
____________________________
❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
SAKON ZUCIYATA ZUWA GAREKI MARYAMA SARAUNIYAR MATA, TAURARUWATA SANYIN IDANIYATA❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
maryam, kisani sonki yamun babbar illa acikin zuciyata nagane hakanne ta hanyoyi kamar haka, akowanne second dayake shudewa tunaninki na manne acikin zuciyata, aduk lokacin dana dau wasu awanni bangankiba senaji gabadaya nutsuwata tatafi, harse naganki nake samun nutsuwa. Idanuwana basa gajiya da kallon kyakkyawar fuskarki, aduk.lokacin dana ganki inajin farin ciki Mara misaltuwa acikin zuciyata, inajin wata nutsuwa me tattare da nishadi tana bin gabban jikina, ianjin dama in dawwama ina kallonki,zuciyata na bugawa aduk lokacin dana tunaki. Komai naki na burgeni, maganarki, nutsuwarki, tafiyarki,tattausan murmushinki. Akodayaushe hoton kyakkyawar fuskarki na manne acikin idona da zuciyata, mar………
Wani yawu me daci na hadiye makut, zuciyata na mahaukacin bugu, jikina gabadaya yakama rawa takardar ta fadi kasa batare dana karasa karantawaba, wani uban gumine yahau tsatstsafomun ta ko ina ajikina. dakyar na’iya furta Kalmar “innalillahi,wa’inna ilaihirraji’un.” Meyake shirin faruwa da rayuwatane, duka abunda yaya sadiq yarubuta amatsayin soyyayya agareni, sunakeji akan yaya mustapha, kenan hakan yana nufin nima nakamu da son yayamustapha, sonsa nakeyi. Tashin hankali!………….✍️
kuyi manage da wannan pls,tun shekaran jiya naso Baku sekuma nafita,jiya kuma naje school bansamu kainaba se dare,nafara typing bacci yadaukeni seyanzu nasamu na muku. kuyi hakuri da typing error banyi editing ba ina saurine zani school
BY
zeey kumurya
ABUNDA KA SHUKA………
(shizaka girba)
MALLAKIN
????
ZAINAB USMAN KUMURYA
FARIN JINI WRITERS ASSO…..????
~Free novel~
Bismillahirrahmanirrahim
2️⃣6️⃣
………..”innalillahiwa’inna’ilaihirraji’un, allahummma ajirni fil masibati, wa’aklifni khairan minha” naita maimaitawa a fili, cikin dimuwa da razanin kwakwalwa, zuciyata na tsananta bugu. Tabbas babu tantama son mustapha nakeyi, nashiga uku ni maryam wacce kaddarace ta kawoni gidannan ta wahala kota azabar rayuwa zankirata. Mikewa tsaye nayi ina goge gumin dake tsatstsafowa asaman goshina. zarya nafarayi ina kaiwa da komowa,cikin mawuyacin halin dabansan yazan misalta muku shiba. Sonake hawaye yasilalomun ko zanji dadin abunda nakeji acikin zuciyata na damuwa. “Yazama dole nacire soyayyar mustapha daga cikin zuciyata, to tayaya? Natambayi kaina, tunanin maganar damukayi da saleemat na tuno. Babu shakka saleemat tagane son yamustapha nakeyi shiyasa tace nayi nesa dashi. Tahakane kawai sonsa zebar cikin zuciyata, kuma sannan zanyi kokarin ganin na cusa son yayasadiq acikin zuciyata tare kuma dadagewa da addu’a, ta hakanne kawai wannan kaddararren son zefita daga zuciyata, wannan wanne irin jarabtace, son Wanda besan kanayiba, bemasan dazamanaba, banda haukan so ta bakin yaya sadiq inani inason yayamustapha. mutumin dabe Masan inayiba, besan daniba. zama nayi ina sauke ajiyar zuciya, aganina nasamu mafitar cire son yaya mustapha acikin zuciyata. tunane tunane nayi tayi har akayi sallar isha’i amma nakasa mikewa nayi, yau tsabar firgici kogaida da daddy banjeba, nama manta. dakyar na lallaba naje nayi alwala nadawo nayi sallar. Acikin sallahta addu’a natayi akan Allah yaciremun son yaya mustapha acikin raina,nama godewa Allah dasonnasa beyi mugun tasiri azuciyata. Ina zaune na rafka uban tagumi, naji ana knocking kofata. Ahankali na mike naje nabude, yaya sadiq nagani tsaye,nishaf namamanta yace zamuyi magana. Kasa nayi dakaina saboda kallon daya tastareni dashi, banason yagano wani abu nadamuwa kokadan. Juyawa yayi yana cewa, “kikaraso muyi magana” cikin sanyin jiki nabi bayanshi batare dana amsaba, na zauna agefensa. Yau samannamu shiru, duk basanan, tunda nadawoma ko mommy banganiba nasan suna part din daddy. Satar kallon yaya sadiq yayi, shima duk ya rame kamar baya cikin nutsuwarsa, duk yayi wani iri. Ko duk sonnawane yamaidashi…… “Maryam naji dadin amincewa soyayyata dakikayi, nayi farin ciki Mara misaltuwa, harna rasa bakin miki godiya. Amma dan Allah inason kifadamun gaskiya, har zuciyarki abunda kike fadamun gaskiyane, kokuma kin amincewa soyayyata dan wani abu, kokuma dan kina ganin idan kikaki amincemun kamar bakiyi halarciba. nibanason natursasaki balle namiki dole akan soyyata, kuma banaso ki cutu, inafatan kingane menake nufi. Gyada masa kai nayi cikin danne damuwata nace. “duk abunda nafada maka yaya, har cikin zuciyata yake, cancantarka da kamatarkace yasa na amince maka. Kowacce mace datasan kanta, zatayi alfahari dakai idan ta sameka amatsayin mijinta, shiyasa nima bazanso damarnan ta subcemunba.” Daga haka nayi shiru danbansan mekuma zankara cewa, wadannan dinma dakyar na iya furtasu burina a yanzu kawai insamu kadaici. Cikin jin dadin maganganun maryam sadiq yace, “gaskiya bazance nataba jin kalamai masu dadin wannan arayuwataba,idanma naji toh gaskiya namanta, yau kam maryam kinwarkamun da ciwon dake damuna acikin zuciyata, yau zanyi kwanan farinciki dana dade banyi irinsaba, nagode,nagode, nagode sosai, maryam da amsar tayin soyayyata dakikayi, ubangiji yamiki sakayya da gidan aljanna” “amin” na’amsa ina sauke numfashi nakara da fadin, “ammafa yaya sadiq akwai matsala a soyayyarmu” dasauri yajuyo cikin mamaki yana kallona, yace. “Matsala kuma wacce iri kenan” gyara zama nayi cikin jin dacin abunda zanfada nace,”Yaya sadiq koda ahalinka basu hana soyyarmu saboda talaucinaba zasu hana saboda rashin asalina, ninan dakake ganina bansan mahaifinaba kuma bansan kowa nasaba, dangin mahaifiya kawai gare…” Nakasa karasa zancena saboda kukan dayake kokarin kufcemun. Cikin tsananin tausayawa yaya sadiq yace, “kada kidamu maryam dan wannan, ni sadiq ina sonki ahaka kuma zan iya rayuwa dake ahaka, insha Allahu kuma zantayaki da addu’ar Allah ya bayyana miki dangin mahaifinki. Kuma indai maganar iyayenane, daddy bashi da matsala, shi mutum ne me fuskantar abu da kuma masa duba na fahimta, nasan insha Allahu ze fahimcemu. Ita kuma mommy nasan ta yanda zan shawo kanta,harta amince, kikwantar da hankalinki banason ganin kina damuwa.” Ajiyar zuciya nakara saukewa akaro na babu adadi, nace. “Shikenan insha Allah zandena damuwar, sannan kuma yaya ina neman wata alfarma dakai guda daya a soyayyarmu dan Allah kamun ita” “uhm, inajinki fadamun wacce irin alfarmace.” Cewar sadiq yana maida hankalinsa duka akan maryam. “Yaya sonake ka boye soyayyata dakai,tayanda babu Wanda ze fuskanta” cikin sauri sadiq yace, “banganeba mekike nufiba?” “Ina nufin midunga soyayyarmu aboye kada kowa nagidannan yasani ko kuma wani awaje har zuwa wani lokaci nan gaba.” “To maryam mene fa’idar hakan, akwai wani abu aibune a soyayyar tamu, nikam nafison nanuna miki soyayya agaban kowa ta yanda zaki tabbatar da har zuciyata ina sonki” “kayi hakuri yaya, dan Allah kamun wannan alfarma, ina da dalilin haka, idan lokaci yayi zanfada maka dalili. Shiru yaya sadiq yayi na wasu sakanni, sannan yace. “Shikenan maryam namiki wannan alfarmar, inafatan lokacin bame tsaho bane.” “Bawani me tsaho bane insha Allah” “tom shikenan kikoma ciki ki huta naga kamar duk agajiye kike, da safe zamu karasa magana” kai kawai na gyada masa na mike na koma daki, dama nagaji da zaman. Shiko sadiq binta yayi da kallo, cikin so da kaunarta gami da tausayinta, ya lura tabbas akwai abunda yake damunta, a yanzu amma ze tambayeta da safe yaji. Ina shiga daki na kwanta saboda nemawa kaina nutsuwa dan har wani jiri_jiri nakeji yana dibata.