Uncategorized

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE HAUSA NOVEL

shima wannan ba editing,???? nagode da addu’oinku, Allah yajikan musulman dasuka rigamu gidan gaskiya baki daya????????

BY
zeey kumurya
ABUNDA KA SHUKA………
(shizaka girba)

MALLAKIN
????
ZAINAB USMAN KUMURYA

FARIN JINI WRITERS ASSO…..????

~Free novel~

Bismillahirrahmanirrahim

2️⃣3️⃣

……….Salimat yau wanki sukesha ita da umma, tana sabawa umma na tishi da dauraya. dan’autansu me suna hanifne ya shigo da gudu yana kwalawa saleemat kira,tun daga soro. “Yaya saleema,yaya saleema!” “Na’am, autan umma ya’akayine irin wannan kira haka” “yanzu naga yamaryam ansauketa a wata mota me kyau” saleemat dabatayi tunanin ganin maryam yanzuba tace, “autan umma banason karya, ina kaga yamaryam din, sedai idan wata kagani.” “Allah yasaleemat yamaryam nagani itafa da wani mutum me mota” murmushi umma tayi tace, “mutanen dake zuwa gidan gwaggo ai yawa garesu, yadaiga wata yake tunanin maryam dince, danyaga kullum cikin zancenta muke” “gaskiya dai, amma banda haka maryam meze hadata da wani harda za’akawota a mota, bama na tunanin zuwan maryam unguwarnan yanzu” cewar saleemat tana mikewa domin shanya kayan da umma ta dauraye. Turo baki hanif yayi ganin sun karyatashi ya juya ze fita. Hanashi fita saleemat tayi dan yanzu idan yafita se lokacin islamiyya yayi bedawoba. Harsuka gama wankin hirar maryam sukeyi, abunda ya kara tabbatar musu ba maryam ce tazoba,jin gudar gwaggo dansunsa gwaggo bazatayiwa zuwan maryam wannan murnarba. wanka saleemat tayiwa kannenta biyu ta shiryasu suka tafi islamiyya. Cike da murna da doki nanufi gidansu saleemat bayan nadau kayan dana boye adakina. Saleemat na bakin rijiya tanajan ruwan wanka bayan tayi sallah taci abinci na shigo gidan da sallama. Da matukar mamaki saleemat ta juyo tana kallon bakin kofa tare da sakin gugan hannunta a lokaci guda tana waro idanunta waje. Fuskata dauke da murmushi nacigaba da tunkararta mamakin ganin maryam yahana saleemat ko motsi balle ta amsa sallamar data mata. Cikin ihun murna kuma, ta kwasa da gudu ta rukunkume maryam, nima rungumeta nayi ajikina cikin jindadin ganinta,atare muka sauke ajiyar zuciya ni da ita. Umma ce tafito daga daki tana fadin lafiyarki kuwa salima kikasaki guda haka, wannan aise kifadarwada mutum gaba ga Ku…..maganar umma ce ta tsaya ganin salimat rungume da wata. Sakin maryam salimat tayi cikin tsananin murna da farincikinganin maryam mara misaltuwa tace, “umma she dagaske hanif yake maryam tazo” kafin umma tayi magana nanufeta da gudu na rungumeta itama ina fadin, “ummata nayi kewarki sosai” umma dake cike da dinbun mamaki da farincikin ganin maryam tace, “maryama dagaske kece agidannamu yau” “nice umma” nafadi haka ina sakinta. “Maraba lale marhabun diyata, kai amma naji dadin ganinki,shigo, shigo, shigo” umma ta kama hannuna muka shiga daki. saleemat dake tabun maryam da kallo ganin cikin kwanaki kadan ta sauya tabi bayansu zuwa dakin. Farin cikin datake ciki yau baze misaltuba naganin kawa,aminiya,kuma yar’uwarta da kulkum take kwana take tashi da ita aranta. Gaishe da umma maryam tayi tare da dan taba hirar yaushe gamo, salimat dai tatasa maryam agaba kawai tana kallonta. Fita umma tayi da kanta domin takawowa maryam abinci da ruwa. Hararar salimat nayi bayan umma tafita nace, “wannan kallonfa, kintasani agaba ko kewatama bakiyiba ko” matsowa kusa da maryam suhailat tayi ta rungumuta a jikinta tace, “haba tawan, aike ko fada miki akayi banyi kewarkiba nasan zaki karyata, naga kinkaramun wani kyaune da fresh ga wani daddadan kamshi dake tashi ajikinki, kuma ta ummanki kike bataniba,shiyasa namiki shiru” “hmmm,ainazo zaki fara, ya kwana 2 ya makaranta?” “Alhamdulillah muna shirin farama waec” “masha Allah,Allah ya taimaka yabada sa’a, kinsan nima nakoma school da islamiyya” cikin mamaki salimat take duban maryam,amma batace komaiba. “Dagaske kawata,nakoma makaranta,nima” nafadi haka ina murmushi. rukunkumeni salimat tayi cikin tsananin murna tana murmushi tace, “wayyo dadi, amma gaskiya maryam naji dadin wannan labarin, amma gaskiya mutanen gidan suna da kirki dasuka saki a school” daidainan umma ta dawo da ruwa da abinci ahannunta harda lemo, dasauri muka tashi muka karbeta ina mata sannu tare da godiya. Cikin tsananin farin ciki salimat ta mata bayanin na koma makaranta, tayani murna umma tayi sosai tare damun addu’ar samun nasara. Abinci umma tace na sakko naci, jallop din taliyace da zafinta taji kayan hadi daidai misali, wanka salimat ta shiga kafin nagama cin abincin, umma kuwa tarasa inda zatasaka maryam don farincikin ganinta fess,batayi zaton zasu ganta hakaba, ga kuma daddadan labarin ta koma karatu, umma setaji wata nutsuwa hankalinta ya kwanta akan aikatau din maryam. Bayan nagama cin abincine umma ta dubeni tace, “maryama ya gidan aikinnaki babu dai wata matsala ko?” Ajiyar zuciya nasauke nace. “Gashinandai umma kinsan masu kudi, inadai dan fuskantar matsala daga wasu yayan gidan,amma matar gidankam babu wata matsala, bata shiga sabgata idan ba aiki zanmataba. Sauran ma’aikatan gidanma muna zaune lafiya, kuma kome zasuci agidan nima zan iyaci, ba’amun iyaka da abinci ko sha kowanne irine,megidan dabayananma danaje gidan yayi tafiya, sati biyu dasuka wuce yadawo kuma shima gaskiyadai bashi da matsala…………….

Labarin komai na gidan maryam tabawa umma, harda kirkin da sadiq da baaba talatu suke mata da zuwan su aunty, labarin fyaden da’akewa yan aikin gidan kawai bata fadawa ummaba dan kar hankalinta yatashi,tadaice tatayata da addu’a akan Allah yakareta daga duk wani sharri nagidan. Numfashi umma tasauke tace, “Dama ba duka hali yazama dayaba, ” Allah yasakawa wannan yaro dayake dawainiya dake da alkhairi, Allah yabiyasa da aljannah, sukuma sauran yaran gidan sekiyi takatsantsan da bacin ransu, kikuma kama kanki tunda kince yaran gidan duk samarine. kikara hakuri maryam komai lokacine, kuma komai me wucewane kinji” “insha Allah umma nagode sosai” salimat ce ta dawo dakin umma kuma tafita domin karasa aikin gida. Labarin gidan alh. Menasara nabawa maryam atakaice itama, addu’a taitaiwa yaya sadiq itama dakuma kara bani baki. Sallar la’asar mukayi sannan mukacigaba da hirarmu cikin jindadin ganin juna dakuma kewa. Farincikin kasancewa da salimat ayau yaragemun tunanin mustapha araina, amma duk da haka yana fadomun arai lokaci zuwa lokaci.

Muna cikin hira naga salimat tayi shiru tana kallona. cikin mamakinta nace, “Menene naga kintsaya kina kallona?” Numfashi salimat ta sauke tace, kamar akwai abunda kedamunki Wanda kike kokarin boyemun amma fuskarki tagaza boyewa seda ta nuna” nuna kaina nayi da hannu nace, “nikuma gaskiya babu abunda yake damuna” kama hannun maryam salimat tayi tace, “bekamata ayanda Muke dake kiboyemun wani abu dake damunkiba, muna zaunannen senaga kinyi shiru harda lumshe ido, kina sauke numfashi, tabbas hakan alamace ta akwai abunda yake damunki acikin ranki” “gaskiya babu komai, sedai ko tunanin exam dazamu fara next week” “hmmm, maryam kenan maganar dakikeyi yanzu tana kara fallasa abunda ke ranki,kinsan maryam nasanki nasan duk wani moment dinki, kifadamun abunda ke damunki kona samu kwanciyar hankali, domin kuwa tabbas idan kika tafi ahaka, zaki barni cikin damuwane, kifadamun koda wata matsala dakike fuskanta agidan aikin,nikuma zanbaki shawarar dazata amfaneki tare da tayaki da addu’a da yardar Allah” shiru nayi ina sauke numfashi, tabbas salimat tayi gaskiya, aduk lokacin da mustapha yafadomun araine nake shiga yanayin data fada, kuma salimat bata cancanci na boye mata komai na rayuwataba,kuma dama ina son tambaya akan abunda nakeji akan mustapha. Wata doguwar ajiyar zuciya nasauke ina duban salimat nace, “nima bansan meke damunaba kawata, amma na tsinci kaina acikin wani irin yanayi a kwanakin dasuka shude, zuciyata ta kasance kullum cikin tunanin wani bawan Allah take, dakuma kwadayin ganinsa akodayaushe, aduk lokacin dana gansa inajin zuciyata na wata irin bugawa tare da samun nutsuwa araina, inajin dazan wuni ina kallonsa bazan gajiba, bansan yanda zan kwatanta miki yanda nake jinsa arainaba, ada nayi tunanin tsoronsa danakeji seda daga baya kuma naga abun yawuce akirashi da tsoro” “waye shi?” Salimat ta jehomun wannan tambayar. Labarin musty na bata atakaice. Shiru salimat tayi, domin tagane maryam ta kamo da son mustapha ne, batare data saniba, amma bazata fada mataba dankar tatada mata da hankali, zata tayata dai da addu’a Allah yayaye mata, domin abunda baze yiyubane wannan, soyayyar maryam da danmekudi irin alh. menasara, bata mata fatan hakan koda nangaba, domin ayanda maryam tabata labarin yaran gidan zasu zangwametane kawai su kyareta, koda ta auresa bazataji dadin danginsaba. to idanma bahakaba shi Wanda takeso din yamasan tanayi, inma yasan tanayi zesotane,mutumin da tasan ko kallo maryam bata ishesaba. Addu’a salimat tacewa maryam tadage da ita, tare kuma da nisanta kanta da haduwarsu da mustapha zataji saukin abun aranta,kuma dantariga tasawa ranta tsoronsane yiyasa takejin hakan akansa. Godiya na mata,cikin yarda da abunda tacemun batare da tunanin komaiba. Hirarmu muka cigaba dayi……

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button