
Juyowa umma tayi tana kallona,hawayene kawai yake kwaranya daga idona har lokacin. Tabbas taji wani kamshi a jikina,amma hakan bazesa ta gasgata maganar gwaggoba,domin tasan maryam tasan halinta ciki da waje tasan abunda zatayi da Wanda bazatayiba. “Maryam kifada mana gaskiyar abunda ya faru.labarin komai na kwashe na fadawa umma, amma kawai senaji nauyin dace mata na fadi ajikinsa,kawai sena cemata bugeshi nayi. Karyata maganata gwaggo tayi,tana cewa “wanne irin kamshine wannan daga ka buge mutum seya zauna ajikinka,inma zanfadi gaskiya infada,ai dama bayau na fara zuwa yawon karuwancinaba.hakuri umma ta kama bata,wasu matama da suka shigo hakuri suka hau bata. Dakyar gwaggo ta hakura amma da cewa tayi seta karyamun kafa taga da wadda zanna zuwa iskancinnawa. Dukan da gwaggo tamun bedameniba kamar yadda take ta faman aibatani,tana dangantani da Kalmar karuwa,durkusawa nayi agurin ina sakin kuka me tsuma zuciya.lallashina umma ta hauyi da banbaki amma Sam bana cinta bana fahimtar metake cewa, wani zafi zuciyata takemun, ahankali na mike na shige dakina bayan kowa ya watse daga gidannamu…..
9:00 pm,suke hallara akan dinning gaba dayan gidan domin yin break fast,kuku kamar yadda yasaba ya gama komai,ya jera akan dinning. Kowa ya hallara amma banda mustapha. Kiransa mommy tayi har 3 missed call amma bedagaba. Kallon suhaita tayi tace” daughter jeki duba ki gani ko lafiya yau son befitoba. Haidarne yace”haba mommy muci abincinmu kawai kinsanfa shi big bro,bawani damuwa yayi da cin abinci ba.harararsa mommy tayi,idan shi bedamuba nina damu,daughter kiyi sauri kikirawoshi.
Suhailat abunnema ya samu tashi tayi tana yiwa haidar gwalo,ta nufi part dinnasa.Baya falo hakan yasata nufar bedroom dinnasa,yana kwance idanunsa,a lumshe tamkar me bacci.tama manta da wani sakon kiranshi da’akace tayi,shaukinsa da wata muguwar sha’awarsace take fizgarta.fadawa tayi jikinsa,tana shigewa jikinsa,yayi nisa a tunanin yarinyar dabe saniba yaji mutum ajikinsa,abunda suhailat bata zato ba,kuma betaba mataba.jitayi yazagaye bayanta da hannayensa yana shafa bayan ta,yana kara matseta ajikinsa.cikin tsananin jin dadi Mara misaltuwa.suhaital ta fara kokarin kissing dinsa,soyake yaji irin yanayin dayaji dazu amma bejiba,ahankali ya bude dara_daran idansa,akan fuskar suhailat ya sauke su,da sauri ya tureta daga jikinsa, tare da mikewa zaune. ransa a matukar bace. Itama suhailat din tashi tayi ganin yanda lokaci daya ya sauya,zatayi magana yanuna mata hanyar kofa,tashi tayi tana turo baki gaba ta fice daga dakin.
Tunda mommy taganta tasha jinin jikinta,ganin yanda take babbata rai,dariya haidar da zannuraini suka kwashe da ita. Haidar yace”dama seda na fada miki karkije kokinjema baze zebo. Harararsa tayi tamkar zatayi kuka tace”mommy kinga su yaa haidar ko? Mikewa mommy tayi tace”kyaleni dasu daughter.Ku zauna,kuci abincinku bari naje na sameshi.
Yana zaune kamar yanda suhailat ta barshi,mommy tashigo bedroom dinnasa.zama tayi agefensa,tare da jawoshi jikinta.cikin rarrashi tafara magana “haba my son,meyasa bakason cin abinci,baka tsoron wani ciwon yakama munkai,please kazo muje muyi dinner.shagwabe fuska yayi sekace yaro yace.” Mommy a koshe nakefa, ni tea kawai zansha. Shafa kansa mommy tayi cikin tsananin kaunarsa, “shikenan my son bari naje ha hado maka. Dakanta ta dafa masa a kitchen din part dinsa,seda yasha sosai tana lallabashi kamar karamin yaro,sannan ta kyaleshi.tana fita ya nufi toilet yasakarwa kansa ruwa koyaji sanyi aransa.domin gaba daya yarasa meke damunsa……
Tunda nashiga daki nake kukan tausayin rayuwata,kusan minti goma gwaggo ta shigo dakin. “Dan ubanki bazaki tashi kikarasa sauran ayyikankiba,maganarta cikin tsawa ta sani dagowa da sauri,mikewa nayi na nufi hanyar fita.jikina a sanyaye nake aikin yau,tunanin dan gayun dana gani yamun tsaye acikin zuciyata. Seda sha biyun dare ta wuce na samu kaina,domin har girki seda nayi. Bayan na karayin wanka nayi sallar isha’i na kwanta akan tabarmata.saboda tarin gajiya da ciwon kan dake damuna saboda kukan danayi tuni bacci ya kwasheni,cikin mintuna kalilan.
*************
Karfe 7:30am,ya gama shirinsa tsaf na zuwa office. Ko break beyiba saboda batashi yakeba,mommy ma awaya ya sanar mata ya tafi.ma’aikatan gidanne suketa gaishesa,hannu kawai yake daga musu. Drivernsa,yana hangosa ya fito da sauri tare da bude masa gaban motar yana gaisheshi. Shima hannu kawai yadaga masa. Ya shige motar.
7:45 sun isa ma’aikatar tasu,kullum haka yake zuwa baya latti,saboda shi bayason karya ka’ida.driver na rike da briefcase dinsa har office dinsa.ma’aikata se kwasar gaisuwa sukeyi a gurinsa. Zama yayi akan kujerarsa.sakatariyarsa ce ta shigo office dinnasa,gaishesa tayi tare da dakko masa wasu takardu ta ‘ajiye masa a gabansa,cikin girmamawa.sannan ta juya ta koma wajen zamanta.
Wata budurwace ta shigo ma’aikatar cikin wata rantsatstsiyar mota. Faka motar tata tayi agurin da’aka tanada domin ajiye motoci.tana sanye da wani Riga da siket na atamfa,dinkin Yakama jikinta sosai,ana ganin shatin komai na jikinta.taci daurinta ture kaga tsiya,ta cokaloshi.gashin dokin data kara ya sakko har gadon bayanta. Fuskarta dauke da bakin glass,takalmin dake kafarta me shegen tsinine.hannunta dauke da wayarta,da wata hadaddiyar handbag.wadda tashiga da kayan jikinta.babu mayafi a jikinta.tafiya ta farayi cikin takunta na Jan hankali.duk inda ta ratsa se’an kalleta.office dinsa ta nufa direct. Sakatariya tana zaune taga mata tashigo ta wuceta,magana ta fara mata tana kokarin dakatar da ita,amma ko juyowa batayi ta kalletaba.batare da Neman iziniba ta murda handle din kofar office din tashige. Yana cikin danne_danne a laptop,kawai yaga mace ta shigo masa,ba sallama. Dagowa yayi cike da tsantsar mamaki yana kallonta. Karasowa tayi gaban table dinnasa, Jakarta ta ajiye akai,tare da zare glass din dake sanye a idanunta,shima ta ajiyeshi. Zama tayi akan daya daga kujerun dake gaban table dinnasa,tare da Dora kafa daya kan daya.kallonta kawai ya tsaya yakeyi yanda ta dage tana abubuwa sekace office din ubanta.
Murmushi tayi akaron farko tana wani fari da idonta tace” mustapha sulaiman me nasara kallon mamaki kakemun ko? Aidama na fada maka bazan barkaba,kuma bazan dena bibiyarkaba harse ka soni, kota tsiya kota arziki………✍️
BY
zeey kumurya
ABUNDA KA SHUKA………
(shizaka girba)
MALLAKIN
????
ZAINAB USMAN KUMURYA
FARIN JINI WRITERS ASSO…..????
~Free novel~
Bismillahirrahmanirrahim
0️⃣4️⃣
……….mtssss yaja wani dogon tsaki,ya maida hankalinsa akan abunda yakeyi batare da yace mata kalaba,domin shi bashi da lokacinta.kara gyara zama tayi tana kallonsa tamkar zata lashesa.wayar dake gefensa ya latsa tare da karawa a kunne. “Kizo yanzu” kawai ya furta tare da kashe wayar.ya hade girar sama data kasa.sakatariyarsace ta shigo office din da sallama. Cikin girmamawa tace. “Sir gani” dagowa yayi yana dubanta,budurwar data shigo ya nuna mata da hannu batare da yace komaiba. Ta gane meyake nufi,maida dubanta tayi ga budurwar wadda take ta taunar cingum dinta hankali kwance,tana girgirza kafafuwanta.bayani ta fara masa cikin girmamawa. “Yallabai kawai gani nayi tataho zata shigo office dinka,ina mata magana kuma,ko saurarena batayiba,nayi kokarin hanata amma….Daga mata hannu yayi tare da nuna mata kofa.da hannunsa.ficewa tayi Daga office din,budurwar ta bita da harara.tana jifanta da wani mugun kallo.