Uncategorized

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE HAUSA NOVEL

BY
zeey kumurya
ABUNDA KA SHUKA………
(shizaka girba)

MALLAKIN
????
ZAINAB USMAN KUMURYA

FARIN JINI WRITERS ASSO…..????

~Free novel~

Bismillahirrahmanirrahim

3️⃣5️⃣

………..Gaba daya suka juya atare cikin tsananin mamakin jin muryar me maganar gami da abunda yafada, mutumin dasuka manta rabon dasuji yayi doguwar magana irin haka. “Faruq! ni mahaifiyarka kake jifa da wadannan muggan kalaman, nikake cewa nayiwa dana nacikina asiri kuma bani na haifesaba,kana cikin hayyacinka kuwa faruq!?” mommy tafadi haka cikin tsawa da matsanancin tashin hankali. murmushi faruq yayi, gami da yin taku yakaraso har gaban mommy yace, “ina cikin hayyacina mommy nake fada miki wadannan maganganun,kidena wani borin kunya,kina nuna kamar bakisan abunda kinfi kowa sanin saba,yau ranar tonan asirinki ce tazo keda wanda kuke shirya komai tare, kisani asirin dakikamun na shekara da shekaru ya karye hakama wanda kikayiwa daddy ya karye” kafin mommy tayi magana aunty tatari numfashin faruq tana duban daddy tace, “yaya kanajin me faruq yake cewa akan mahaifiyarsa amma kayi shiru kana kallonsa, menene gaskiyar al’amarin yaya?” Shiru daddy yayi bece komaiba amma fuskarsa tana nuni da tsantsar damuwa, da tashin hankali,kusan 50 second sannan ya numfasa yace, “tabbas atika ba’ita ta haifi mustapha b…” wata hantsilowa mustapha yayi daga kan gado jikinsa gabadaya yadauki wata irin kyarma hannunsa narawa yahau nuna mommy yana kallon daddy, magana yakeson yayi amma yakasa se bakinsa dake motsi alamar yanason yace wani abu. aunty, haidar,zannurain atare suka mike tsaye cikin tsananin dimuwa jin abunda daddy yace,aunty hartana yarda wayarta kasa batare data saniba, baya mustapha yayi luuu,ze fadi kasa,dasauri daddy yataro jikinsa,suka zauna abakin gado, dama jikinnashi babu kwari gakuwa wani bakin zance dayakeji wanda yake kokarin saka zuciyarsa ta buga, wanda yajishi tamkar saukar ruwan narkakkiyar dalma atsakiyar kansa. kallon mommy aunty takeyi amma itama takasa magana se girgiza kai kawai takeyi, aranta tana cewa, “wanne irin burine wannan da mommy takeson cikawa wanda har tayiwa danta na cikinta da kuma mijinta asiri,kuma take kokarin kashe mustapha” mommy kuwa jitayi gabadaya yawun bakinta ya kafe kaf, zuciyarta tahau harbawa dasauri cikin tsananin tashin hankali bata taba tunanin abun zezo mata ahakaba, “nashiga uku ni atika,yanzu kenan sulaiman ze iya tuno komai daya faru ada” mommy ta fadi haka atunaninta azuci tayi maganar, amma seta tsinkayi muryar daddy yana fadin, “tabbas tunanina yadawo akan abunda kika gusarmun da hankali akansa, kuma ranar wanka ba’aboyen cibi yau zansanar da mustapha abunda nake da burin sanar masa shekara da shekaru,amma kika rufe mun baki ruf namanta nakasa sanar masa.” wani irin murmushi mommy tayi me ciwo cikin karfin hali tace, “to seme, sulaiman idan kafada masa, kadade baka sanar da mustapha gaskiyaba, to bari kaji insanar maka fadar abunda kake kokarin yi, daidai yake da tonawa mustapha asirin dani dakai muka rufa masa arayuwarsa” shima daddy murmushin yayi yace, “insha Allahu, fadata saidai tazamo masa alkhairi arayuwarsa” mommy tana kokarin sake magana sadiq dake falo tundazu yashigo dakin asukwane fuskarsa murtuk babu alamun fara’a yana bin kowa da kallo dai_dai, zaro ido aunty tayi cikin tsananin razani ganin rigar dataga mutumin jiya datagani yafita da ita ajikin sadiq,ga kuma kansa yane da hirami, hannunsa duka biyun da safunan hannu, alhalin ba lokacin sanyi bane. dafe kanta tayi tana furta Kalmar hazbunallau wa’inimal wakil afili. tana addu’a aranta,Allah yasa abunda take zargi karya tabbata kokuma fatan idonta beganin mata daidaiba,kai bamata tunanin haka sediq ze aikata abunda take tunani,kilan jiyanne idonta beganinmata daidaiba. “Sadiq meyadawo dakai yau kuma?” Mommy tatambayeshi cikin tsananin firgici tana kallonsa. be’iya bata amsaba se faruq daya nuna mata da hannunsa. zama aunty tayi dabas akasa tamarasa mezata kira wannan bakon al’amarin me cike da rudu da tashin hankali acikinsa. Mommy ma zama tayi a gefen gado gumi na tsatstsafoma mata ako’ina najikinta, domin bata taba tunanin abun zejuye mata hakaba, bata taba tunanin wannan ranar tonan asirin zata zomataba arayuwarta, tarasa wanne sakaci tayi dakomai nata ya lalace, amma duk da haka zuciyarta bata sadudaba, takudircewa ranta agama wannan rikicin dakanta zata koma gurin boka tsidau,yasake mata sabon aiki. Faruq ma zama yayi akasa agefen aunty, haidar da zannurain kuwa basa gane komai akan abunda yake faruwa,kwakwalensu gabadaya sun toshe tsabar tararrabi sunma kasa magana, yanzu dama ba mommynsuce ta haifi mustapha ba, “to wacece ta haifesa?” tambayar da suhailat data daskare a tsugunne itama takeyiwa kanta kenan, shiru dakin yadauka kowa da tunanin dayakeyi acikin ransa,babu wanda yadamu da yanda sukaga sadiq,dominsu basusan komaiba akan fyaden da akeyi agidanba,hatta da daddy kuwa, mommy ce kadai tasani seshi meyin da faruq.

aunty ce tanisa cikin tsananin damuwa ta katse shirun tana duban daddy tace, “yaya kafada mana abunda yake faruwa kunsamu acikin duhu kaida faruq da aunty atika,kasanarma menene kuke boyewa da kuma gaskiyar al’amari akan abunda mu bamu saniba,sannan kuma tayaya Muhammad yazama badan aunty atikaba, wacece mahaifiyarsa to?.” numfasawa daddy yayi yakalli su haidar da sadiq yace su zauna labarine me tsaho, babu musu dukansu suka yiwa kansu mazauni cikin son jin yanda daddy ze warwaremusu yanda abun yake, daddy ma raba mustapha yayi da jikinsa ya zaunar dashi akan gadon bayan yasamasa filo abayansa,cikin tsananin tausayawa ganin yanda numfashinsa yake fita dakyar tsabar tashin hankali. gyara zama daddy yayi yafara magana kamar haka:

Kamar yadda kuka sani, sunana sulaiman Abdullahi, iyayenmu mu uku kacal suka haifa, nine babba se mebimun isma’il se auta saudart. Mu cikakkun yan kanone muna zaune a unguwar gwammaja. Mahaifinmu tun muna yara Allah yayi masa rasuwa, lokacin banfi shekara 12 ba,shikuma isma’il shekara 8,yayinda saudart take karama sosai danko yayeta ba’ayiba. Mutuwar mahaifinmu bakaramin girgizamu tayiba nida innarmu,tashin hankalin da muka shiga baze faduba, haka mahaifiyarmu ta rungumemo ta cigaba da rainonmu ta kuma tashi tsaye da neman kudi domin ta rufa mana asiri. Nima tun lokacin banzaunaba nafara yan bugegene domin na dinga taimakawa mahaifiyata, dan babu metaimakonta se Allah, kunsan yanda zumuncin yanzu ya lalace, babu mekulaka sekana dashi, yan’uwan mahaifinmu ba wani kula sukeyi damuba,amma duk da haka bamu yada suba muna zuwa mugaishesu nida isma’il. haka muka cigaba da rayuwarmu cikin rufin asirin Allah, harnakai munzalin zama saurayi, lokacin nagama degree na farko,saboda halin rayuwa sena tsaya da karatun haka nacigaba da yan buge_bugena,dan mahaifiyarmu girma yakamata wasu sana’oin duk bata iyasu. Ina da shekara ashirin da hudu, itama mahaifiyarmu Allah yamata rasuwa bayan gajeriyar jinya datayi, A wannan lokacin munshiga tashin hankali fiye da mutuwar mahaifinmu, danni kusan zaucewa nayi seda aka hadamun da rokon Allah sannan nadawo nutsuwata,haka mukacigaba da rayuwa cikin maraici da kuncin rayuwa, wata cousin din innarmu itace tadauki saudart, domin innarmu bata da yan’uwa dasuke uwa daya ko uba daya. Gidanmu yazama daga ni se isma’il muke rayuwa aciki, bani da wasu abokanai hakama isma’il, mune abokan junanmu komai tare mukeyi mu nemi shawarar juna, muhaka mu binne tare. bayan rasuwar innata da watanni nafara zuwa kasuwa da taimakon wani Dan ajinmu damukai makaranta tare me suna sa’idu. wani alh, yahadani dashi nake masa jiran shago anan kasuwar wanbai,Wanda da shi sa’idunne yake masa,sekuma yanzu yasamu wani kasuwancin shine yakaini na maye gurbinsa. cikin ikon Allah tunda nakoma shagon se cinikin shagon ya ninku fiye dana baya, kullum idan aka tashi daga kasuwa sena biya gidan alhajin munyi lissafe lissafenmu sannan nake komawa gida, to a wannan zuwa gidan alhajin danakeyi anan nahadu da atika (mommy) gidansu makotane da gidan alhajin, kullum naje da yamma zanganta ita kuma tadawo daga islamiyya ita da kawayenta, amma fa kullum cikin yin fada take, wataranma harda dambe, danni kaina nasha rabasu. Kuma a lokacin ba yarinya bace, da girmanta danta zama cikakkiyar budurwa zama tayi shekara 19,sedai tana da karamin jiki. Kullum idan ta ganni setayi ta kallona, nikuma bansan meyasaba dariya take bani saboda tsiwarta,se’inta tsokanarta. Watarana bayan nazo mungama abunda zamuyi da alh, nafito zantafi gida segata da gudunta tatareni tabani wata takarda,nace mata ta mecece, tacemun idannaje gida nakaranta nagani. Banyi tunanin komaiba nakarba nazira a aljihu na wuce gida. Ninama manta da wani batun takardar data bani, seda nazo bacci zancire riga najita acikin aljihuna, dakkowa nayi ina mamakin menene, seda naganta kuma sena tuna, warwarewa nayi nakaranta, gabadaya abunda takardar ta kunsa wai atika tana sonane, dariyama ni abun yabani nazauna nayita kyakyatawa danni a lokacin ko tunanin wata soyayya banayi, tunanin yanda zansamu rufin asirin kaina na tallafi rayuwar yan’uwana kawai nakeyi. Isma’il ne yatambayeni mene yasani dariya haka, takardar hannuna nabasa ina basa labarin atika, tsaki yayi bayan yagama karantawa yakada baki yace, “yaya niko zakayi soyayyama bana fatan kayi da irin wadannan marasa kunyar, dandaga ganinta bata da tarbiyya tunda har tana mace ta iya furta maka kalmarso” bance masa komaiba,saboda bandauki zancen gabadaya da wani mahimmanciba nayi kwanciyata bacci. washegari kamar kodayaushe bayan nabaro kasuwa nazo unguwar su atika, ina fitowa kamar kullum muka kara haduwa da ita, ba kunya tatambayeni kona karanta takardar data bani, nace mata eh, seta tambayeni kona amince da soyayyarta, dariya kawai namata nawuce dan a tunanina wasa kawai takeyi itama. Intakaice muku zance,kullum se atika tatareni ta jaddadamun itafa sona takeyi dagaske, tun ina daukar abun wasa harnima naji nafara tausayinta dan wataran har kuka take sanyamun akan insota, batare danayi shawara da kowaba na amincewa soyayyar atika muka fara soyayya, dukda ni jikina yana bani bazamuyi aureba, danni talakane sukuma su atika suna da kudinsu, seda soyayyarmu tayi nisa nakejin labarin ashe atika itama marainiyace babu uwa ba uba, agurin kanin mahaifinta take, kuma anrigaya da anmata miji, yana kasar waje yana karatune shiyasa ba’ayi aurannasuba. banyi kasa a gwiwaba nasanarwada atika akan muhakura da juna tunda anrigaya anmata miji, amma atika tace sam ita batasan wannan zanceba ni takeso kuma ni zata aura. kanin mahaifinta yafatattakeni yace karna kara zuwa gurin yarsa, idanba hakaba seyasa andaureni, tundaga ranar dayamun hakan koda nazo unguwar bana sauraren atika, amma atika taki hakura dani har kasuwa take biyoni shagona, nayi mata rarrashin duniya akan muhakura da juna,amma atika takiji. Atika irin matannanne masu kafiya da taurinkai, rikicin da’aki da atika agidansu akan tahakura dani baze misaltuba,karshema kanin mahaifinta cewa yayi ta zaba koni koshi tace tazabeni, haka yatattaro mata kayanta yakoreta, tana kuka kanwarta na kuka, dayake su biyu iyayensu suka haifa, kafin su rasu, yan’uwa da abokan arziki suka dinga rokon marikin atika akan yayi hakuri tacigaba da zama agurinsa, amma yace yarantse matukar bata canza ra’ayintaba shima bazata cigaba da zaunar masa agidaba, tunda tace be’isa da itaba. itama atika ta kafe akan bakanta. cikin masu bawa kawun atika baki harda wannan alhajin danake zuwa gurinsa, toni kuma ganin atika ta guji kowa nata saboda ni, senayanke shawarar auranta a wannan lokacin, duk da nasan bawani karfi gareniba amma auranta shine kadai halarcin dazanmata akan abunda tamun. bansamu matsalaba agurin magabatanaba danaje musu da zancen zanyi aure, sudai tunda ficikarsu bazatayi ciwoba basu da damuwa, isma’il nema yanunamun kin amincewarsa danshifa atika bata masaba, dakyar nasamu na rarrasheshi ya amince. Ubangidana shine yatsayamana nida atika a aurenmu, ita yay mata kayan daki da kayan amfanin gida, nikuma yahadamun lefe. Gidanmu damuke ciki dama daki ukune kuma bawasu masu girmaba, guda biyu nagyarawa atika dayan kuma na hanyar kofar gida isma’il yacigaba da zama aciki, ubangidana shine yazama waliyyin atika aka daura mana aure atika tatare agidana, gaskiya babu karya atika tanunamun soyayya, tasoni kamarme azamanmu, dafarko bamu samu wata matsala da itaba,seda Allah yayiwa megidana rasuwa magada suka amshe shagonsu. Nashiga tashin hankali bakaramiba, domin bansan wacce Sana’a zankamaba wadda zan rufawa kaina asiriba. Isma’il shima alokacin baya sana’ar komai, hasalima karatu yakeyi ninake daukar nauyinsa, rayuwafa ta sauyamana gabadaya ga atika nadauke da dankaramin ciki a lokacin, abincin dazamucima wataran gagararmu yakeyi, ga atika bata hakuri kokadan akan rashi, kullum cikin mita da masifa takemun akan nafita nasamota abunda zataci, haka nake fita nayi yan buge_bugena daga bayama senakoma yin dako akasuwa, duk dan asamu abun kaiwa bakin salati.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button