
Mommy bayan fitar aunty da maryam takai hannu da nufin daukar abunda yafashedin sekuma tayi wani tunani tafasa ta fice daga dakin dasauri cikin wani irin yanayi mewuyar fassaruwa. hankalin aunty a matukar tashe take shafawa maryam ruwa ajikinta, suhailat kuma namata firfita bisa umarnin aunty. gashi hankalin aunty ya rabu biyu, sotake taje taga menene adakin maryam dayake hayaki, tabbas kotantama batayi akwai wata kulallaliya akarkashin kasa da kuma kitimurmura dake faruwa,sannan kuma ga tunanin wanda tagani yafice daga falon. hannun maryam aunty ta wanke mata jinin tare da daure matashi da kyalle. Kusan 20 minutes sannan maryam taja dogon numfashi gami da mikewa zaune a firgice tana kokarin guduwa tare da fadin, “waye kai, meyasa kakeson cutar dani kayi hakuri dan Allah karka rabani da martabata, aunty, mommy kutaimakeni,karku bari yabatamun rayuwa!” Kalaman da maryam takeyi kenan cikin kuka. Fahimtar da aunty tayi bata cikin hayyacinta seta riketa gam ajikinta tahau shafa bayanta.tare da karanto addu’a tana tofa mata. Luf maryam tayi ajikin aunty, tana sauke ajiyar zuciya. Can kuma cikin wahalalliyar murya tace, “ruwa,ruwa” suhailat ce tatashi tadakko takawo mata, domin ita kanta jikinta yayi sanyi da yanda abubuwan suke faruwa ta kuma fahimci wanine yazo domin ya cutar da maryam din a kalamanata. Ruwan aunty tabawa maryam tasha sannan ta kwantar da ita akan gado tana cigaba da tofa mata addu’a, bajimawa bacci menauyi yayi awon gaba da ita. ganin maryam tasamu bacci aunty tadubi suhailat tace, “kikwanta kema kinga tsakiyar darene zanje naduba dakin maryam din” gyada mata kai suhailat tayi, sotake tatambayi aunty meke faruwa amma takasa magana. ficewa aunty tayi ta nufi dakin maryam zuciyarta namata sake_sake, kalaman maryam sunkara sata acikin duhu,kenan wanda tagani ya fita farmaki yakaiwa maryam. “tabbas akwai abunda ake kullawa maryam, tunda naga wani yafita da gudu daga falonnan sannan kuma ga abunda nagani adakinta, ga kuma kalaman datakeyi. amma insha Allahu koma waye sedai mugun nufinsa yakoma kansa” aunty ta fadi haka afili, sanda tashiga dakin maryam din, bin dakin tahauyi da kallo daga gani ansha artabo tsakanin koma waye da maryam, ganin yanda dakin yake duk a hargitse. Tsugunnawa tayi agaban abunnan tana karanto ayatul kursiyyu a fili sannan tasa hannu tadauki abun, dasauri aunty tasakeshi saboda zafin dataji ahannunta yana shirin konata. Kurawa abun ido tayi danganin menene aciki, abunda kawai ta fahimta wata yarkaramar layace sekuma gashi dake saman layar, har lokacin kuma hayaki nafita daga cikin abun kadan_kadan. aunty macece dabata tsoro kokadan akan irin wadannan abubuwan, tunani barkataine sukazo mata cikin kwanyarta akan abunda yafaru. Daddy seda ya idar da sallah yake tambayar zannurain ina faruq, yace masa shima tashi yayi yaga begansaba. duddubawa daddy yace yayi ko yana wani dakin, amma zannurain yaduba ko’ina a part din begansaba har kasa begansaba. Daddy beyi tunanin komaiba danyasan halin faruq, may be abunnasane ya motsa ya koma part dinsu……
Mommy tana komawa dakinta cikin tsananin tashin hankali ta daukko wayarta missed call din zannurain tagani, dama tasan za’ayi haka dantasan zuwa yanzu mustapha ya mike. wata Number ta lalulubo takira takara wayar a kunnenta, ringing biyu aka daga cikin kunar zuciya gami da tsananin bakin ciki mommy tafara magana. “Dan’ albarkana, ya’akayi haka ta faru meyasa al’amuran suka lalace yauma bakayi nasara akannata bane?” Daga daya bangaren akace, “hmmmm, mommy yarinyar tana wahalar damu gashi gabadaya ta dagula mana lissafi tadawo mana da hannun agogo baya, muna gabda cimma nasara akan abunda mukayi shekaru muna nema, amma rana daya tazo ta ruguza mana komai. waiyama akayi wannan kaskon yazo dakinta?” “bansaniba nima wlh, shine abunda yafi komai dagamun hankali dasani dimuwa” cewar mommy cikin tsananin bacin rai. “Mommy, akwai matsalafa domin boka tsidau yacemun aikinmu yana gab da lalacewa,matukar bamu dageba” wata mahaukaciyar dariya mommy takece da ita, kafin daga baya ta hade rai tace, “karyane dana, aikina baze taba lalacewaba nicefa atika, kaidai kazuba ido kaga abunda zanyi, itama yarinyar datake batamun shirina sena kasheta da hannuna,.!,domin tunda tazo gidannan komai nawa yakeyin baya” mommy takarasa zancen cikin Karaji,zuciyarta na tafarfasa. “Amma mo…. ” karkace komai dana, kaidai kawai katabbatar kabar gidannan adarennan kafin wani yaganka” mommy tana gama fadar haka ta katse kiran tare da bin bayan kiran zannurain,amma harta katse shima bedagaba, time din yaje duban faruq wayartasa kuma tana silent shiyasa daddy beji kiranba. Aunty ta jima durkushe agaban abunnan tana karanto addu’a tana tofawa acikinsa, sannan tasamu hayakin dake fita daga cikinsa yadena fita. ahankali takai hannu akaro na biyu ta dauki abun setaji babu zafinnan, dakinta ta nufa dashi dauke ahannunta……
AFTER SOME HOURS
Har safiya su aunty basusan halin da’ake cikiba game da farfadowar mustapha, kuma haryanzu maryam bata tashiba aunty ma bata tashetaba,duk da zuciyarta a kwadaice take dajin ina maryam ta samo abunnan. zannurain bega missed call din mommy ba sebayan daya dawo daga masallacin sallar asuba,yabi bayan kirannata kuma bata dagaba. A masallaci daddy haidar kawai yagani bega faruq ba, ya tambayi haidar koya baroshi a part dinsune yace masa besaniba koyana cikin dakinshi. tare da haidar suka dunguma duka zuwa part din mustapha, dan tun kafin a tada sallah zannurain ya guntsa masa yaya ya mike. Aunty takira daddy danta sanar masa abunda yake faruwa yace mata tazo part din mustapha shima akwai abunda yakeson sanar mata, takuma biya tataho da mommy dansuna ta sabanin kira da ita. Koda aunty tazo dakin mommy, seta tarar mommy tana cikin toilet hakan yasata ficewa tafadawa suhailat idan mommy tafito tasamesu a part din mustaphan. Mustapha yana kwance akan gado, idanunsa a lumshe amma ba bacci yakeba, su haidar suna zagaye dashi, sun rasa inda zasu tsoma kansu dan farinciki, ahaka aunty tashigo ta samesu bakinta dauke da sallama, amsa mata sukayi atare fuskokinsu dauke da murmushi. da mamaki aunty take kallonsu kafin tace wani abu haidar yay caraf yace, “auntynmu kibani goron albishir dan albishir din dazan miki yacancanta kibani goro me daraja, yayanmu ya warke harya mike zaune dakans……”dagaske kake haidar” aunty tafadi haka cikin tsananin farin ciki tana nufar inda mustapha yake. “Dagaske yake saudart” cewar daddy yana murmushi. “Godiya ta tabbata ga Allah, me rahama dajin kai ga bayinsa,Allah kakara sassauta mana, ka kara mana lafiya, Allah duk wanda yake cikin hali na jinya Allah shima kabashi lafiya” aunty tafadi haka tana shafa fuskar mustapha, gabadaya suka amsa mata da “ameen”, banda mustapha dako bude idonsa beyiba. “Yaya yaushe ya farfado dinne?” aunty tatambayi daddy. “Tun jiya cikin dare zannurain yakirani yasanarmun wai ya tashi a firgice,amma yanzu komai yayi daidai danhar wanka usman yataimaka masa yayi gami da sallah, amma maganacefa haryanzu beyiba” “kai, masha Allah, jiki yayi kyau, ai maganar se’ahankali zeyine da yardar Allah,ahakanma angodewa Allah, sannu kaji Muhammad Allah yakara sauki” “ameen,ameen” duban zannurain aunty tayi tace, “amma zannurain a wani irin firgici ya farka?” Numfashi zannurain yasauke yace, “aunty nidai ina bacci naji wata irin kara daganan kuma senaji muryarsa yatashi yana kiran sunan Allah” “kara kuma harnan kunjiyo wannan karar?” Aunty tatambayeshi cike da mamaki, “aunty nima ai naji” cewar haidar, daddy ma cike da mamaki yace, “aiko nima naso naji wata kara cikin baccina, karar mene” shiru aunty tayi batace komaiba, se gyada kai kawai takeyi,cikin ranta tace. “Tabbas babu tantama abunda tadakko daga dakin maryam shine abunda yafashe kuma yayi wannan karar, kuma yanada nasaba da ciwon mustapha, to amma meyakaishi dakin maryam, ko wanda tagani yafita daga dakin shine ajiye abun” bata dame bata wannan amsar se maryam, itace zata fayyacemata zare da abawa tunda adakinta abun yafaru, daddy yabude baki danufin yakara tambayar aunty akan wai meke faruwane ganin tayi shiru, amma shigowar mommy da suhailat ta hanashi maganar. Su haidar naganin mommy suka ruga gareta suna rige_rigen sanar mata yaya yatashi, dansunsa setafi kowa farin ciki da tashin mustapha, atare suka sanar mata, pretending na murnar da mommy tayi akan tashin mustapha baze misaltuba, harda kukanta na murna, suhailat ma tayi murna sosai, kokunyar su aunty batajiba taje ta rungumeshi tana shashshafashi. mommy cikin tsananin murnar datake nunawa ta karasa gabanshi, ta kama hannunsa ta rike tana fadin, “my son, tashi kaga mommynka, bude idonka naganka naji dadi araina, yau ranar farin cikin muce son, tunda Allah yabaka lafiya” a matukar firgice mustapha ya bude idonsa gami da tashi zaune yafara ja baya daga kusa da mommy,jin muryarta yana fadin, “pls mommy kiyi hakuri idan wani lefinna miki kidenamun abunda kikemun kullum pls mom,inajin azaba sosai ajikina..!” cikin raunananniyar yayi maganar yana sakin numfarfashi,alamun dakyarma ya iya yin maganar. dafe kirji mommy tayi tace, “son kasan mekake cewa kuwa, nicefa mommynka koka manta nine” girgiza kai mustapha yahauyi yana kara jabaya, rikeshi haidar yayi ganin kamar baya cikin hayyacinsa. cikin tashin hankali mommy ta juyo tana kallon daddy, idanunta na zubar da hawayen munafurci tace, “daddy kaji me son dina yake cewa, yau nice son bayason narabeshi, wai ina masa wani abu, wlh anshiga tsakanina da dana, anmasa mugun asirin daya manta kansa pls daddy kayi wani abu akai,wlh angamamun da dana” ta karasa zancen tana fashewa da kuka. wani irin kallo aunty takebin mommy dashi na tuhuma, kafin daddy yayi magana, sukaji daga bakin kofar dakin anacewa, “babu wanda yayi masa asiri danya rabaku, face ke dakikayi masa asirin dakanki akokarinki na ganin ya mutu, danki cika wani banzan burinki,saboda bake kika haifesaba. sekuma Allah bebaki nasaraba gashi ya warke a lokacin dabakiyi tsammaniba………..✍️