Uncategorized

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE HAUSA NOVEL

Alhamdulillah,kafin yamma na wartsake zazzabin yasauka,kodan nasha maganine. yaya sadiq yakara dawowa yamun sannu. Amma suhailat mun hadu kotamun sannu, kuma nasan tasan bani da lafiya. Hakan bedameniba tunda gashi Allah ya bani lafiya. Littafin literature nadauka, naduba saboda ta kansa zamu fara exam ran Monday. Da daddare danaje gaida daddy, yayitamun sannu haryana cewa dahar part dinma zezo yadubani da kansa sekuma gani nazo. Bayan nadawo muka hadu sa yaya sadiq,namasa zancen maido masa da waya, seya nunamun bacin ransa akan hakan, yakuma ce inada bukatar rike waya nima kodan karatu da sauran abubuwa, nakuma dinga gaisawa da kawaye da yan’uwana,nace masa mommy bazatayi fadaba, yacemun ba’abun da zatace, dan yasaimun waya. Dakko wayar nayi ya kunnata, dama acike take yacazamun ita, nunamun duk yanda zanyi amfani da ita yayi, yakuma bude mun abubuwa. Godiya na masa sosai, muka cigaba da hirarmu cikin nishadi, ammafa duk abunda ke faruwa ayinin yau tunanin yaya mustapha nanan daram araina kamar kodayaushe, babu abunda yaragu daurewa kawai nakeyi a kokarina nason cireshi daga raina,dan ma naganshi dazu a part din daddy kewarsa ta ragu daga raina………..✍️

Ku dakaceni zuwa dare, zankara Baku wani da yardar Allah, inason nakarashe book din kafin azumine,idan Allah yabani iko. naso muku typing fiye da wannan, amma gaba daya zafi ya hargitsani????

BY
zeey kumurya
ABUNDA KA SHUKA………
(shizaka girba)

MALLAKIN
????
ZAINAB USMAN KUMURYA

FARIN JINI WRITERS ASSO…..????

~Free novel~

Bismillahirrahmanirrahim

2️⃣7️⃣

DEDICATED TO FAUZIYA S MADAKI (MY AUTA) much love dear????????????????????

_____________________________
AFTER SIX MONTHS
_____________________________

……….Rayuwa nata tafiya tamkar gudun ruwa, (Allah yasa mudace) yau gashi harnayi kusan wata takwas agidan alh, menasara. Nasamu cigaba agidan sosai ta fannin ilimi, dan yanzu gashi harmun shiga ss3. Azaman danayi na watanninan agidan bakaramin canzawa nayiba, nakara kyau da fari, dama bakin na wahalane da hayaki. Canzawar danayi bata wasa bace, naxama kalar yayan masu kudinnan, fatata tacanza tayi kyau tayi sumul_sumul,hatta gashin kaina yacanza yakara baki da tsawo saboda gyara. Komai na gayu da amfanin ya mace yayasadiq yana saimun, har yawa sukemun nake bayarwa,kuma ba’amun iyaka da duk wani abunci kosha agidan,yanda yayan gidan zasuci nima haka zanci komene son raina . Zuwa yanzun kaina ya waye sosai, amma ba irin wayewa wacca ba’asoba wayewa tasanin rayuwa. Zuwa yanzu turanci yazauna sosai abakina, littattafan addinima nasansu sosai, kur’ani me girmama nakusa saukeshi. Gaskiya babu abunda zancewa yaya sadiq domin shine silar zamana komai arayuwa. Zuwa yanzun shakuwa me karfi tashiga tsakanina da yaya sadiq,duk wata damuwata yasani nima nasan tasa, shine abokin shawarata. sedaifa har yanzu babu digon sonsa acikin zuciyata, son mustapha ne zaune daram araina, nayi ina yina da kokarin ganin nacire sonnasa amma nakasa, amma duk da haka ina iyakar kokarina wajen ganin nabawa yaya sadiq kulawa yanda kamata, kamar yadda yake bani. Soyayya mukeyi me tsafta da tsari, koda hannuna yaya sadiq betaba rikewaba. Kuma har wannan lokacin aboye mukeyin soyayyartamu,babu Wanda yasani sedai zee dana fada mata tun farko. danko saleemah banfadawaba haryanzu. Aliya tadawo har sau biyu, amma aunty sau daya takara dawowa,nima naje har kadunan na musu wuni guda, tarema mukaje da yaya sadiq. Naje unguwarmu wajen gwaggo dasu saleemat sosai, dan yanzu duk sanda nakeson fita yaya sadiq yana kaini, har gidan kawayena. Saleemat tataba zuwa gurina sau daya, shima dakyar umma tabarta. Gwaggo kuwa tasha cemun zatabiyoni idannaje sena mata wayo nagud,do,dannasan idan tazo kunyatani zatayi.

Zaman danayi ayanzu nagane halin kowa nagidan dakuma yanayin gidan. Shidai megidan yana da kirki sosai, gashi bashida fariya ko karya, Allah yabashi kudin daze iyayin abubuwa na jindadin rayuwa, amma kuma yanayin komai nasa daidai misali baya zafafawa. Yanada gidajen mai, da makarantu na boko dana islamiyya, da kamfanunnuka na sarrafa abubuwa, sannan gashi mutum ne meyawan sadaka da kyauta. sabanin mommy datake komai nata cikin fariya da nuna isa gami da gadara, amma haryau nakasa gane halinta,wani lokacin tamaka kirki, wani lokacin kuma rashin kirki. gidan alh, menasara basayin baki kwata_kwata, kawayen mommy ne kadai suke zuwa se su aunty. Amma ko yan’uwan ta bantaba ganiba agidan tunda nazo. Suhailat halin mommy ne da ita Sak, babu ta Inda tabarta, kamar yadda suke tsananin kama. Har yanzu tsakanina da ita kyara da hantara,narasa meyasa ta tsaneni haka. Su zannurain da haidar kuwa, yanzu nasamu lafiya musammanma haidar shiri muke dashi sosai har karatun boko yana koyamun abunda banganeba. Sai heartbeat (mustapha) sunan danasa masa kenan. Shima na fuskanci wasu daga cikin halayennasa.Shi mutum ne miskili,irin miskilancinnan me cin rai nashariya. amma gaskiya yanada kirki sosai, kuma sam baya shiga sabgar mutane, kuma bayason raini akwai tsare gida, shiyasa kannensa suke masifar tsoronsa, last kuma shi masifaffene,nakarshe idan aka tabosa. Daddy mutum ne metafiye_tafiye, amma idan yaxo gida yana jimawa kafin yakoma. Yaya sadiq ma yanzu baya wata agida seyayi tafiya,harkar kasuwancinsu. Yau laraba, sakaliyar yammace, zaune nake nikadai a garden ina tunanin rayuwa. Yaya sadiq bayanan yayi tafiya tun shekaran jiya. Kewarsa gaba daya tacikamun zuciya, shiyasama nazo garden din na zauna, kullum anan muke tadinmu nudashi. Nikam haryanzu hankalina yakasa kwanciya akan soyayyarmu dashi nasan zeyi wahala su mommy su amince masa ya aureni, dandai yadagene. aduk lokacin dana fada masa haka, seyayta lallabani yana bani baki akan zasu amince. Tunani nakeyi akan maganarmu dashi last kafin yatafi, yacemun dazarar yadawo zefadawa daddy abunda ke tsakaninmu shiyagaji da wannan boye_boyen damukeyi. inda naji dadima daddyn bayanan kuma bedade dayin tafiyarba. Ganin magriba tagabato sena nabar garden din. Ina cikin tafiya kafinnakarasa part dinmu, nahango motar tashigo. Haka kawai naji gabada yafadi bankuma san daliliba. tsayawa nayi danganin waze fito daga motar. Wata sassanyar ajiyar zuciya na sauke ganin Wanda yafito bayan drivernsa yabude masa murfin motar, yaya mustapha ne ashe shiyasa zuciya ta tahau luguden bugun data saba aduk sanda naganshi, lumshe ido nayi cikin wani irin yanayi. “Oh ni maryam, bansan sanda zandena son wannan bawan Allahn ba.” Nafadi haka afili cikin tsananin damuwa. Nayi iyakar yina wajen ganin nacire sonsa daga zuciyata amma abu yafaskara, narasa wannan wacce irin kaddara ce. Gashi wani irin zazzafan so nake masa, wanda idan nawuni bangansaba gabadaya fita nake daga hayyacina,narasa mekemun dadi aduniya,harse nagansa nake samun nutsuwa. Yanzunma dana gansa bakaramin dadi najiba, gaskiya so bemun adalciba nikadai nasan irin wahalar da zuciyata takesha akan bawan Allah nan, mutumin da nasan yamun nisa nahar abada, bazantaba samunsaba, domin nikaina nasan niba kalarsa bace, yawuce ajina. idanma na samesa ina zan iya kishi da suhailat? Yanda take tsananin sonsa, bata iya boye soyyayar datake masa agaban kowa manuna masa kauna takeyi,tsaf zata iya wa mutum illa akansa. Anma fara zancen bikinsu tunda suhailat din tana level 4 ne yanzu, tana kammalawa kuma za’asha bikinsu. Cikin sanyin jiki naja kafata datamun sanyi nacigaba da tafiya.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button