
6:18,am. Nafito daga part dinmu nanufi nashi, ma’aikatan gidan burjik kowa nata aikinshi a farfajiyar gidan, masu shara nayi masu bawa flower ruwa nayi gasunandai sunata fama. Ahankali nabude kofar part dinnasa bakina dauke da sallama, tsayawa nayi ina karewa falon kasan kallo, namanta rabona dana shigo part dinnan, ancanza komai na falon,tundaga kan kujeru labulaye center carpet komaidai ancanza daga Wanda nasani. Falon fess naganshi babu datti, ga wani daddadan kamshi dayake tashi, toni banmaga abun datti daza’a gyaraba ananba. Ganin zanbatawa kaina lokaci, sena shiga inda mommy tacemun nadakko abun shara, nashare falon, bayan na kwashe yar kurar dana tara nayi mopping din falon, da goge_gogen su TV da dinning. Kafin nagama duk senaji nagaji dan falon yafi na mommy girma. Kitchen din kasan nashiga shima na gyara cikin Sauri danna kusa latti, dama kasannasa babu bedrooms, daga falo se toilet se kitchen, shima toilet din, wankeshi nayi tass,tsaf dai nagyara kasan nanufi sama ganin har 7 ta wuce. Sauri_sauri na fara gyara falon saman,ina cikin goge kan dinning naji wani irin yanayi ajikina, zuciyata ta fara bugawa, da sauri na juyo bayana. Ido hudu mukayi dashi yana tsaye yana kallona, daddadan kamshinsa gaba daya ya mamaye falon, cikin shirinsa na zuwa office yake tsaf harda briefcase dinsa a hannunsa. Shi mustapha mamakin ganin maryam yayi, duk da mommy tafada masa zata turo masu aiki su gyara masa part dinsa beyi tunanin wannan yarinyar zata turo masaba, gashi kuwa abunda bayaso harya fito bata gama aikinba,dama banda abun mommy wannan yar mutsilar yarinyar ina zata iya wani aiki. “Ina kwana” nagaisheshi cikin faduwar gaban kallon danaga yana mini fuskarsa a tsuke, gyadamun kai yayi har lokacin bedena kallonaba, nidai tsaye nayi kaina a kasa nakasa cigaba da aikin, sedanaga yajuya ya fara tafiya sannan na dago ina kallon bayansa harya fice. Ajiyar zuciya nasauke, nahau gulmarsa araina. Yarame, amma bakaramin kyau yakaramunba, nadade banganshi close to close hakaba, sedai gani daga nesa. Wani irin nishadi naji acikin zuciyata dana gansa, gaskiya so bala’ine,senaji dama ya zauna inta kallonsa. Cikin jindadi nakarasa aikin part din nasa. makullin daya ajiye akan kujera nadauka narufe duka kofofi biyun nasama dana kasan part din, sannan na koma part dinmu.mommy dasu binta masu aiki sunata kokarin hada breakfast a kitchen,mukullin part dinnasa nabawa mommy,namusu sannu da aiki na wuce dakina. Karasa shiryawa nayi. Nadakko wayata zan kashe naga missed call din yaya sadiq, dama munsaba kullum kafin natafi school semunyi waya. Banbi bayan kiranba saboda nayi latti, text kawai namasa nakashe wayar, cikin kudin da yaya sadiq yake bani, nadauki 500 nafito natafi.
Koda nadawo daga school nasha aiki sosai, har dare ina fama, ga girkin rana gana dare. Aiko jikina yayi tubus da gajiya…….
Yau kwana 8 dafara aikin gyara part din yaya mustapha,da duka aikin gidan. Yaya sadiq kuma kwanansa biyu da dawowa daga tafiyar da yayi. karfe 6,nagama shirina na nufi part dinshi. cikin tsananin farinciki, inajin dadin wannan aikin,saboda kullum ina ganin heartbeat yanda yakamata,koda naje da wuri nagama aikin, idan befitoba se inta lakai_lakai harse yafito nagansa. Aiko yanzu kullum da murmushi dauke a fuskata nake wuni,yaya sadiq har yakasa hakuri yatambayeni meyake sani farin ciki haka, nace masa duk murnar dawowarsace. Kafin 30 minutes nagama gyaran kasansa, nanufi sama. Inayi ina waigen koze fito amma harna gama ko motsinsa babu, kin tafiya nayi koze fito amma naji shiru mintuna fiye da 15 sun shude befitoba, haka na taso jiki a sabule cikin takaicin rashin ganinsa na fito daga part din,jinake kamar na koma kozan tarar yafito. Abakin part dinmu nayi kicibus da yaya sadiq, cike da mamaki ya tsaya yana kallona. ”Maryam, daga ina haka tundazu Inata jiranki kizo mu wuce na saukeki harna gaji dajira na biyo bayanki.” “Yihakuri yayana, mommy ce ta aikeni nakaiwa yaya mustapha abu” “what!,me kuma mommy ta aikeki kai masa da sassafennan” yafadi haka cikin karaji haryaso ya bani tsoro. Dama banfada masa ina zuwa part din mustapha yimasa aikiba,dannasan seya hanani,nikuma bazanzo hakaba kodan karna dena ganin kyakkyawar fuskar heart beat ina jindadi. “tea nefa tabani nakaimasa” nabashi amsa ina dan bata fuska. Ajiyar zuciya sadiq yasauke yace, “shikenan nizan wuce naga 8 ta kusa, karnayi latti a office driver ya kaiki” yakarashe zancen yana duba agogon hannunsa. “Tom,Adawo lafiya, Allah yakiyaye” “ameen, matar sena dawo kikulamun dakanki. “Insha Allah byeee” nakarashe zancen ina daga masa hannu alamar bye_bye fuskata dauke da murmushi. Adaidai lokacin aunty suhailat tafito daga part dinmu, dasauri kuma naga tajuya takoma ciki. Nima juyawa nayi nashige domin naje nakarasa shirina. “Mom,mom,mom” suhailat take ta kwalawa mommy kira tundaga falo harta shiga dakinta. “Na’am, my daughter irin wannan kira haka” zama suhailat tayi agefen mommy tana fadin, “mom, nifa wani abu nake zargi a gidannan mara yiyuwa” cike da mamaki mommy tace, “banganeba suhailat wanne abune haka” tabe baki suhailat tayi tace, “mom nifa ina zargin waccan kujakar yarinyar yaya sadiq yake soyayya da ita” “wacce yarinya kenan daughter” “hmm,mom kenan. Wacce yarinya garemu banda house girl din gidannan, maryam take kowa,ohi mata” murmushi mommy tayi tace, “haba suhailat,tayaya za’ayi sadiq yayi soyyaya da maryam, kawaidai kinsanshi shina kowane.” “Kai,mom banda irin wannan, tunda ake kawo yara gidannan aikatau wakika taba ganin yayima haka, yanafa kula da yarinyar sosai, yana kashe mata kudi mom kamar bakya ganine” “Ina gani daughter kuma ina sane dashi,amma bandauki hakan da wata manufaba gaskiya,dankinsan sadiq dina damacan shi mutum ne me kyauta da tausayawa mutane.” “Mommy kenan, amma yanda yakeyiwa maryam din hidimane yayi yawa, kulawar dayake bata ta wuce ace iya tausayawace kawai.” Dafa kafadar suhailat mommy tayi tace, “karki damu kanki akan haka daughter zan bincika nagani koma menene zansan tayanda zan bullo masa” “yadai kamata mom,dankaryaje yadakko mana abun kunya,da Allah wadai a idanun jama’a” suhailat ta fadi haka tana mikewa, sallama tayiwa mom ta fice, dama school zata tsegumi yadawo da ita. Zuciyata cike da tunanin yaya mustapha gami da kewarsa, nakarasa shirina nafito nayiwa mommy sallama nafice. Harna nufi gurin danasan driver yana jirana senaji ina, bazan iya barin gidaba batare dana ganshiba nariga dana sabarwa idona da zuciyata da ganinsa kullum, ahankali na juya nanufi part dinnashi,haka kawai naji zuciyata na bugawa, gashi kuma ina danjin tsoron bansan mezance masaba,idannakoma. Ahankali na tura kofar falon kasa senajita abude, ajiyar zuciya nasauke cikin farin ciki ganin yananan befitaba. Sama na haye cikin sauri, shima ina tura kofar najita abude. Anan na tsaya kuma ina sake_sake araina,wata zuciyar tanacemun nashiga bedroom dinsa wata zuciyar tana gargadina ga aikata hakan, domin aka’idama hakan bekamataba, kuma shima idan yakamanifa nasan sena yabawa aya zakinta. harjuya kuma senaga ina bazan iya komawa batare dana ganshiba tunda nazo kuma sedai komai zefaru yafaru ta fanjama fanjam,so ya rufemun ido,burina kawai ingansa. Cikin kwarin zuciya na juyo na dawo, duk da bugun da zuciyata takemun haka na runtse ido na bude dakin danasan yana ciki, cikin ikon Allah kuwa kofar dakin abude take, ahankali na tura zuciyata na tsananta bugu, tsayawa nayi ina kallonsa yanda yake kwance akan makeken gadonsa,tamkar gawa. Jikinsa gabadaya alullube yake da bargo, fuskarsa ce kawai a bude, idanunsa a lumshe da’alama bacci yakeyi. Cikin sanda nafara taku, harnaje gaban gadon natsaya ina kallonsa, ina sauke ajiyar zuciya akai_akai. Ina tunanin intasheshi amma kuma inajin tsoro, atunanina baccine yadaukesa batare dayasan lokaci yayi hakaba. “Maryam,karkiyi kuskuren haka,tunda dai kinganshi hankakinki ya kwanta kitafi kawai,kar tsautsayi yasashi farkawa yaganki tsaye akansa,mezakice masa yakawoki dakinsa” wata zuciyar ta gargadeni da aikata haka. Badon nasoba sedan tsorandanakeji najuya nafara tafiya,ina tafe ina waigensa harna fice daga dakin. Senajini duk wani iri,zuciyata sam babu dadi,kamar wani abu mara dadi nashirin faruwa dani. Haka kawai naji hankalina sam yakasa kwanciya bankuma san daliliba. Inda driver yake jirana naje nasamesa, nasanma harya gaji da jirana……….