace komaiba tayi gaba. Nidai bandamuba saboda farincikin danakeji danyau zanga umma da saleemat dita da gwaggo. Seda nafara zuwa nayiwa baaba talatu sallama sannan na nufi parking space inda yaya sadiq yake jirana, danyace shize kaini tin jiya dana fada masa zani gida. Yana bakin gurin kuwa yana jirana, har mamakin yaya sadiq nakeyi kullum bana jiranshi sedai shi yajirani ko makaranta zamu. Tunda sadiq yahango maryam yakura mata ido, tayi matukar yimasa kyau yau, duk da mayafi tasaka amma yarufe mata ko’ina na jikinta, tayi shigarta ta mutunci, harta karaso garesa amma yakasa dauke idonsa daga kanta. Wani kallo naga yaya sadiq yana bina dashi, dukse naji na tsargu, daurewa nayi nagaisheshi cikin sanyin murya naji ya amsamun. Babu bata lokaci muka shige mota yaja muka tafi dama tun jiya nafada masa sunan unguwarmu. Yau tafiyar tamu babu hira, waka kawai yake samana a motar ta soyayya. Cikin abunda befi 20 minutes ba muka isa ungurmu ta darmanawa wata boyayyiyar ajiyar zuciya nasauke murna tacikamun ruhina, jinake tamkar nayi shekaru rabona da unguwar,Muna tafe ina nuna masa hanya har kofar gidan gwaggo, Allah yasoma mota tana shiga har layinnamu. Cikin zumudi na bude kofa da nufin fita. Tsayar dani yaya sadiq yayi da fadin, “to sarkin hanzari zaki tafi ko sallama bamuyiba, idan kinshiga kimun iso zanshigo mugaisa da mutanen gidan. Cikin jin kunya nayi murmushi nace, “to yayana” sannan na fice daga motar. Binta yayi da kallo harta shige, Kalmar yayana data kirashi da ita tamasa dashi. Lumshe idonsa yayi tare da kwantar da kansa ajikin kujera. Da gudu nashiga gidan ina kwalawa gwaggo kira, “gwaggo! Gwaggo!” Hajiya gwaggo tana daki tana lissafin kudi taji ana kwala mata kira. Ajiye kudin tayi da sauri tana fadin, “wanakeji haka kamar muryar maryam” “nice gwaggo” nafadi haka ina shiga dakinnata. “Oh ni ladi, yanzu yannan seyau kika tuna dani, wato kinsamu daula kinmanta da niko” “kai gwaggo bazata sauya halintaba” nafadi haka araiana, a fili kuwa senace, “haba gwaggota karkice haka mana, kullum da tunaninki nake kwana nake tashi”
Hararata gwaggo tayi tare da fadin, “kinganki kuwa maryam, sekace matar gwamna fatarki kamar jikin kifi dan kyau, amma da kina bazaki aikatau dinnanba,gashinan yanzu kinje kinajin dadinki kinyi limun buki dake.” Dariya nayi bayan nazauna agefenta nace, “ai gwaggo bawananne abun murnaba harfa makaranta aka sani agidan boko da islamiyya” memakon naga gwaggo tayi murna senaga ta kebe baki tace, “wannan yarinyar jarabbaki tasan karatu yawa gareta, keda aka turaki aiki meyakaiki kuma yarda asaki a makaranta, dayaushe kikesamun lokacin aikin kenan?” “Gwaggo ai aikin bawani meyawa bane, idannadawo nakeyi” batakara bi takan zancenba.ledar hannuna ta kalla tace, “mene wannan aleda badai shine iya dan abun dakika kawomunba, yanzu maryam saboda bakin hali irinnaki kina irin wannan katon gidan amma zakizo gurina da dan abunda zaki kawomun kena….sallamar dawani yaro ya kwadane yakatsewa gwaggo zancenta, mikewa tayi tafice tana amsawa. Da kallon takaici nabita,ita ko murnar ganinama batayiba ta abunda nakawo mata kawai takeyi, ko tambayata wanne hali nake ciki agidan batayiba, babu ruwanta ko yankan naman jikina akeyi, itadai na kawo mata kudi da kaya. kai nayarda da’ake cewa me hali baya taba canza halinsa. Dakinnata nabi da kallo gaba daya yayi kaca_kaca wani bashi_bashine yake tashima adakin, itama tayi wani dukun_dukun da ita, idonta harda kwansar bacci. Wata guda naji gwaggo ta rangada tana fadin, “kai haihuwa me dadi, yanzu duk wannan kayan Wanda sukazo da maryam dinne yakawo,wayyo dadi.” Dasauri nafito daga dakin har inayin tuntube, jin abunda gwaggo tace. Turus na tsaya ina kallon kayan da yara suketa shigowa dashi, kayan abincine, shinkafa taliya macaroni, indomie magi hardasu gwangwanin madara, da born vita,milo katun_katun din gwangwanaye da crase din kwai guda biyu. Daya daga cikin yaran na kalla nace, “kai dan malam wayabako kayannan yace kukawo?” “Wanine a waje acikin wata katuwar mota mekyau” kama haba nayi cike da mamaki, yaya sadiq kenan shine da wannan hidimar, dannasandai shine awaje acikin mota, dan layinmu mota biyu bazata zaunaba,kuma nasan yana waje yana jirana, to inama kayannan suke danni bangansuba a motar. “A boot mana” nabawa kaina amsa. Gwaggo dake tsaye tanata zuba sunbatu da santi, tazari wani mayafinta a igiya tana fadin, “bari naje mugaisa, kai abu yayi kyaufa” tsayar da gwaggo nayi amma taki tsayawa nasan yanzu setace ta bani kunya agurin mutumin danake ganin girmansa, jikina asanyaye nabi bayanta cike da takaicin halayenta. Sadiq yana tsaye ajikin motarsa yana sallamar yaran dasuka kai kaya gidansu maryam, gwaggo tafito tana washe hakora tace, “sannu dan arziki irin albarka, yaron kirki, aiba akasa kadibaba gada kayi, haka halin mahaifinka yake kyauta gareshi” karasowa sadiq yayi har gaban gwaggo ya tsugunna yana gaidata, amsawa gwaggo tayi cikin jindadi tana dariya. Daidai nan nakaraso zauren gidanmu, wani bakin cikine yakamani jin kalaman da gwaggo take sakarwa yaya sadiq, na roko. Waidama bata da abinci bata dame kawo mata, segashi Allah yajeho matashi, dabezoba dabatasan yanda zatayi da kantaba,ga bata kudi duk bashikan mutanene akanta. Kalamaidai na zubar da mutunci da aji gwaggo take masa harda kukan munafurci, ga wani Karin abun takaicinma tundaga soro gidan duk bola da yaana. Bangamajin surukatannataba nakoma ciki, tunda abunda nake gudu ya auku. Sauri nayi kafin tadawo na kwaso turaruka da mai acikin Wanda nazo dashi nakai dakina na gidan na boye, dan idan tagani bazata bari nabawa saleemat dinba. Shima dakin gabadaya yayi kura, da yaanar ga wani uban shirgi Mara kan gado aciki. Seda tagama babatunta da zubar da mutuncin sannan tadawo, da kudi ahannunta me yawa da sadiq yabata. Rawa tahauyi da juyi atsakar gida duk dan murna. Mutum angirma ba’asan angirmaba. Fita nayi don muyi sallama da yaya sadiq. kunyarsa duk ta lullubeni nama kasa hada ido dashi, hakadai mukayi sallamar yace bayan magriba zezo yadaukeni. Ina dawowa gidan nacire kayan jikina, nadauki wani zanin gwaggo Medan hankali nadaura nahau gyaran gidan gwaggo. Tsakar gidan nafara sharewa zuwa soro, bola himuli natara. Sannan na dawo wankin bandaki, duk yabi yadafe se uban zarni da wari, haka na wanke matashi tass ina tsartar da yawu. Kayan wanke_wanke nahada shima himili guda, wasu kwanukan duka anbar guntun abinci aciki haryayi funfuna. Bazan iya wankewaba gaskiya tattarasu nayi nakai bola na wanke sauran dazan iya. Tass nagyarawa gwaggo gidanta cikin abunda befi awa biyuba, har tsintsiya nasa na rage yanar gidan. Seda nayi wanka dan kyankyamin jikina nake sannan nasa kayana nayi sallar azhar.gyaran dakintane seda na idar da sallah kawai namata. Amma gwaggo ko sannu batamunma, nidama dan Allah nayi badon itaba. Lissafe lissafen kudinta kawai takeyi. Wankine kawai banyiwa gwaggoba, shima dan ina saurine inje inga masoyiyata saleemat. Maryam na kallon gwaggo tanacin bredinta da miya, amma kotayi batamataba dukkuwa da uwar bautarnan data mata. Jakata nadauka nace mata zanje gidansu saleemat. Ledar danazo da ita dama tuni ta janyeta, seda tacaje jakata tass harda jikina taga babu komai sannan ta barni na tafi, wai duk dan karna kaiwa su saleemat komai, gwaggo, gwaggo hmmmm????????………..✍️