Uncategorized

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE HAUSA NOVEL

Ina gama ayyukana nakoma daki nayi wanka nashirya cikin uniform dina. Kotunanin abinci banba nazumbula hijabina nafito domin tafiya school. Mommy nagani a falo taci kwalliya da’alama turakar miji zata koma. Gaisheta nayi ta’amsa tana bina da kallonta, yaukam ta kuramun ido sosai. Harna fara tafiya ta tsaidani da fadin. “Maryam lafiya kike kuwa,naganki haka?” “Lafiya kalau mommy, kainane kedanmun ciwo” nabata amsa kwalla nataruwa a idona ta tausayin kaina. “Ayya sannu, Allah yasawwake dafatandai kinsha magani ko?” Kaina gyada mata alamar eh. Sannu ta karamun nikuma nafice. Kodanaje makarantarma su zee da salma setambayata suke lafiya nake, nace musu marata kemun ciwo kawai dansu barni. Sannu sukamun dafatan samun sauki. Dakyar na iya zana text din damukayi, danni yau komai ya kuncemun tsoro da fargabane kawai acikin raina. Gashi yau bamu tafi gida da wuriba saboda munyi practical din biology. Seda 4 tawucema nadawo gida. Abun mamaki ina shiga falo naga yaya sadiq zaune, dama ina school Inata addu’ar Allah yasa yadawo. Jinayi gabadaya Rabin damuwata tatafi, wani farincikine ya lullubeni kamar naje narungumesa haka naji. Murnar danakeyi taganinsa kasa boyuwa tayi, zama nayi ina jera masa sannu da zuwa da tambayarsa ya hanya. Shikuwa sadiq ganin yanda maryam tayi murnar ganinsa alamun tayi kewarsa seyaji tamkar anmasa albishir da aljannah, domin hakan nanuni da cewa itama tafara damuwa dashi. hira muka dan taba yana tambayata ya karatu da komai da komai nace masa komai lafiya. daga karshe yacewa maryam taje ta kimtsa tafito tasamesa afalo. saboda sadiq yakudiri niyyar yau zesanar da maryam abunda ke ransa,koyahuta.

Wanka nayi tare dayin sallah sannan naci abinci, dan yunwa tafara nukurkusata. Kamar yadda yaya sadiq yace nasamesa afalo anan naje nasamesa. Shikadaine a falon ya kwantar da jikinsa ajikin kujera idanunsa a lumshe. Zama nayi agefensa inafadin “sannu yaya sadiq ya gajiyar” bude idonsa yayi yasaukesu akan maryam sannan yace, “yawwa maryama be babban suna, kema sannunki, yakaratunne” “alhamdulillah yaya” gyadamun kai yayi tare da janyo ledar dake gefensa ya mikomun yana fadin ga tsarabarki tunda kinki fadamun abunda kikeso” cikin jin kunya nace, “yaya sadiq mekuma kasiyomun kaibaka gajiya dan Allah dayimun hidima, abun yayi yawa wl…. “Shiiiiii” yaya sadiq yakatseni yana Dora danyatsansa abaki yace, “babu wata hidima maryam anan, kuma banason wata doguwar godiya rike kawai” karbar ledar nayi tare da fadin ”nagode” hararata yayi saboda godiyar dana masa, murmusawa nayi ina kallonsa. Gabadaya yarame yayi wani iri, kamar bashiba. Kasa daurewa nayi nace, “yaya lafiya kuwa naganka wani iri kokayi cutane a tafiyar dakayi” girgizamun kai yayi alamun a’a tare da fadin, “wani abu ke damuna maryam, gabadaya yahanani sukuni dajin dadin rayuwa” “subhanallah wanne irin abune wannan yaya sadiq?” natambayeshi cikin yanayin damuwa. “Idan kinjima bazaki iya magancemunba kitayi da addu’a kawai” marairaicewa nayi nace, “karkace haka yaya, kafadamun mana koda da shawarace se’inbaka da kuma addu’ar” harga Allah nadamu da damuwar yaya sadiq,senaji duk babu dadi dayace wani abu nadamunsa. Sadiq kuwa juya abunda zecewa maryam yakeyi aransa, besan yazataji abunba kokuma ta daukesa. Ganin yayi shiru yana tunani sena cemasa. “Shikenan yaya, Allah yayayemaka koma meke damunka tunda bazaka fadamunba.” Kallona yajuyo yayi nawasu sakanni,kamar yadda nima nake kallonsa, zuciyata nadan harbawa. wani gwauran numfashi yasauke. Ya dauke kansa daga kallona yace, MARYAM! CIWON SONKI KEDAMUNA!!……….✍️

BY
zeey kumurya

ABUNDA KA SHUKA………
(shizaka girba)

MALLAKIN
????
ZAINAB USMAN KUMURYA

FARIN JINI WRITERS ASSO…..????

~Free novel~

Bismillahirrahmanirrahim

2️⃣5️⃣

DEDICATED TO????
MEERAH
NANA
Xeey
abjamila824
Jidderh m Ahmad
Maman jani
pheenar_Abdallah
Aseeyah

Comments dunku nasani nishadi masoyan asali,nagode sosai Allah yabar kauna❤️????

………..Cikin tsananin dimuwa dajin kalaman yaya sadiq nake kallonsa baki bude cikin rashin abunyi, tabbas ayanda yayi maganar babu alamar wasa acikinta,balle ince wasa yakemun. Wani yawu na hadiye cikin rawar murya nace, “yaya sadiq kasan me kake fada kuwa, kokamanta maryam ce agabanka yar aikin gidanku?” Juyowa yayi yana kallona da idanunsa da suka sauya launi,cikin wata kasalalliyar murya yace, “nasani maryam, nasan kece agabana,kuma gaskiyar abunda ke zuciyata nake fadamiki INA TSANANIN SONKI DA KAUNARKI MARYAM” yakarasa zancen yana taune lips dinsa gami da runtse idonsa. Tashin hankali Wanda ba’asamasa rana, wacce irin fitina yaya sadiq yakeson kunnomun agidansu dazece yana sona. Wani gwauron numfashi nasauke zuciyata na dokawa nace, “yaya sadiq!” bude idonsa yayi yazubamun amma bece komaiba. Kasa nayi dakaina narasama mezance masa, ganin abunnake tamkar mafarki nakeyi yauni yaya sadiq yace yana sona, “SO FA!” girgiza kaina nahauyi ahankali nafara magana batare dana dago kainaba. “Yaya sadiq wutsiyar rakumi tayi nesa da kasa babu…….. “Look maryam banason jin wadannan kalamanki, please and please maryam, ki amincewa soyayyata, zuciyata nagab da bugawa. idan har kikaki amsar soyyata zanshiga mummunan hali. Maryam na miki alkawarin bazaki kuka daniba insha Allah, zanzame miki bangon rayuwa, zanshayar dake zallar kauna da tsantasar soyayya azamanmu” dagowa nayi na kallesa da sauri yanda yaketa rokona,gabadaya ya marairaice duk yabi yabani tausayi. Kaina gabadaya ya kulle narasa abunyi, wannan shine karon farko arayuwata da wani danamiji yace yana sona, kuma mutum me kima da daraja a idanuna. Kawar dakaina nayi daga kallonsa nace, “dole nafadi abunda bakasan ji yaya sadiq, nifa mutum ce talaka ba yarkowaba, kaikuma fa,da akwai bambamci sosai atsakanina dakai kuma ni gaskiya ayanzu babu soyayya atsarina domin banshirya mataba, kayi hakuri idan kalamaina sun bata maka rai.” Runtse idonsa yayi cikin takaicin kalamanta zuciyarsa na masa zafi yace, “maryam bakisan soba, bakisan zafinsa da radadinsaba. So baya duba cancanta ko kamata balle kuma matsayi. So baya shawara a lokacin daze shige zuciyar mutum. kisani inasonki a duk yanda kike koda kece karshen talauci a duniya, da talaka dame kudi duk dayane agurin Allah, nima haka yake agurina, dan haka kicire batun matsayi a soyayyata dake. Bazan miki doleba kokuma na tursasaki akan dole sekin soniba, kuma dan Allah banason kiduba abubuwan dana miki kice zaki soni dan haka, nafison kisoni dan karan kanki. amma zanbaki nanda kwana 3 kije kiyi shawara,akan haka, kuma kada ki cuci kanki,wajen bani amsa. nabarki lafiya” yakarasa zancen yana Mikewa tsaye. Bejira amsar da maryam zata bashiba yafara tafiya, cikin daci da kunar zuciya,kallona daya mutum zewa sadiq yagane yana cikin tsananin damuwa.

Daskarewa nayi a zaune tamkar mutum mutumi ina binsa da kallo amma nakasa magana, harya fice daga falon. Lumshe idona nayi ina sauke dogon numfashi. “Anya kuwa nayiwa kaina adalci, yaya sadiq be cancanci nakishiba, yamun halacci arayuwa, amma inda matsalar take mahaifiyarsa, koda na amince masa munfara soyyya ba yarda zatayi da auranmu, musamman da abun yahadarmun biyu ga rashin asali ga kuma talauci.” Nafadi hakan araina. Nakasa tabuka komai, kwakwalwata ta tsaya tunaninma nakasa, inadai zaune ni kadai afalon. Addu’a nakeyi Allah yasa mafarki nakeyi bagaskiya bane wannan al’amari. Kiran sallar magriba ne yasani motsawa na mike tare da daukar ledar da yaya sadiq ya bani nayi dakina, zuciyata cike fal da damuwar bakon al’amarin daya tunkaro rayuwata Wanda bantaba tunaninshiba koda nan gaba.cikin sanyin jiki nayi alawala nayi sallah, nadade ina addu’a acikin sujjadata akan Allah ya warwaremun duk wata matsala ta rayuwata yakuma tabbatarmun da abunda yake na alkahairi agareni. Ga matsalar jiya bangama fita daga cikiba yau ga yaya sadiq ya kara shigomun da wata. Koda na idar da sallarma zama nayi Inata tunane_tunane. Da kyar na iya yunkurawa domin zuwa nagaida daddy. Ledar da yaya sadiq yabanima ko budeta banma na’ajiye acikin loka. Mommy da daddy da suhailat sukadai na tarar a falonnasa. Tunda maryam tashigo daddy ya kura mata ido yana kallonta, yarinyar tana matukar bashi sha’awa hankali da nutsuwarta, yanaso yamata tambayoyi akan rayuwarta, musamman yanzu daya gano da Wanda kallonnasu yake iri daya ga kuma muryarta datake masa………”ina wuni daddy” muryar maryam ta katse masa tunani, da gaisuwarta. Cikin fara’a yace, “lafiya kalau maryama, ya karatunnaki” “Alhamdulillah” “to masha Allah, Allah yataimaka yayi albarka” “ameen daddy nagode” nafadi haka cikin jindadi ina mikewa domin komawa. Inajin dadin addu’ar daddy akodayaushe kullum nazo seya samun albarka. Sallama nayi musu na fice…

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button