Uncategorized

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE HAUSA NOVEL

Kafin magriba na kafa kaskon a warata saboda har anfara zuwa nema.ina tsaka da suyar awarar bayan sallar magriba, abun mamaki,gwaggo ta fito daga daki da saurinta. Maryam zo kije gidan lantana yanzunannan zaki karbomin wani sako,kiyi sauri sakonna saurine,kuma kinga da sauran awara karki zauna. “Toh gwaggo insha Allahu bazan zaunaba,dakina nanufa da niyyar in shiga na dakko hijabi,saboda na jikina yana dan kauri kaurin hayaki,amma gwaggo ta dakamun wata irin tsawa,” gidan uwarwa zaki kuma bayan na fada miki sauri nakeyi. Da sauri nayi hanyar fita,jikina na rawa.lantana tana gandun sarki ne,da dan nisa tsakaninmu hakan yasa nake tafiya da dan sauri sauri…..

Text yayiwa mommy zeje gurin abokinsa,lukman saboda damunsa dayakeyi akan bayason zuwa wajensa sedaishi yayita zuwa.mommy tana ganin text dinsa tayi murmushi, domin dama sometimes yasaba mata hakan,idan zefada mata Abu befiya kirantaba,sedai ya mata text.reply ta masa akan Allah ya kiyaye hanya.shikadai yaja motarsa,yatafi batare da koda drivernsaba…….

Kusan minti goma sha biyar nayi ahanya,kafin nakarasa gidan lantana.amma nadaje lantana ta barni a tsakar gida ta shige daki,fiye da minti talatin sannan ta fito ta bani sakon.a lokacin raina yakai kololuwa wajen baci,domin nasan tana sane tamun haka,ga tsoro da fargabar abunda gwaggo zatamun yamun rufdugu akaina. Ashe sakon kudine shiyasa naga gwaggo tana rawar jiki.karba nayi na nufi gida.wajen ba mutane sosai,hasalima tunda na taho banhadu da kowaba,gudu na farayi zuciyata na bugawa,tsorone me tsanani ya kamani Wanda bansan kona meneba…….

Cikin takunsa na cikakken namiji,jarumi, yake tafiya,shida lukmanne daya rakoshi ze tafi gida,tafiya sukeyi zasu karasa gurin motarsa,dayay parking a gefen titi.kamar an cillota daga sama kawai jiyayi ta bugi kirjinsa,da sauri nayi baya jinnayi karo da mutum,banzataba banyi tsammaniba,saboda hankalina gaba daya baya jikina,yayi gida.wani daddadan kamshine yaziyarci hancina,wanda tunda uwata ta haifeni bantabajin irinsaba.wata irin bugawa kirjina yayi da karfi,jikina ya fara rawa,kaina naji ya mugun saramun, jinayi kawai nayi luuuu zanfadi,taroni yayi da tattausan hannunsa,ya hadeni da jikinsa.wani irin yammm yaji ajikinsa,tsigar jikinsa ta tashi ta mimmike,lokaci daya yanayinsa ya sauya,lumshe idonsa yayi cikin amsar bakon yanayin daya riskeshi,zuciyarsa na bugawa dasauri da sauri,kafarsace ta gagara daukarsa,kasa mukayi gabadayanmu dani dashi,shi yafarayin kasa ni kuma na fada kan faffadan kirjinsa,wani mahaukacin feeling ne yaji ya bujuro masa,jinta a kwance a kirjinsa, Wanda betaba jin irinsaba tunda yake arayuwarsa. wani irin harbawa jijiyarsa tayi ajikina,jinayi wani Abu kamar an harbomun ya zungureni……………..✍️

BY
zeey kumurya
AUNDA KA SHUKA………
(shizaka girba)

MALLAKIN
????
ZAINAB USMAN KUMURYA

FARIN JINI WRITERS ASSO…..????

~Free novel~

Bismillahirrahmanirrahim

0️⃣3️⃣

………..Bansan ya’akaiba kawai gani nayi na mike tsaye,jikina ya kama kyarma tamkar anjonamun schocking, wannan shine karon farko arayuwata dana taba hada jiki da wani da namijin,dayan da suke tarene ya rike hannuna,ganin bana cikin nutsuwata yace. “sannu ‘yanmata,ba bakin magana se rawa kawai na jikina yakeyi,tamkar mazari.

Tattaro duk wata juriyarsa yayi,ya mike tsaye,har yanzu yanajin bakon yanayin ajikinsa.

Dakyar na tattara nutsuwata na sunkuya nadauki sakon gwaggo daya fadi kasa,Allah yasama kudin a cikin Leda ta sakamun.ban kara kallon Wanda muka fadi tareba,saboda kunya da tsananin tsoron daya rufeni. Kai na akasa,cikin rawar murya nace” ka..yi..ha..kuri…dan.. Alllah,shiru yayi kawai batare da yacemun komaiba. wani tsorone ya kara mamayeni karnaje kobe hakuraba. Dayan ne kawai yamun magana. “Karki damu ‘yan mata,amma dai kidinga kula gashi dare yayi,muje mu rage miki hanya ko? A’a nagode,ina gama fadar hakan na kama hanya na fara tafiya,zuciyata cike da zullumin,kodai Wanda na buge kurmane,amma banda haka mezesa mutum yaki magana.gashi gaba daya kamshin turarensa ya gamemin jikina,Jinakeyi tamkar yana gurin har yanzu.saitin zuciyata na dafa,saboda har lokacin tana bugawa da sauri da sauri.numfashi na sauke,wani bakon yanayi dabansan na meneba yana ziyartata.

Dubansa lukman yayi ganin yanda gaba daya yanayinsa ya sauya,shi duk a tunaninsa ransane ya matukar baci akan abunda ya faru,hakuri ya hau bashi,amma seyaga ya daga masa hannu kawai,gurin motarsa ya nufa ya bata wuta.

Ikon Allah ne kawai yakaishi gida,saboda har lokacin jiyakeyi tamkar tana kwance a kirjinnnashi,wani irin yanayi yake ciki me wuyar fassarawa. Bedroom dinsa ya nufa tare da fadawa kan gadonsa,ina ze ganta,a ina zekara ganinta,ya kara rungumeta kozeji irin yanayin dayaji sanda tana kwance a kirjinsa,gashi ko fuskarta beganiba,saboda gurin ba wadataccen haske,kansa ya dafe,tare da runtse idonsa,zuciyarsa na bugawa da sauri da sauri….

Kusan minti talatin nayi ahanya,saboda tunanin mutumin da na buge,se lumshe ido nakeyi saboda dadin kamshinsa,dayaki barin jikina,seda nazo kwanar gidanmu sannan na tuna da Abunda na bari,ga tuyar awara gashi gwaggo tace inyi sauri.addu’ar Neman tsari na fara karantowa a zuciyata.cike da tsananin tsoro na shiga gidan da sallama ta.gurin suyar awarar na kalla,kaskon na gani da guntun mai akasa, alamun an gama suyar awarar. Dakin gwaggo na nufa zuciyata na tsananta bugu,babu wutar nepa,amma dakin gwaggo da akwai sola. Tana zaune akan doguwar kujerar dake dakinnata,ta Dora kafa daya kan daya. Tsugunnawa nayi agabanta, “gwaggo ga sakonnaki” na furta cikin sanyin murya.

Wani mugun kallo ta jefeni dashi,tace.”gidan ubanwa kika tsaya kusan awa biyu,kuma nakira lantana tacemun tun dazu ta baki sakon. Baya na farayi ina bawa gwaggo hakuri,domin bansan mezance mataba,nasan yau me kwatata a hannun gwaggo se Allah.wata wayar wuta ta janyo agefenta me matukar kauri ta zubamun agadon bayana,da gudu na tashi nayi tsakar gida ina kokarin fita waje,amma seda gwaggo ta cimmun.dukana ta hauyi kota ina,sekace jaka,ihu nakeyi da dukkan karfina ina Neman taimako,ina bata hakuri,amma tamkar kara zugata nakeyi.

Umman su saleemat wadda katangar gidansu take jikin namun gidan,itace ta shigo da saurinta.tsakiyarmu ta shiga ta rike wayar hannun gwaggo.da sauri na tashi na buya abayanta ina sakin ajiyar zuciya,akai akai.

“Ke suwaiba,ki matsamun ki bani guri kuma ki cikamun bulala,gwaggo ce take fadar haka cikin daga murya,se zaro ido takeyi ta fiffika tamkar wata sabuwar kamu.

“Bazan cikaba,gwaggo.yaza’ayi ki samu yarinya marainiyar Allah ki maidata sekace jaka,kullum sekin jibgeta haka akeyi. Tafa hannuwa gwaggo ta farayi tana salati,”ni zakiyiwa rashin kunya suwaiba,har cikin gidana.lallai wuyanki yayi kauri,kifita daga safgata suwaiba,banason shishshigin da kikemun akan maryam. “Ba shishshigi bane gaskiyace gwaggo kuma dole a fada miki,amma ni ba rashin kunya zan mikiba.Abunda kikeyi ba kya kyautawa… ” yaza’ayi in kyauta in aiki yarinyar tun dazu taje ta zauna,amma se yanzu zata dawomun gida,dama nasan tun ba yauba,ai bin maza takeyi idan kuma sharri na mata kamshin turaren ubanwa takeyi,gatanan ai ki shanshanata kiji.saboda yadda gwaggo take magana cikin kakkausar murya tare da daga murya mutane ‘yan gulma harsun fara shigowa gidannamu.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button