
Kasancewar yau Friday, 12:30 ake tashinmu, kuma duk ran Friday yaya sadiq ne yake zuwa daukata idan yana gari. Idan yadawo daga gurin aiki seya biyo mutafi kafin ya wuce masallacin juma’a. Jiransa natsayi a bakin gate din makaranta, amma shiru_shiru bezoba, babu shi babu driver,nasan wani babban uzurine yatsaidashi. Ganin nayi kusan mintuna 20 atsaye dalibai duk sun tafi, su zeema sunjima da tafiya,ga lokacin masallaci yakusato, nasan yanzu ankusa kashe hanya. Adaidaita sahu na yanke shawarar hawa kawai yakaini gida. dama makarantar tamu akan titi take. Guda daya na tare yace nakawo 100 babu bata lokaci na haye muka nufi gida. Har kofar gida yakaini na ya saukeni nabiyashi hakkinshi. Gaba daya jikina babu dadi kokadan, knocking nayi megadi yazo ya budemun, gaishesa nayi nawuce ciki. Maimakon nayi hanyar part dinmu, sena nufi part din yaya mustapha sonake kawai naganshi, naji dadi azuciyata. Harna kusa zuwa wata zuciyar ta tunatar dani yanzu hakafa yana masallaci saboda lokacin sallah yayi,tokodama bahakaba idannaje mezance masa? Juyawa nayi cikin sanyin jiki nakoma nanufi part dinmu. banci karo da kowaba a part din kasa hakama nasama. gaba daya part dinma tsit najishi. Dakina na wuce nayi wanka tare da dauro alwala, nayi sallah. Ina idarwa bayan nayi lazimi nakaranta khahfi. Kwanciya nayi saboda wani bacci dayake cina, inason naje nacewa mommy nadawo nakuma kunna wayata nakira yaya sadiq nasan yanzu shima yakirani yaji kona dawo gida,amma wani irin bacci nakeji, bari nayi nadan runtsa idan natahi nayi duk abunda zanyi………….
Karfe biyu na rana,a garin kano tayiwa aunty, danma a motor driver dinta yakawota, taso biyo jirgi sekuma taga ze bata mata lokacine kawai. Itakadaima tataho aliya tana school batamasan tatahoba se sallahu tabar mata gurin masu aikinta. Wayar sadiq takira yasanar mata asibitin dasuke suka nufi can. Su mommy ansha kuka ita da suhailat sun hakura sunyi shiru. Se tasashi dasukayi agama suna kallonshi. Su haidar kuwa dakyar sadiq ya taushesu suka nufi masallaci. Daddy ma yakirasu yace jirgin karfe uku zebiyo. Su aunty nashigowa asibitin suka hadu dasu yaya sadiq sundawo daga masallaci. Tunda aunty tagansu taji gabanta yafadi yanda taga fuskokinsu babu walwala kokadan kamar mustaphan mutuwa yayi, tatabbatar bakaramin jiki yake jiba. Ahanzarce ta fito bayan driver yayi parking, tabi bayansu yaya sadiq dasukayi gaba dansu basu gantaba. “Sadiq, sadiq” aunty ta kwalla masa kira lokacin data kusa cimmusu. Gabadaya suka juyo suna kallonta. “Aunty harkin karaso, sannu da zuwa” cewar sadiq. “Nakaraso sadiq yajikinnasa,ina fatan da sauki dai ko” “jiki alhamdulillah za’ace,sauki kam sena Allah.” shiru aunty tayi jin abunda sadiq yace, hankalinta ya kara tashi,dama kwana 2 se mafarkinsa takeyi cikin mawuyacin hali. Gaisheta su zannurain sukayi asanyaye, itama ahakan ta amsa musu suka dunguma zuwa dakin dayake. Mommy nazaune ta rafka uban tagumi,kana ganinta kasan hankalinta sam ba’a kwance yakeba duk ta wani burkice. Doctor ne tsaye akan mustapha yana dubasa, bisa takurawar mommy,ganin mustapha yaki farkawa har yanzu. Da sallama dauke abakunansu duka suka dakin. Doctor ne kawai ya amsa musu amma mommy kodagowa ta kasayi, suhailat kam tatasashi agaba takasa motsawa daga inda ta zauna,se sauke ajiyar zuciya take saukewa akai_akai…………✍️
BY
Zeey kumurya
ABUNDA KA SHUKA………
(shizaka girba)
MALLAKIN
????
ZAINAB USMAN KUMURYA
FARIN JINI WRITERS ASSO…..????
~Free novel~
Bismillahirrahmanirrahim
3️⃣0️⃣
………Karasawa kusa da mommy aunty tayi tagaisheta tare da tambayarta me jiki, cikin dashashshiya gami da sanyin murya mommy ta amsa mata. Tausayin mommy gaba daya yacika aunty, lokaci daya harta rame tayi zuru_zuru,kamar me jinyar itama. Gaisawa aunty sukayi da doctor dayake kokarin fita. “Doctor me’ake ciki ne, dan Allah kafadamun halin da dana yake ciki tun safe amma haryanzu kunkasa gano meke damunshi” mommy ta tsaida Dr, dake kokarin fita da fadin haka idonta na zubar hawaye. Asanyaye Dr yajuyo,shikansa jikinsa yayi sanyi da lamarin, sunyi kwajin jininma amma benuna musu akwai wani abu dake damunsaba, cikin son kwantarwada mommy hankali yace, “hajiya kikara hakuri munakan aikine, insha Allahu kafin dare zamu gano abunda kedamunsa” “to yaushe ze farfado” “shima nanbada jimawaba insha Allah,ciki gaba da masa addu’a kawai.” shiru mommy tayi tana ayyana matukar mustapha be farfado ayauba sesuncanza asibiti, ita barima daddy yazo, kasar gaba daya za’a bari dashi. Gwara suje wata kasar aduba mata lafiyar danta. Cike da tausayawa aunty takebin mustapha da kallo, ita kanta bakaramin tsorata tayiba daganin yanda mustaphan yakomab lokaci daya, ahankali ta karasa daf da dashi takai hannu tataba goshinsa, zafin datajine yasata sauke hannunta dasauri, wannan wanne irin ciwone yake damun sa, zafin jikinsa ba irinna zafin ciwo bane data sani, nasa tamkar ana rura garwashin wuta, ga kuma bayanin dataji Dr,yanayiwa mommy na ba’asanma meke damunsaba. bin jikinsa tacigaba dayi da kallo,gaba daya jikinnasa ya shika ga numfashinsa dake fita dakyar. wani wahalallen numfashi aunty ta sauke afili ta furta. “Ya Allah,kabawa wannan yaro lafiya, kakawo masa sassauci da rangwame acikin wannan ciwon” gaba daya suka hada baki gurin cewa “ameen” jikin aunty gabadaya yayi sanyi, itakam wannan ciwo na mustapha ya firgitata ba kadanba, bata tunanin wannan ciwon na tashine. Kafadar suhailat dake gefenta ta dafa cikin rarrashi tafara mata magana. “Kiyi hakuri suhailat ba kukane mafitaba ahalin yanzu, addu’arki kawai yake bukata” aunty ta karashe zancen da share mata hawaye, ganin tunda tashigo dakin suhailat kuka kawai takeyi. Duk sesukabawa aunty tausayi, tabbas dole duka hankulansu ya tashi domin mustapha tamkar uba yake agurinsu duka, da daddy yana gari dabaya gari, shine ke musu komai, kuma duk da baya sakar musu fuska amma yajasu ajiki sosai, koyaya yaga wani sauyi atattare dasu ze tambayesu menene matsalarsu kuma ya magance musu ita,gwargwadon iyawarsa. mazauni aunty tayiwa kanta, sadiq yana bata bayanin ciwon mustaphan dakuma bayanin da likita ya masa…….
Seda uku na rana ta wuce natashi daga bacci, nayi mamakin dadewar danayi ina baccin, duk da sam baccin bayamun dadi kawaidai yinshi nayi. cikin sauri na sakko daga kangadona nashiga toilet na kuskure baki, dannasan yanzu haka mommy tanacan tana jirana, ga girki zanyi. Nayi zaton ganin yaran gidan a falo kasancewar yau Friday,amma senaga babu kowa. Kofar dakin mommy naje nayi knocking naji shiru, komawa kan kujera nayi nazauna, atunanina tana wani uzurinne,mintuna biyar suka shude naji shiru. Yanke shawara nayi kawai bari naje naduba may be bacci takeyi. Koda nashiga dakin senaga batanan, mamakine yakamani dan gaskiya da wuya kaga mommy batanan a irin wannan lokacin, kuma babu alamun tana toilet,amma nasan banisa tayiba tunda har tabar dakinta abude. Fitowa nayi nanufi kitchen nafara wanke_wanken dabanyiba. Harna gama nakoma dakina nayi sallar la’asar ko motsin bera banjiba a part dinba balle na mutum.
Se a lokacin nadakko wayata na kunna, ina kunnawa sakon yaya sadiq na shigowa,karantawa nafarayi acikin zuciyata kamar haka. my love,am sorry yau banzo na dakkokiba wani babban uzurine yatsaidani, dafatan kina lafiya,tun dazu naketa kiran wayarki akashe. need your du’a sweet murmushi nayi tare da lumshe idona, aduk lokacin danaga wani sako na yaya sadiq koyamun kalamai na soyayya se’inji dama daga gurin yaya mustapha nake jinsu, tausayin yaya sadiq ne yakamani, ganinshi kullum cikin yin abunda zesani farinciki yakeyi amma ni kuma zuciyata naga wani can daban dabemasan ina yiba, aduk lokacin dana tuna haka se inji wani kunci yaziyarci zuciyata, da ina da yanda zanyi dana sauya sonda nakewa yaya mustapha zuwa ga yaya sadiq domin shiya cancanta zuciyata taso, amma kash nayi iya yina amma nakasa yin hakan, kullum son mustapha kara ta’azzara yakeyi acikin zuciyata.