
Apart din daddy kuwa, yau yaran gidan duk basu je canba, mustapha yana part dinsa suhailat kuma taje gurinsa,dama sune suka fiya zama a part dinnasa. Mommy ce kawai tare da daddy suke hira. Daddy yana lura da lokacin da maryam take zuwa gaishesa, yauseyaga har lokacin ya wuce bata zoba, har an fara kiran sallar isha’i a wasu masallatan. Duban mommy yayi danyakasa hakuri, domin aduk lokacin dayaga maryam zuciyarsa na kokarin tuno masa wani abu daya manta. Yace, “hajiya yau kinga yarinyarnan shiru batazo gaidaniba ko lafiya” takaicine yaturnike mommy, bedamu da yayansa nacikinsa dabasu zoba sewatacan daban, danne rashin jindadin hakan tayi tace, “kasan jiki da jini, kilan tadawo daga makaranta ta gajine, amma innakoma part din zantambayeta dalili.” “Hakane, ai yarinyarma tana da kokari gata da hankali da nutsuwa daga ganinta daga gidan tarbiyya tafito” daddy yafadi haka yana mikewa domin zuwa yayi alwala yatafi masallaci. Wani kallo mommy tabishi dashi batace komaiba, se abubuwan datake kissimawa aranta. Shidai daddy toilet yanufa yayi alwalarsa yafice.
_____________________________
MUSTAPHA
_____________________________
Komai na tafiyar masa yanda yakamata, musamman agurin aiki, dasukayi promotion din dazasuyi, amma duk da haka yanzu basosai yake samun kansaba, tunda daddy yana gari. Kullum bayan magriba seyaje sun tattaunawa akan harkar kasuwancinnasu, se can dare yake samun kansa. Yau kam daya dawo akwai aikin dazeyi shiyasa beje part din daddyba sedai waya da sukayi, yana dawowa daga masallaci yadukufa akan system. Suhailat bayan ta dawo daga school da yamma likis kamar kodayaushe. Wanka tayi ta shirya cikin wasu hadaddun kaya riga da skirt yan kanti. Tayi kyau sosai, ta bulbule jikinta da turaruka se tashin kamshi takeyi. Yau sotakeyi ta gigita yayannata, tayanda zata samo yayarda ta tabashi, tayi matukar kewar lallausar fatarsa. Cikin takunta na kasaita da isa ta fito tanufi part dinnasa. Kamar kodayaushe kofarsa abude take, shi mutumne ba’abocin yawan rufe kofaba, saboda yatsani ayi knocking yataso yabude, shiyasa yake barinsu a bude, se can dare yake rufewa. bedroom dinsane kawai idan yana ciki yake kullewa. Afalonsa na kasa tatarar dashi, wata dagowar ajiyar zuciya ta sauke tafara binsa da kallo tamkar zata lashesa. Singlet ce ajikinsa da wando three quarter, kasancewar lokacin zafi yashigo yanzu, danshi Allah yahalicceshi mutum ne mejin zafi ajikinsa, shiyasa baya kaunar zafi kokakan. Sallama ta masa,dagowa yayi da sauri yana kallonta dan besan da shigowartaba, kallonta yayi na wasu sakanni, sannan yamaida kansa kan abunda yakeyi bayan ya amsa mata sallamar. Zama suhailat tayi a gefensa cikin faduwar gaba, domin taga daya ganta maimakon yayi murna sema bata rai dayayi. Kurawa damtsensa da kirjinsa ido tayi, tana hadiyar yawu. Sotake takai hannu tatabasa kotaji dadi amma babu fuska, tarasa meyasa yake mata haka yanzu, baya bata duk wata kulawa data dace ta soyayya. Magana tayi masa amma yashareta, batasan haushinta yake jiba saboda shigar datayi, duk da ita suhailat aganinta tayi shigar mutunci,dan tasan halinsa. Cikin raunin murya suhailat ta kara masa magana da fadin, “haba yaya meyasa kakemun hakane yanzu, baka nemana karage duk wata kulawa da kake bani, idannazo gurinkama kokuma inmun hadu, sedai kaita batamun rai, baka sakarmun fuska, pls yaya idan wani abunnamaka kayi hakuri mu koma kamar da, zuciyata baza ta iya jurar wannan yanayinba, kasan ina tsananin sonka da kaunarka.” Takarashe maganar da sakin kuka, domin harga ALLAH soyayyarsa na azabatar da ita. Runtse idanunsa yayi, cikin tausayinta. Shikansa bazece ga dalilin dayasa yake mata hakaba. Suhailat tana bukatar kulawarshi, tunda tana tsananin sonsa kuma itace matar daze aura, shi halayentane bayaso amma idan yatuna ba itace babbar me lefiba, lefin mommy ne, tunda itace bata tsawatarmata seyaji haushinta dayakeji yaragu. Ahankali yakai hannu, ya kwantar da kanta akan kafadarsa batare dayace mata komaiba, yaci gaba da aikinsa. Wasu ajiyar zuciya suhailat tahau saukewa, dama abunda takeso kenan, tasan hakan daya mata alamun rarrashine. Lumshe idonta tayi cikin jin dadi tana shakar kamshinsa. Can kuma ta bude idonta ta kurawa kyakkyawar fuskarsa ido, gaskiya tayi dace da masoyi, abunda yake kara rikitata kenan akansa kyawunsa, tarasa ina yasamo wannan kyannasa, tunda mommy da daddy basu kaisa kyauba, a familynsuma kaf tana tunanin babu me kyawunsa. Badon yagama aikinba ya ture system din yace ta bashi labari,bayan yarabata da jikinsa. Aiko suhailat ansamu abunyi nantaita masa zuba, cikin jin dadi, danma yarage mata jin dadin, daya rabata da jikinsa. seda aka kira sallar isha’i tatafi, shima badon tasoba danma dai yace ze kirata anjimane.
Yau a part dinmu sukayi dinner,danaje serving dinsu mommy tatambayeni meyasa banje nagaida daddy ba nace mata baccine yadaukeni. bansaniba. Yaya sadiq kam yaubezo gurin dinner dinba, bankuma San daliliba. Haidar nata kwasata da hira, suhailat kuwa sedai harare harare dataketa wullomun, batasan bata ita nakeba abunda ke kainama yafi karfina,dakyar ma na iya serving dinnasu na koma daki. Saboda bana hayyacina ko yunwa banaji, kokari kawai nakeyi nacire tunanin yaya mustapha daga zuciyata, amma abun yaci tura, fuskarsa kawai nake gani a idona, ga wata jarababbebiyar kewarsa data addabeni amma na kudurcewa raina kozan mutu bazanbari mukara haduwa dashiba saidai bisa tsautsayi. Dama tunda daddy yadawo mommy ba sosai take aikena part dinsaba kamarda. Haka naita juye, juye akan gado ina tunane_tunane, gashi cikina ciwo yakemun nasan lokacin yin al’adatane yayi, namamanta banyiwa yaya sadiq zancen wayar daya baniba, seda nadawo naganta natuna,killaceta nayi dasafe inzan wuce school nabasa. Ana wata ga wata, gadamuwa nacimun rai, gakuma azababben ciwon ciki, daya addabamun kamar kodayaushe idan zanyi period. Ko motsawa nakasayi balle nayi yunkurin fita karbo magani agurin mommy, gashi dare yana karayi. Dafe cikin kawai nayi ina salati, gabadaya nahada uban gumi, se murkukusu nakeyi. Secan zuwa dare nasamu yalafamun bayan nafarajin alamun digar jinin daga jikina, bankaiga yunkurin mikewaba wani wahalallen bacci yadaukeni.
Ban farkaba se cikin dare, jikina duk yamun tsami, kirjina har wani nauyi yakemun saboda damuwa, ga wani azababben ciwon kai. haka na daure nashiga toilet na tsafatace jikina nadawo na kwanta jikina sam babu kwari kasala duk ta lullubeni ga wani sanyi danake ji yana ratsa jikina, kuma nakasa tashi inkashe koda fankane, se lulluba nayi da bargo. a wahalcedai nakarasa daren yau.
Washegari, da zazzabi natashi mezafi ajikina, hakan yasa nakasa koda tashi daga kwancen danake. Mommy dakanta taje har dakin maryam danganin shiru bata fitoba, ganin halin datake ciki mommy ta kira family doctor dinsu yazo ya duba maryam. Dan taga maryam din najin jiki se rawar dari takeyi. Allura doctor din yamun tare da bani magunguna. Baba talatu mommy takira tazo ta kula dani, baccine yakara daukeni. Baba talatu ita ta fanshi maryam tayi ayyukan part din. Se wajen 1 na farka, alhamdulillah naji dadin jikina sedai kasalar jiki. Yau kam ba batun zuwa school dama Friday ce. Tea me kauri baba talatu ta hadamun nasha tanata jeramun sannu, anan take sanarmun sadiq yazo har sau biyu bantashiba. Danasha tea din kuma senaji dadi sosai, wanka nayi nadawo nakara kwanciya.