Uncategorized

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE HAUSA NOVEL

Gwaggo nafita taga wata tsohuwar kawarta dasuka fi shekara basu haduba. irin matannanne masu zaman saudiya, gatanan fess da ita taci gayunta. wangale baki gwaggo tayi cikin mamaki tace, “hajja gana,dama rai kanga rai” murmushi matar tayi tace, “gashi kuwa ladi mun hadu” makullin dake hannun gwaggo tasa tabude gidan tana zubawa hajja gana maraba cikin muryar ganinta. Bayan sun shiga gidan, hajja gana tazauna agefen gadon gwaggo adarare saboda kyankyami tace, “wato haryanzu Ladi halinkidai besauyaba na kazanta” bata fuska gwaggo tayi tace, “nifa matsalata dake kenan hajja,shegen tsantsaini iyayin tsiya,kinsaba da saudiya ko’ina fess,aibaza kihada nan da canba,kuma ni gaskiya aiki wahalar dani yakeyi,bazan iya wani bautar gidaba,barinshi nake yaci dattinshi yagama” “Gyada kai hajja, tayi tace. “Amma kin iya fita tun farar safiya gidan makota,ana jiyo muryarki har kwararo kinata kwakwazo” “badole kijini har kwararoba hajja,yarinyace naje nace tarakani gidan da maryam take aikatau amma taki,saboda tsabar bakin hali” “ladi!, wacce maryam din ce take aikatau kuma, badai takiba.?” “Ita mana, ai aikatau nakaita” cike da takaici hajja tace, “amma wlh ladi, Allah wadaran halinki yanzu duk abunda maryam take miki a gidannan shine kika dauketa kikakaita aikatau,saboda zalinci” cikin rashin damuwa gwaggo tace, “yoo duk abunda takemun yafi kudin dazansamune” “hmmm, ladi tsinannen son kudinkine ze kasheki, banda haka dudu nawane kudin aikin da ake biyan masu aiki,nasan bekai ribarki ta sana’ar da yarinyarnan take mikiba” dariya gwaggo tayi tace, “wannan dayawa ne hajja, gidan alh. Menasaranefa take aikin, 200,000 duk wata haka nake jinsu dumus yanzu takai kusan wata tara tana aikin, kudina sunanan a ninke ina tarawa” galala hajja tayi tana kallon gwaggo, tsabar takaicima takasa magana.

Secan ta numfasa tace, “ladi, wlh wlh wlh idan bakiyi wasaba son kudinkine ze kasheki. Tsabar masifa kidauki yarinya kikaita aikatau,ke bakirasa ciba baki rasa shaba, yarinyarnan duk irin bautar datake miki amma be ishekiba sekin cutar da ita h…… “dakata hajja, wai meyasa kowa yazo seya dinga bankyautaba,bankyataba, danna kai maryam aikatau. Yarinyarnan fa tawace, duk wanda zesota abayana yake, kuma aikinnan data tafi, hutantane dacigabanta itama. Bakiga yanda ta canzaba tayi bul_bul abunta tayi fari kal kamar kya tsaga jini yafito ajikinta, kuma sunsata a makaranta to kuma mene faduwa anan,aganinama aise riba data samu” gwaggo takatse hajja dafadin haka cikin masifa. “Ladi,yakamata kidinga tunani akan abubuwan dazaki aikata kafin ki aikata, 200,000 yayi yawa a kudin aiki, ko aikin gwamanati sekana babban aiki zaka samu 200,000” dariya gwaggo tayi tace, “kinmanta kudin mutuminne hajja, kuma gashi da kyauta ance,koda maryam bata masu aiki ayanda ake fadar halinsu ze iya bamu kyauta”Hararar gwaggo hajja tayi tace, “gaskiya ladi haryanzu bakisan duniyaba, to bari kiji infada miki,masu kudi sunfiki son kudinsu, idanma zaki dawo cikin hankalinki kidawo kinsan inda yake miki ciwo. Haka kawai baza’adinga daukar makudan kudi ana baki amatsayin iya na aikin maryam, ninasan halin masu kudi,nazauna da manyan masu kudi, dan haka ina baki shawara kije kidakko maryam tunkafin kiyi danasani, kada kiyi sanadin abunda za’a cutar da marainiyar Allah. Ladi, kinsan illar cutar da maraya kuwa, kiji tsoron Allah mana ladi, duk abunda kikayiwa yarinyarnan abaya be isaba kiba sekin kaita inda……….. “kinga dan Allah hajja, dakata. Niba wa’azai nace kizo kimunba, ku mutane bakwason fadar alkhairi sedai kuyita munana zato, maryam dai bazan dakkota daga gidan aikatauba, sena tara kudin zuwa saudiya da siyen makeken gida, dan haka ki sauraramun. Dan’uwan mijin innama yazo yayi nasa nagaji, dan haka kema kisauraramun,kibarni inyi abunda naso,daga zuwanki karki batan rai.” Kallon gwaggo kawai hajja takeyi cike da mamakin shegen son kudi irinnata, gashi kuma kudinnata baya ciyuwa, tana dai danci acikinta, amma ko suturar arziki bata iya daurawa, kullum ita kenan bin gidajen masu adashi tana zubi. Sanin halin gwaggo na kafiya da naci akan abunda tasa agaba yasa hajja, ta kyaleta da maganar maryama,amma ta kudircewa ranta insha Allah setaje ta dakko maryam dakanta, danyanda duniyarnan ta lalace, ta safarar yara kanana yan mata zuwa kasar waje. itama sam hankalinta beyarda da wannan aikinba,ga uban kudin da’akace ana bayarwa,akan dan aikin gida. abunda mamaki sosai,dama can ita rayuwar yarinyar nabata tausayi. (Gwaggo, yakamata kiyi hankali mana, ayanda kawayenki da suke zugaki akan abunda kikeyiwa maryam ada, amma yanzu duk abunsu su suke kara tunatar dake,abunda kikayi badai_dai bane,amma kinkasa ganewa.)……….


Awanni biyu sun shude,amma har lokacin su mommy basusan halinda mustapha yake cikiba,likitocin dai suna kansa har wannan lokacin. Haidar dakanshi yaje makaranta yadakko suhailat, aiko tana zuwa taji abunda yafaru ta haukata gurin da kuka, tana kiran abarta taje taga mustapha. Wata nurse ce ta tausheta tare da bata baki, aka samu tayi shiru da gunjin datakeyi, mommy kam zuwa yanzu ko magana bata iyayi. Daddyma yakirasu yakai sau biyar domin yaji yanayin jikinnasa, shima yanacan yanata cuku_cukun tahowa naija.

Se wajen daya saura likitocin suka fito gabadaya su mommy sukayi kansu da tambayar yaya jikinnasa. Dr, musaddiq wanda shine babba acikin likitocin ya dubi su mommy yace. “Hajiya ku kwantar da hankalinku munsamu numfashinnasa yadaidaita munma daura masa drip, tare dayimasa allurori,yasamu bacci yanzu” “to yanzu doctor zamu iya shiga muganshi” mommy ta fadi haka da saurinta. “Ehh, zaku iya shiga ku ganshi” ai ko gama rufe bakinsa Dr, beyiba suka nufi dakin dukansu. Duban yaya sadiq Dr, yayi ganin duk yafisu tawakkali yace, “abokina idan badamuwa kasameni a office mana, muyi magana” “ohk badamuwa” yaya sadiq yabashi amsa, tare da bin bayansa zuwa office dinnasa. Mustapha na kwance, akan gadon asibitin dakin dayake, shikadaine adakin se wani gado dake gefennasa. Kusa dashi su mommy suka kasara suka kura masa ido cike da jimami. Gaba daya jikinsu haidar yayi sanyi da ganin halin da yayannasu yake ciki. Duk’abun mutum idan yaga mustapha ahalin dayake ciki seya tausaya masa, lokaci daya ya zabge yayi wata uwar rama, ga numfashinsa dake fita a wahalce, bawan Allah shikadai yasan azabar dayake ji ajikinsa. Kuka suhailat ta fashe dashi tana fadin, “mommy yanzu yayane kwance ahaka kamar gawa, mom dubeshifa yanda yakoma,sekuma karasa gaban gadonnasa tana fashewa da kuka. “mommy kam takasa magana se girgiza kai kawai takeyi hawaye na malala a fuskarta.

Acan office din Dr, kuwa bayan sun shiga sun zauna. Dr yadubi sadiq yace, “sadiq! Agaskiya dan’uwanku yana cikin wani yanayi na mawuyacin hali, numfashinsa gaba daya yayi sama, dakyar muka samu muka shawo kan matsalar, saidaifa wata matsalar daban, duk binkicenmun munkasa gano meke damunshi takamaimai daya yashi a wannan halin,naso ace mahaifiyarku nayiwa wannan bayanin amma naga gaba daya naga a rude take, bazama ta fuskanci me nake cewaba, shiyasa nakiraka kai kazo domin na maka bayani.” Numfasawa yaya sadiq yayi, cikin tsananin damuwa data kasa boyuwa har a fuskarsa yace, “doctor kaina gabadaya ya kulle narasama mezance akan wannan al’amarin,saboda jiya lafiya kalau muka rabu dashi, yau fa kawai akaga yatashi da wannan ciwon metayar da hankali,da sanya rudu a zuciya.” “Haka dama ikon Allah yake yawuce gaban komai, wannan kadanne daga cikin ikonnasa. Fatanmu kawai Allah yabashi lafiya, yanzudai mun dibi jininshi zamu auna, insha Allah zamu gano inda matsalar take semusan abunyi” “tom shikenan Dr, mungode sosai bari naje naga jikinnashi.” Musabaha sukayi sadiq yafice daga office din zuciyarsa Sam babu dadi………

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button