
Mommy natarar zaune afalo ita kadai, sannu namata ina kokarin shiga dakina ta kirani. Dawowa nayi na tsugunna agabanta. “Yawwa maryam, tundazu nake nemanki,binta tacemun kinfita garden, kinsan saura kwana 3 Christmas gobe su kuku zasu tafi garinsu se bayan 2 week zasu dawo, yanzu aikinki yadadu a gidannan harda girki kezaki fanshesa, inafatan kin iya girkin ai” dagamata kai nayi alamar eh. “Ohk, sannan kuma se gyaran part din son shima duk masu masa aikin dasuke masa zasu tafi tarene, zaki dinga zuwa kina masa tun sassafe kafin kitafi school danshi yafison kafin yafito yaga angama masa komai,.” Damma kirjina ya buga, gabana yayanke yafadi, yanzu part dinsa zandinga zuwa gyarawa, meyasa mommy bazata tura waniba seni, nifa adole nake barin muna haduwa dashi, danba yanda zanyine,amma gashi mommy takara kusantamu, dan babu tayanda za’ayi nagama gyara part dinsa duka ace bamu hadu b…”maryam!” Mommy takatsemun tunani da kiran sunana. “Na’am” na’amsa ina sauke numfashi. “Dafatan kinji duka abunda nace miki kuma zaki kiyaye.” “Insha Allah mommy” “yawwa daga gobe zaki fara, zaki iya tashi ki tafi” ahankali na mike nafara tafiya tamkar wadda kwai yafashewa aciki.
bani da zabi banda bin umarnin mommy tunda aikinta nakeyi agidan. Da wuri nayanke shawarar zan kwanta yau, saboda karnayi latti gurin tashi da wuri gobe,tunda aikina ya ninku akannada. bayan nayi serving dinsu nima naci abincin na kwanta. Ina kwanciya naji wayata na vibrate nasan yaya sadiq ne. Janyota nayi nadaga tare yin sallama,cikin danne abunda kedamuna. Daga daya bangaren yaya sadiq yace,
“Wa’alaikissalam tauraruwar zuciyata, harnaji dadi danaji wannan daddadar muryartaki, wata nutsuwace ta lullubeni, dako gaba daya nakasa aiwatar da komai”
Murmushi nayi nace,
“Nima inanan kewarka ta hanani sukuni,yayana”
“Uhm, shine kokikirani balle kimun dan text ko?”
“Sorry yayana, nasan kana aikine shiyasa amma ai namaka sakon zuciya da zuciya, shi’ai nasan ya’iso gareka”
Murmushi yayi me sauti cikin jin dadin kalamanta yace,
“Naganshi indai wannanne, dafatan nima kibiyar dana harbo miki ta reply ta karaso gareki”
“Ehhh, mana tunyaushe shiyasama kaga ai nakai haryanzu kalau, dabata karasoba datuni katawo jinya ai,danda bazankai yanzu lafiya kalauba”….
Hira muka cigaba dayi irinta ta masoya, duk da ni karfin hali kawai nakeyi, dakyar yaya sadiq yabarni shima danyaji nafara masa shiru alamun bacci yafara Cina. Munagama wayar kuwa bacci yadaukeni bajimawa. Cikin baccina naji ana tabani, dafarko nayi tunanin a baccine sedaga baya naji abun ya girmama,kuma kamar azahiri. Bude idona nayi ahankali, tacikin duhu naga kamar inuwar mutum akaina, wata mahaukaciyar bugu zuciyata tayi tamkar zata faso kirjina tafito, cikin tsananin firgici da tsorata nayi yunkurin mikewa zaune, amma aka mayar dani kwancen danake aka danneni da karfi tamkar za’a ballani,numfashinama dakyar yake fita. Wani irin kamshi me kamar kaurine yake tashi daga jikin mutumin, irin wanda naji randa aka taba shigomun daki. runtse idona nayi jikina gaba daya yahau kyarma, addu’ar neman tsari daga Allah nafara karantowa araina, domin shikadai gareni ahalin yanzu kuma shine kadai ze iya kubutar dani. Cikin wata irin dashashshiyar murya mutumin yafara magana. “Yarinya yau babu me kwatarki ahannuna, yau sena cika burina na karshe arayuwa akanki, yau mafarkin dana dade Inayi ze tabbata agaskiya, kece cikar burina na karshe arayuwa,dan haka dole nacikawa kaina burinaaaa!!!!……….✍️
kyan alkawari cikawa, kutaba wannan,ko editing banyiba. zamu hadu gobe, insha Allah
By
zeey kumurya
ABUNDA KA SHUKA………
(shizaka girba)
MALLAKIN
????
ZAINAB USMAN KUMURYA
FARIN JINI WRITERS ASSO…..????
~Free novel~
Bismillahirrahmanirrahim
2️⃣8️⃣
………….Cikin wani irin karfi danaji yaziyarceni na hankade mutumin daga kaina tare da mikewa zaune da Sauri ina maida numfashi,da sauri da sauri. jabaya nafarayi cikin tsananin tsorata gami da razani, bakina nacigaba da karanto addu’ar neman tsarin daga ubangiji ,kafin na kara wani yunkuri mutumin yakara yowa kaina, cikin azama naja baya sosai harnakai karshen gado, sonake na kurma ihu,kozan samu dauki amma nakasa tamkar ansa super glue anrufemun baki,nakasa koda motsashi,ga wani kauri_kauri dake tashi daga jikin mutumin dayake kokarin tarwatsamun kaina. saboda tsabar tsorata cikina se har wani kugi yakemun. Hannunsa yakuma sawa yadamki gashin kaina da karfi yana kokarin maidani kasa, saboda tsananin azabar data ziyarceni, bansan sanda nadankara masa cizo a gefen wuyansaba. Wata yar siririyar kara yasaki tare da sakina yasauka daga kan gadon da sauri,ya fice daga dakin da gudu. Nima cikin fitar hayyaci nasakko,nabi bayansa numfashina nafita dakyar, banmasan inda nake jefa kafataba,hannuna dafe da kaina dayake mugun saramun gami da juyamun, ina fita falo naga wayam babu kowa harya fece, kuma falon akawai haske balle ince buya yayi, daidai lokacin mommy tafito daga dakinta cikin firgici ta fara fadin, “maryam lafiya meke faruwa, naji anbuga kofar falo da karfi” ban iya bata amsaba saboda wani jiri daya kwasheni nayi kasa luuuu zanfadi, dasauri mommy tataho tatarota jikinta, girgiza maryam tahauyi tana tambayarta lafiya,maryam batamasan tana yiba tatafi duniyar suma. Daukar maryam mommy tayi takaita dakinta ta kwantar da ita akan gado. Ruwa me sanyi ta debo tahau shafawa maryam a fuskarta zuwa wuyanta,kusan 12 minutes tana mata haka, kafin maryam taja wani dogon numfashi, ajiyar zuciya mommy tasauke ganin maryam ta farfado, hartaji sanyi aranta kar yar mutane, ta mace mata. “Maryam,maryam,maryam!” Naji muryar mommy asama tana kiran sunana, ahankali na bude idona dayaymun nauyi ina kallonta dishi_dishi, sonake namata magana amma nakasa harshena yamun nauyi, tunanin abunda yafaru nake kokarin yi, amma nakasa,ga wata sarawa da kaina yakemun tamkar ze rabe biyu. Duk da bana cikin nutsuwata amma yanayin mommy dana fuskanta, gaba daya arude take, har wani gumi naga tana hadawa. Mayar da idona nayi na lumshe,cikin karfin hali nafara karanto addu’a acikin raina, cikin ikon Allah bansan sanda bacci ya daukeniba….
Ahankali na bude idona Wanda hakan yayi daidai da kiran sallar asuba da’ake kwadawa. Ahankali na yunkura na tashi zaune ina karewa dakin mommy kallo, jikina rass najishi babu ciwon komai kamar jiya. tunanin abunda yafaru har ganni adakin mommy nake kokarin yi amma nakasa, hakura nayi da tunanin na sakko daga kan gadon nanufi toilet domin yin alwala, abunda ya bani mamaki mommy bata dakin. Koda nafito daga toilet din sena ga mommy zaune akan dadduma da hijabi ajikinta. Kallon maryam mommy tahauyi cikin kura mata ido, nidai kasa nayi da kaina ina kokarin gaisheta naji tace, “maryam harkin tashi, yakikejin kannaki yanzu?” cikin sanyin murya nace mata, “dasauki mommy,yama tafi duka” “masha Allah haka akeso, ga dardumacan dakko sekiyi sallar” dakai na amsa mata na dakko dardumar na shimfida, kaina gaba daya ya kulle narasa tuno mekefaruwa. Jam’i mukabi dukanmu nida mommy, ana idarwa nayi lazimina na mike naiwa mommy sallama nakoma dakina. Dakin na tsaya ina karewa kallo, babu wata alama data nunamun wani abu yafaru, dakin fess dashi setashin kamshin room freshener yakeyi da turaren wuta. Toilet nafada nayo wanka nadawo shap_shap nasaka uniform dina na zunbula hijabi,dakina na tattare kafin gari yayi haske intafi gyaran part din heartbeart.