Uncategorized

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE HAUSA NOVEL

Bankulataba saboda na fuskanci ganin dukiyarnan yana kokarin sakata maida haram halak agaremu. maganganu atika tayita fadamun akan dama bangaji arzikiba dole ince haka, tayi hakuri dani alokacin da babu yanzu kuma Allah yakawo mana hanyar arziki bazan toshetaba, dan haka dole muci dukiyarnan . nidai bankulataba namayardasu cikin jakar narufe na ajiye. tundaga wannan lokaci atika takoma nunawa mustapha kauna da kulawa da tarairaya fiye da tunanin me tunani, abunnata seya dinga bani mamaki, dama shi abun duniya yafi komai saukin canza halin mutum. Kwana biyu daganin wannan gwalagwalai mukayi sallama da mutanen garin niger muka dawo kasarmu me tarin albarka Nigeria tare da wannan dumbin kayan dukiyar. Munsauka lafiya agarinmu kano,agidanmu da muke kafin mutafi anan muka sauka, isma’il yakara gyara gidan saboda alokacin yasamu sana’a yanayi anan gando suke aikin kafintanci, anan muka tarar da saudart (aunty) tazo itama domin tarbarmu. Mustapha fa yasha dauka ranar agurin mutane, dama tun lokacin da mahaifiyar mustapha tabanishi bajimawa na musu aiken cewa atika tahaihu, shiyasa duk daukarsu mustapha dan cikinmune. Kowa se yaba kyawun da Allah yayiwa mustapha yakeyi, itadai atika sedai kawai ta kalli mutum amma badamar magana, dan tun lokacin danaga tana bobbotsarewa akan rikon mustapha nace mata duk ranar data sanar da wani mustapha badanmu bane a bakin aurenta, wannan daliline yasa taboye sirrin har kawo yau danake baku labarinnan bata taba fadawa waniba, domin babu karya atika tana tsananin sona batason rabuwarmu. anan gidan muka cigaba da zama, kullum atika tadinga damuna kenan da maganar dukiyarnan, nikuma gaskiya ina tsoron tabata danbansan ya matsayin hakan yake a musulunciba. danaga ta isheni sena nemi shawarar dan’uwana rabin jiki isma’eel nakuma fada masa yanda muka samu mustapha, isma’il yasha mamaki sosai yakuma tausayawa mustapha tare da yiwa mahaifiyarsa addu’ar Allah ya kubutar da ita yakuma kaddara saduwarta da danta. Shawara yabani akan muje gurin wani malamin addini kawai mutambayesa. Haka kuwa akayi mukashirya mukaje gurin wani babban malami namasa bayanin abunda yake faruwa,seyacemun. Zan iya juya dukiyar mustapha tunda mahaifiyarsa Lokacin data bayar cewa tayi nadauka zata taimakamun amma fa da sharadi tunda wata kila gadon mustaphanne idan yagirma zanbashi ragamar dukiyarsa gaba daya. Godiya nayiwa malam nace za’akiyaye insha Allah. Kodanadawo gida nafadawa atika abunda malam yace, seta tubure tace ita sam batayarda idan mustapha ya girmaba ace masa dukiya tasaceba, kawai nabarta amatsayin tawa. nikuma nacewa atika bata isaba maganar Allah zanbi batataba, akan hakan harfada mukayi da atika. Isma’eel ne yahadani da wani baban abokinsa dayake sana’ar saida gwalagwalai, acikin gold din ko rabi bandibaba amma danaji kudinsu seda na girgiza domin milliyoyi aka siya tun a wancan zamaninma. danaga harkar gold din ana samu sosai senace bari kawai nima nakoma harkar saida gold din. Sauran na dakko aka narkamun zuwa sarka da dankunnaye gami da zobuna,wannan shine farkon silar arzikina a duniya. cikin watanni kadan cinikifa yabude kudi se zuwa sukemun kota ina, nikaina har tsorata nayi kar’a zargeni domin gwalagwalannan kudi suke kawowa bana wasaba. nanfa yan’uwa sukamun caa da tambaya ina nasamu wannan uban jarin haka dare daya, nanna sanar musu, ubangidane dani agarin Niger shiya dorani akan dukiyarsa, dayake bawani damuwa sukayi da lamarinmuba sebasu wani tsananta binkiceba. Ganin arziki yasamu atika tatada balli akan ita bazata haihu agidan damukeba sena sake mana gida mekyau na yangayu. Naso ki,amma isma’eel yace namata babu komai ai. Anan unguwar tarauni nasai wani katon fili natamfatsa ginina me matukar kyau nazamani muka koma. Burin atika yacika tafara shiga sahun matan attajirai. Ko kwana goma bamuyi da komawaba atika tahaifi danta namiji nasa masa suna abubakar sadiq. bayan haihuwar abubakar bajimawa Allah yayiwa marikin atika rasuwa, bayan yasha doguwar jinya. kafin yarasu seda atika tanemi gafararsa bisa takurawata akan abunda tamasa a lokacin auranmu. Munji mutuwar tasa sosai,bayan sadakar bakwai atika ta dakko kanwarta jamila tadawo hannunta da zama. Arzikina kara habaka yakeyi abun har mamaki yake bani. hakan yasa nafara saro kaya daga kasashen waje ina saidawa. kafin wani lokaci arzikina yahabaka sunana yafara kewaya sassa na garin kano a jerun masu kudi, nakasarwa atika bakin aljihu tana wadaka da kudi son ranta. tasa abunda takeso taci abunda takeso. Cikin ikon Allah kuma se atika take ta haihuwa akufai_akufai, dan sadiq beyi shekara biyuba tahaifi faruq, shima befi shekara biyuba ta haifi yan biyu haidar da zannurain daganan kuma haihuwar ta tsaya mata. atika macece me matukar son yayanta bata kaunar lefinsu kokadan, amma soyayyar datake nunawa mustapha daban take, nikuma banyi tunanin komaiba dadin hakanma nakeji dannayi tunanin sauyin rayuwar da muka samune yasata sassauta masa. soyayya ce ta kullu tsakanin isma’eel da jamila kanwar atika, munji dadin hakan sosai dan gaskiya atika ba halinsu daya da jamilaba, jamila yarinyace me hakuri da hankali babu ruwanta. tana gama makaranta akayi bikinsu tare aka hada dana saudart. ansha shagali sosai,lokacin su zannurain basufi shekara ukuba a duniya. Zuwa lokacin nashahara akudi sosai nashiga sahun attajiran kasarnan sunana ya yado a birni da kauyuka. Samun kudina besani girmankai ko kyamatar talakaba. har lokacin kowa nawane kuma abun hannuna berufemun idoba base nafadaba kunsan kyautata ba yabon kaiba. Sabanin atika data dauki girmankai da izza gamida kasaita ta dorawa kanta, matan yan siyasa da manyan masu kudi sune abokan huldarta, yan’uwanta kuwa danawa ko kallo basu ishetaba. ta raina arzikinsu tafi karfin ta kulasu. Nagina masallatai da makarantu da kamfanunnuka nadora abokanaina akai da yan’uwa. na hakawa iyayena dasuka rigamu gidan gaskiya rijiyoyi da fanfuna akauyuka da gurararen da suke bukatar ruwa. har saudart tayi haihuwar fari jamila bata haihuba, nanfa tatada hankalinta harda koke_koke domin ita macece meson yaya, nida kaina nabata hakuri da banbaki nace bataga yanda atika tayibane yanzu kuma da Allah yabata haihuwar gashi hartayi yaya biyar. takara hakuri komai lokacine. cikin ikon Allah ba’afi shekara biyu da zancen haihuwarba itama Allah yabata haihuwar diya mace. Zokuga murna gurin ahalinmu domin dukkanmu bamu da diya mace, saudart ma namiji ta Haifa. Ranar suna yarinya taci sunan mahaifiyarmu Ummukulsum amma ana kiranta da suhailat suhailat tataso cikin soyayyar yan’uwa da iyaye kasancewarta ita kadaice mace, kowa sonta da riritata yakeyi amma babu kamar atika. Mustapha nema baya nuna mata wata kauna, domin shi damacan tun yana yaro miskiline nakarshe kuma bayason hayaniya ita kuma suhailat akwai kuka da tabara shiyasa sam basa shiri. Bayan arba’in dintane muka dawo wannan gidan dana tamfatsashi, part din da mustapha yake yanzu anan isma’eel yazauna shida medakinsa jamila. hakan yasa kullum suhailat tana gurinmu shan nonone kawai ke maidata gurin mahaifiyarta. Arziki nadada bunkasa yayin da burukan atika nadada yawaita, munjejje saudiya munsauke farali gami da umra akaro dayawa. Akullum cikin fadawa atika da isma’eel nake kobayan raina idan mustapha ya mallaki hankalin kansa su damkamasa dukiyarsa gabadaya a hannunsa. domin ko mutuwa nayi yayana basu da gado acikinta. Wannan magana tawa bakaramin bakanta ran atika takeba a duk sanda nafada mata haka. Haka rayuwa tayita tafiya kullum samuna kara gaba yakeyi kamar yadda nima kullum cikin sadaka da bada kyauta nake, domin banmanta halin danashigaba lokacin ina halin talauci. Mustapha primary school kawai yayi anan kasar atika ta matsa sedai afita dashi waje yakarasa karatunnasa, kin amuncewa nayi amma nacin atika yasa nabarsa yaje yayi,shima ba’ason ransaba umarnin mahaifiyarsa kawai yabi yatafi. Ranar bakin ciki arayuwata ranar dabazan taba mantawa da itaba itace ranar da isma’eel yayi hatsari ya mutu shida medakinsa ahanyarsu ta zuwa abuja, fadar irin tashin hankalin damuka shiga a lokacin rasuwar su isma’eel baze faduba. mutuwar ta shigeni sosai nayi rashin dan’uwa Rabin jiki abokin shawara gakuma tsananin tausayin suhailat da maraici yasameta tuntana yar karamarta. danma karfin rikonta ahannunmu yake dantamafi shakuwa da atika fiye da mahaifiyarta. daga gaisuwar isma’il da mustapha yazo yace baze koma karatu wajeba, alokacin saboda atika bata son bacin ransa tahakura badon tasoba yadawo gida dazama. Bayan mutuwar su isma’il atika suka tafi kasar turkey ita da yara duka mustapha ne kadai bandashi yace baze busuba, se yakoma gurin saudart da zama. anan yakarasa Senior class dinsa, saboda su atika sundade a turkey dansunyi kusan shekara 4 sannan suka dawo, nima se zamana yafi karfi a can tunda iyalina sunacan,nan kuma da masu kularmun da dukiyata. bayan sun dawo mustapha yakoma america domin cigaba da karatunsa anan yayi degree dinsa nafarko dana biyu har PHD dinsa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button