
By
zeey kumurya
ABUNDA KA SHUKA………
(shizaka girba)
3️⃣6️⃣
………..Tsayawa nayi kawai ina kallonta cikin kura ido, domin tabbatar da abunda take fada har cikin zuciyarta gaskiyane. Kasancewar gurin da wadatar hasken kwayayan gidan mutane ina ganin yanda hawaye yake zuba daga idanunta tamkar ankunna fanfo se shatata yakeyi. Cikin tsananin tausayawa nakai hannu nakarbi yaron daketa bacci abunsa, duk wannan uban gudun da mahaifiyarsa tasha amma be farkaba. “Suwaye zasu kashe miki danki, kuma akanme?” Na tambayeta ina kallonta bayan na karbi yaron. girgizamun kai tahauyi cikin kuka tace, “babu ishashshen lokaci dazan makama bayanin kosu suwaye,amma dai su mugayene azzalumai wadanda san duniyarsu yamantar dasu Allah, sun kashemun mijina, nima basu kyaleniba Neman rayuwata sukeyi data dana,duk akan abun duniya.” wani numfashi taja tare da runtse idanunta tace, “kagudu karsu karaso,domin ni nasan duk inda nashigama agarinnan,sesun nemoni sunkasheni,kadauki wannan jakar zata taimakeka arayuwa” batajira amsataba ta bude idonta takurawa danta idanunta dasuke zubar hawaye, sumbatar goshinsa tayi gami dayin magana da yarensu cikin kuka me karya zuciyar mesaurare. Har cikin zuciyata nakejin kukan matarnan, tsabar tausayinta ita da danta nama kasa magana, se kwalla data cikamun idona. Ina shirin kara mata magana najiyo taku alamun ana tahowa inda muke, dasauri muka juya dukanmu nida matar daga inda ta bullo daganan takun yake tahowa, nikaina ba itaba bakaramin tsorata nayiba domin ga dukkan alamu wadanda take fadane suka biyo bayanta bisa ga yadda naga duk ta firgice. Rungume yaron nayi a kirjina da hannun haguna, hannun damana kuma na rarrafa nahaye kan bishiyar damuke tsaye akasanta, domin nanne kadai gurin dazan iya buya bazasu ganniba. cikin ikon Allah kuwa nahaye bishiyar tamkar dan biri ina maida numfashi, ninama manta da jakar datacemun indauka seda naga tadauketa ta ziramun acikin wani kurmin bishiyar. Sannan ta ruga da gudu ta miki wata hanya, ko minti 4 bata cika da tafiyaba wasu mutane guda hudu suka karaso gurin, hannayensu dauke da fitilu hanyar da matar tabi nan suka mika suma da gudu, naji sunyi magana cikin yarensu na buzaye amma banfahimci mesukaceba ga dukkan alamudai hango matar sukayi.
wata nannauyar ajiyar zuciya nasauke bayan sunbar gurin,wani matsanancin tausayin matarne yakamani,lallai mahaifiya, mahaifiyace tazabi danta yarayu ahannun wanda bata saniba,batasan daga inda yakeba akan akashemata shi, tazabi ita tarasa rayuwarta danta yarayu. wasu zafafan hawayene suka shiga kwaranyomun inajin dama zan iya danaje nataimaki matarnan daga hannun azzaluman mutanen data ambata. rokon Allah nashigayi akan Allah ya kubutar da ita, insha Allahu bazasu samu nasara akantaba. Nakai kusan minti talatin akan bishiyarnan ina sakawa da kwancewa sannan nadiro jikina asanyaye. Jakar data ajiyemun nadauka senaji jakar da nauyi,mamakine yakamani ganin yanda matarnan ta iya gudu da ita ga kuma goyon yaro abayanta, kodayake gudun ceton rai bazataji nauyin komaiba. Goyo yaron nayi abayana nadauki jakar naruga da gudu zuwa gida, domin nima a matukar tsorace nake, gani nake kamar mutanennan zasu iya dawowa su riskeni. yunwa da gajiyar danakeji ada gabadaya yanzu sunbar jikina,burina kawai inganni acikin gidana na tseratarwa da matarnan da danta.
Cikin ikon Allah, nakarasa gida lafiya alokacin tsakiyar darene gari yayi shiru, se haushin karnuka da kukan tsuntsaye. Nadade ina kwankwasa kofa kafin atika tazo tabudemun kofar. nasan bacci tafara, aiko ko tsayawa batayiba ta juya takoma dakinta, ni dadin hakanma naji,danbansan yanda zamu kareba idan taga yaron bayana. Dakina nashiga na kunce yaron nashimfideshi akan tabarmar dake dakin bayan na kunna light haske ya gauraye dakin. kurawa yaron ido nayi cikin tsananin tausayinsa, gashi kyakkyawa dashi fari kal harwani pink_pink yake tsabar fari. hannuna nakai nashafa kwantacciyar sumar kansa baka sidik, so da kaunar yaron nashiga cikin raina afili na furta. “Ya Allah, karaya wannan bawannaka, kabani abunda zan iya rikeshi,kakuma bani ikon rikeshi bisa amana batare dana cutar dashiba” badon nagaji da kallonsaba na mike nabude wata tsohuwar jakata danake ajiye abubuwa nasaka jakar da matarnan tabani aciki na mayar na zuge na ajiye. kamar ance injuyo naga yaronnan ya bude idonsa yana wawure_wawure da hannunsa yana kaiwa baki dasauri nanufeshi nadaukeshi, aikuwa yabude baki yacanyara kuka, jijjigashi nahauyi cikin son yayi shiru amma ina tamkar kara zugashi nayi se ihu yake da dukkan karfinsa abun tausayi. Se’alokacin nayi tunanin watakila yunwace take damunsa,nanfa hankalina idan yayi dubu yatashi domin banda abunda zanbashi acikin gidannan. Yana hannuna nafita dashi domin nabashi ruwa ko Allah zesa yayi shiru kafin safiya nanemo abunda zanbasa. Atsakar gidan nayi kicibus da atika tafito a hargitse. Gabanane yayanke yafadi danbansan yanda atika zata dauki maganar yaronnanba, tsayawa tayi cak tana kallona cike da tsananin mamaki kafin naji ta lailayo wani uban ashar gami dacewa, “sulaiman mezan gani haka, jariri ahannunaka ina kasamoshi, ina cikin baccina naji kukan yaro yacikamun kunne kamar amafarki, shine nafito inleka waje inga tsinannen yaro daya hanani bacci, kuma se’inganshi acikin gidana” bance mata komaiba harna debo ruwan akofi nazauna nakafawa yaron abaki, nandanan kuwa yakama wawurar kofin da baki abun tausayi yahau kukkutar ruwan, sedayasha kusan rabin kofin sannan nacire kofin daga bakinsa kuka yasaka alamun ruwan be’isheshiba. kara mayarmasa nayi yakarasha, atikadai tana tsaye tana kallon ikon Allah.
seda yakarashan ruwan sosai sannan na’ajiye guntun ruwan. bekarayin kukanba hakanyasa na kwantar dashi akan kafadata ina shafa bayansa, abunda yakara burgeni da yaron yanda yake tsaf sewani daddadan kamshi dake tashi ajikinsa. Kallon atika nayi nace tabiyoni dakinta muyi magana, masifa tahauyi wai maganar mezamuyi ita kawai nafada mata inda nasamo yaro, maimakon nakawo mata abinci sedai kawai taga nashigo mata gida da yaro. Juyin duniya atika tashiga daki muyi magana amma taki, dole haka namata bayani atsakar gida. Bala’i da masifar da atika tamun adarennan baze misaltuba tijira kala_kala akan sena fita da yaron daga gidan,kilama wata naje nayiwa cikin shege ta haifamun dan shine zanzo inhada karyata gata wacca batasan metakeba akawomata rainon shege gida. maganganunta sunbatan rai amma dai haka nadaure naki kulata nashige dakina nabarta atsakar gida tanata hayagaga makota najinta.
dakinma bantsiraba haka tabiyoni taitamun tijara. Halaccin da atika tamunne kawai yasa adarennan bantsige igiyar aurena akantaba,amma raina yabaci matuka danne zuciyata kawai nayi bankulataba. Ranar yanda naga dare haka naga rana,ga kukan dayaron yashigayi shima tamkar ana zarar numfashinsa nasan yunwace take damunsa. Seda asuba nasamu yayi bacci, harnaje masallaci nadawo betashiba. Alokacin banhakuraba nakara zuwa dakin atika nabata hakuri dannasan kowacce macece rana tsaka mijinta yakawo mata jariri gida da tunanin dazatayi, da kyar nashawo kan atika tahakura zamu rike yaronnan,amma seda namata uwar magiya daban baki gami da rantse_rantse akan abunda nafada mata shine gaskiyar al’amari. Aranar da duku_duku nafita Neman abunda zamuci, cikin kudurar Allah wani makocinmu yakaini wani guri nayi aikin safiya nasamo dan abunda ba’asaraba. Cikin tsananin farinciki na auno abunda zamuci da kayan hadi na kawo gida, shikuma yaron na auno masa madara gwangwani daya. Koda nakoma gida yanda nabar yaron adakina haka nashigo nasamesa yanata tsala kuka, atika ko kallon inda yake batayiba, cikin sauri nanufeshi nadaukeshi nahau jijjigashi dama ina wajene amma gabadaya hankalina yana kansa. danayiwa atika maganar tanajinsa yana kuka amma ko daukarsane aitayi. Seta kada baki tacemun ita bata haifi daba bazatayiwa wata bautaba, itakuma tanacan tana hutawa. bankulataba nadama madarar danashigowa da yaron da ita nabasa yasha, dannasan yunwace ke dawainiya dashi. bansaniba ko yunwar dake damunsace kokuma danda ruwan sanyi nadama masa yana gamasha se amai. hankalinafa yatashi danbansan mezan kuma bashiba. Ruwa nabashi yasha sannan na masa wanka nagoyeshi abayana bajimawa bacci yadaukeshi. Atikadai sedai ta kalleni tatabe baki. Intakaice muku zance, nikadai nayita wahala da yaronnan inda nasa masa suna Muhammad mustapha nayita wahala sosai dashi, dan dafarkoma har rashin lafiya yayi kamar baze rayuba, sedaga baya yasamu lafiya. banfi wata dafara rikonshiba nasamu aiki a wani guri, shinema hankalina yadan kwanta dannasamu sana’ar dazamu dinga kaiwa bakin salati. atika tsana kururu take nunawa mustapha, tun yana yaro haka zatayi ta daka masa tsawa shiko bemasan metakeba. nine wankansa, inbashi abinci, tsarkin kashi da fitsari duk nine tare muke kwana tashi. Sedai innafita atika taga yadameta da kuka sannan zata bashi abinci, tana bashi tana zaginshi wataranma hardasu dungure masa kai. Nikuma Allah yadoramun matsanancin so da kaunar mustapha, bana gajiya da daukarsa inta masa wasa, wannan abun yana kara bakanta ran atika gami da kara mata tsanar mustapha aranta.