Uncategorized

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE HAUSA NOVEL

kewar wayata duk ta isheni yau, gashi nakasa fadawa kowa tafada bayan gado, seda daddare daza’asawa yaya mustapha karatu nake fadawa aunty, fada tamun akan meyasa banfadaba tundazuba har gashi dare yayi, dole yanzu sedai abari da safe adakkomun. guntun ruwan safe kawai aunty ta shafa masa, tunda babu wayar saka karatun. Yau zannurain da faruq ne zasu kwana dashi tunda sadiq bayanan. Kafin 10 nadare nayi bacci tunda babu waya ahannuna, dama ita takesa nakai 11 a online muna chat da kawayena a group dinmu na school. cikin baccina yauma naji ana lalubata gami da yamutsani da karfin gaske, a matukar firgice na farka ina kokarin kwarara ihu, naji anrufemun baki, irin kaurin danaji wancan karon yauma shinaji, “ya Allah wannan wacce irin masiface da jaraba gami da bala’i waye wannan memugun nufinne?” nafadi haka araina cikin tsananin firgici gami da razani. banyi kasa a gwiwaba gurin karanto addu’a da kokarin kwatar kaina iya iyawata, gabadaya jikina rawa yakeyi zuciyata na harbawa da sauri_da sauri, ga wani jiri_jiri danakeji yana kwasata amma haka nadaure nacigaba da kokarin kwatar kaina, harna samu na kwaci kaina natashi da mike da sauri na sauka daga kan gadon ina kokarin guduwa, dasauri mutumin yabiyo bayana yadamki gashin kaina da karfi, kara na kwalla da iyakacin karfina saboda matsananciyar azabar data ziyarceni, juyo dani mutumin yayi yafara kokarin maidani kan gadon, turjewa nayi naki tafiya, tamkar masu dambe haka mukahau kokawa ninaki yarda yakaini kasa shima yaki hakura, seja baya nakeyi duk da dakin duhune dinkim amma haka nafara laluban kan mudubin dakina kozan samu makami, cikin ikon Allah naji nataba gaban madubin, hannuna nasa nadaki ruwan madubin da karfi, jikake bassss! Yayi kara ya karye, ko zafin yankar da madubin yamun atafin hannuna banjiba na kara karyo wani, hannunsa daya da mutumin yarike hannuna yana kokarin jana nakartawa mudubin da sauri yasakarmun hannunnawa, rike katakon madubin nayi gam nakara daga madubin dayake hannuna na yankesa goshi cikin duhu batare dana masan inda na yankaba, cikin tsananin jin azaba mutumin ya janyo maryam da dukkan karfinsa, da nufin ya tumurmusata cikin tsananin zafin rai,ganin tana bata masa lokaci. gabadaya muka taho nida madubin, mutumin ya cillani akan gadon, shikuma madubin yafadi kasa, wani abune me kyalli,naga yayi tsalle daga kan madubin yafadi a acan gefe akasa jikake toshhhhhhh!! yafashe wani bakin hayaki yafara fita daga cikinsa tare da wata muguwar kara data karade part din gabadaya me barazanar toshe kunnen mutum yakoma kurma. fashewar abun yayi daidai da tashin mustapha zaune daga kwancen dayake tamkar gawa cikin wani irin yanayi yana kiran sunan ALLAH da dukkan karfin muryarsa da Allah yayi masa…………✍️

By
zeey kumurya

ABUNDA KA SHUKA………
(shizaka girba)

MALLAKIN
????
ZAINAB USMAN KUMURYA

FARIN JINI WRITERS ASSO…..????

~Free novel~

Bismillahirrahmanirrahim

3️⃣4️⃣

………..A matukar firgice zannurain dake gefensa a kwance ya farka daga bacci, saboda karar abunnan harnan suka jiyota, ga kuma sunan Allah da mustapha yakira tamkar acikin kunnensa, ahankali yakai hannu yana shafa inda ya’ajiye wayarsa jikinsa gabadaya na kyarma saboda tsorata, dakyar yasamu ya lalubota ya kunna fitila inda mustapha yake yahaska yaganshi a zaune, bayansa jingine da fuskar gadon amma idanunsa a rufe. Se numfarfashi dayake saukewa akai_akai. abunda ya matukar bawa zannurain mamaki kenan tamkar bashi yaji yana kiran sunan Allah yanzu ba, amma cikin abunda befi sakan gomaba har yayi shiru yakoma gidan jiya,haska kasan dakin zannurain yayi yaga babu faruq babu alamarsa kuma alhalin harya kwanta faruq yana cikin dakin. Number daddy yafara dialing domin yasanarmasa abunda yake faruwa…….

A,part din mommy kuwa, dasauri na toshe kunnuwana da duka hannayena biyu saboda muguwar karar dake tashi adakina, wani mahaukaciyar juyawa naji kaina namun tamkar numfashina zebar gangar jikina, daga nan bankara sanin inda kaina yakeba. cikin zafinnama mutumin yasaki maryam yasakko daga kan gadon yafice da gudu kamar wancan lokacin, aunty tana kan sallaya taji wannan muguwar karar itama, dasauri ta mike tana karanto sunan Allah, dakuma addu’ar neman tsari daga abunki, cikin abunda befi sakan 5 ba, taji karar ta dauke dif, ajiyar zuciya ta sauke cikin dakakkiyar zuciya ta fito falo, karaf a idanunta taga mutum yabude kofar falon yafice da sauri, kasancewar falon akwai wadatuwar haske, cike da tsananin mamaki tayi yunkurin nufar kofar dantaga waye wannan, amma fitowar suhailat a firgice da gudu ya katse mata hanzari, rukunkume aunty suhailat tayi saboda tsananin tsorata da karar dataji, jikinta se rawa yakeyi tamkar mazari tama kasa magana tsabar firgici. ganin yanda take a matukar tsorace aunty ta rungumeta ajikinta tahau tofa mata addu’a akai. Hankalin mommy a matukar tashe tafito daga dakinta, kosu aunty dake tsaye bata kalli inda sukeba tanufi dakin maryam cikin sauri tamkar zata tashi zama, janye suhailat aunty tayi daga jikinta tabi bayan mommy dasauri danse yanzu talura da wani hakayi dayake fita ta wajen key din kofar dakin maryam, suhailat ma cikin sauri tabi bayansu. azafafe mommy ta tatura kofar ta shiga dakin tana kiran sunan maryam da karfi. aunty dake bimata baya tana shiga dakin wani wari gami da kauri mara dadi yaziyarci hancinta, toshe hancinta tayi dasauri cikin tsananin dauriya takarasa shiga dakin, suhailat kuwa dasauri tayi baya tarin dabata shirya masaba ya turniketa, laluban makunnin dakin mommy tayi ta kunna light haske ya gauraye dakin. cike da mamaki gami da tsoro aunty take kallon abunda yafashe din, yanda wani bakin hayaki yake tashi daga cikinsa. Mommy kuwa cike da tsananin tashin hankali take kallon abun, nandanan jikinta yadauki kyarma idanunta sukayi jajur alamar tsananin tashin hankali. Aunty bata lura da halin da mommy take cikiba, tanufi kan gado inda maryam take kwance itama tana kiran sunan ta, amma taji shiru. Batare dawani bata lokaciba aunty ta dakko maryam tafito da ita daga dakin da saurinta cikin tsananin rudewa ganin maryam babu alamar numfashi ajikinta ga wannan hayakin ze iya cutar da ita idan akabarta acikinsa, gakuma jinin dake zuba ahannunta, direct dakinta ta nufa da ita ta shimfideta akan gado,suhailat nabiye da ita abaya a tsorace…………….

Daddy cikin baccinsa shima yaji wannan karar kamar a zahiri kamar a mafarki, bejima da kwanciya ba bacci nacin sa hakan yasa betashiba, amma kiran wayarsa da’ake tayine yasashi dole yatashi ya dakko wayar yaga zannurain ne, gabansane yayanke yafadi danyasan ba lafiyaba, daga wayar yayi da sauri yakara akunnensa kafin yayi magana zannurain yarigashi dafadin “daddy pls kazo part din yaya yanzu” aiko bari daddy beyi yakarasa zancenba, ya mike da sauri yafice daga part dinnasa, danyanda yaji muryar zannurain yasan bakalauba. zannurain kuwa yanata faman jijjiga mustapha gami da kiran sunansa, ahaka daddy yakaraso yazo yasamesu. “Usman lafiya meyafaru dashi” daddy yashigo dakin yana tambayar zannurain cikin tashin hankali. “Dad, inacikin bacci naji muryarsa yana kiran sunan Allah, amma kafin nayi yunkurin tashi harya koma haka, ahaka na tashi nagansa a zaune.” Cikin tsananin farin ciki daddy yace, “usman! Dagaske mustapha dakansa yatashi zaunennan kuma harda magana” “eh daddy dagaske wlh, nima nayi matukar mamaki” wata nannauyar ajiyar zuciya daddy yasauke, tare da fadin. “Alhamdulillah” harsau uku, sannan yakai hannu ya kunna light din dakin. zama yayi a gefen gadon tare da janyo mustapha jikinsa, sakayau daddy yajishi babu wannan mugun nauyi dayayi sanda yana ciwo, gajikinshi normal babu zafinnan kokadan, hannunsa yakai yataba goshinsa yaji shima babu wannan zafin, umarta zannurain daddy yayi yadakko masa ruwa me sanyi a fridge, dasauri zannurain ya mike, ya dakko ruwan ya mika masa, zuba ruwan daddy yayi ahannunasa yahau shafawa mustapha afuskarsa zuwa wuyansa, wani dogon numfashi mustapha yaja, ahankali yafara bude idonsa yana sauke ajiyar zuciya. cikin tsananin farin ciki mara misaltuba daddy yakira sunansa, be amsa masaba se kallo daya bishi dashi. Zannurain dayakasa magana saboda tsananin murna yace, “yaya!” maida kallonsa mustapha yayi akan zannurain ya kura masa ido, cikin tsananin doki zannurain yafara neman layin mommy danya mata wannan daddadan albishir din danyasan setafi kowa murna da farfadowar mustapha, kiran ya shiga amma mommy bata dagaba, behakuraba yakuma kirannata. Daddy dake ta kallon mustapha cike da tsananin tausayawa ganin yanda yaketa sauke ajiyar zuciya ya dubi zannurain yace, “nasan mominku kake kira, idan bata dagaba ka kyaleta zuwa safiya, kakara kiranta” ajiye wayar zannurain yayi yadawo kusa dasu daddy yakama hannun dan’uwansa fuskarsa dauke da fara’a menuni da zallar farin cikin dayake ciki. ganin yanda mustapha yakurawa robar ruwan da haidar ya dakko se daddy ya fuskanci kamar yanason ruwanne, dakkowa yayi yakafa masa abakinsa, aiko tamakar jaririn daya dade besha nonon uwarsaba haka yakama kukkutar ruwan, sedayashanye tasss. sannu daddy yamasa, lumshe idonsa kawai yayi yana cigaba da sauke ajiyoyin zuciya. Kwantar dashi daddy yayi akan gadon, yanufi toilet din dake dakin yadauro alwala yafito yafara sallah dannuna godiyarsa ga ubangiji maji rokon bayinsa dayabawa mustapha lafiya a lokacin dabasuyi zatoba ko tsammaniba, zannurain kuwa yakasa barin kusa da yayansa se kallonsa yakeyi cike da farin cikin tashinnasa…………

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button