Uncategorized

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE HAUSA NOVEL

Tundaga lokacin da isma’il yarasu abubuwa suka fara tabarbarewa, nazama tamkar uwargijiya da baiwarta tsakanina da atika se’abunda tace nayi shinakeyi, kuma duk abunda zatayi nabadaidaiba ban isa na tsawatarmataba. Tarabani da yan’uwana dama ita nata bawani damunta sukayiba. yarama kowa abunda yakeso shiyakeyi babu me kwabarsu,bankuma isa natsawatar musuba. Alokacin ne kuma namanta da batun dukiyar mustapha cefa a hannuna ina juyata, senaji kawai tamkar damacan dukiyar tawace. Burin danake dashi na insanar da mustapha dukiyarsace da kuma burin komawa garin Niger domin nemomasa danginsa duk yakau daga kwakwalwata nama manta dashi gabadaya, sabanin da da kullum da tunanin hakan nake kwana nake tashi araina. kawaidai abunda nasan nayi duk wani harka ta kasuwancina ina saka mustapha akan gaba, sauran yayanama kowa yagama karatu zandorashi akan harkar kasuwancina. Wannan shine takaitaccen labarin dazan Baku, dakuma yanda muka samu mustapha.” shiru dakin yadauka bakajin motsin komai se karar fanka da sassauke numfarfashi da kowa yakeyi. Gabadaya bakunansu sun musu nauyi sunkasa sarrafa harshensu balle susamu damar koda furta harafi dayane, saboda tsabar mamaki gami da al’ajabi da jimami. Mustapha kawai kallon daddy yakeyi tunda yafara bada labarin, wani irin yanayi yakeji ajikinsa me wuyar fassaruwa,yanda yakejin zuciyarsa tamkar ana rura masa wutar garwashi acikinta, gani yakeyi tamkar daddy kirkirar labarin yayi kawai ya basu. tayaya ze iya daukar wannan bakon al’amarin ace mominshi me kaunarsa meson ganin farincikinsa akodayaushe ba’ita ta haifesaba. ahankali ya yunkura idanunsa a lumshe tsabar damuwa ko gani bayayi ya mike yana layi ya karasa gaban mommy yadurkusa yakama hannunta, cikin wahalalliyar murya menuni da me ita shikadai yasan azabar dayakeji yace, “mommynah, nike nasani amatsayin mahaifiya kuma kenaso nacigaba da kallo amatsayin uwata dan Allah kimusantamun abunda daddy yafada konaji sanyin tafarfasar da zuciyata takemun,wlh kwakwalwata bazata iya daukar wannan lamarinba” wani irin kallo mommy tamasa me wuyar fassaruwa tana murmushin mugunta tace, “mustapha kada ka bata bakinka gami da wahalar dakanka akan abunda yake na gaskiya zuwa wanda bashi bane. ninan atika dakaganni banasonka bana kaunarka mesonkama bana sonshi imfact madai duk duniyarnan babu wanda na tsana sama dakai mustapha, saboda haryau zuciyata bata yarda da zancen sulaimanba, nafi yarda da ciki yayiwa wata a waje ta haifeka” mommy tafadi haka babu alamar nadama a tatattare da ita. Gabadaya yarannata ido suka zuba mata suna kallonta yanda take magana babu alamun rahama akan fuskarta. Aunty kuwa kanta nakasa tana karanto addu’ar samun nutsuwa domin kuwa yanda taji al’amarin a baibai waiba mommy ce tahaifi mustapha ba, kuma duk irin tarin soyyayar datake nuna masa ashe duk na muguntane,lallai mommy ta iya zagon kasa,kuma ta cika cikakkiyar makira. mustapha cikin fitar hayyaci yakara damke hannun mommy idanunsa nazubar da hawaye yace, “mommy meyasa bakya sona wanne lefi namiki arayuwa, please and please mommy kisoni sona gaskiya nike kadai nasani amatsayin uwata kome zakimun kuwa bazantaba canza matsayinkiba,domin banida kamarki” dagowa aunty tayi tana kallonsa cike da tausayawa idanunta nazubar da hawaye, yanda yake kuka yana rokon mommy, abunda ta manta rabon dataga kukansa, domin shi mutum ne mejuriya akan komai. tabbas akwai tashin hankalin da idan yazowa mutum duk jarumtarsa be isa ya jure masaba. daddy ma cike da tausayawa yake kallon dannasa abun kaunarsa, duk da daddy yasamu wasu yayan amma bayajin kaunarsu kamar yadda yakejin ta mustapha,kaunar mustapha daban take acikin zuciyarsa. Faruqne ya matso yakama mustapha yarungumeshi ajikinsa. shima idanunsa nazubar da hawaye yace, “yaya mustapha dama nine kai, domin kai kayi sa’ar mahaifiya sabaninmu dabayi sa’artaba, mahaifiyarka tazabi mutuwa kaikuma karayu saboda tsananin kaunar datake maka,amma mu mommy da kanta take cutar damu duk dan akan duniya tabbas nasan idan kaji irin abubuwan da mommy tamaka na cutarwa zaka tsaneta, kuma bakaikadai ta cutarba harda wasu bayin Allah dabasujiba basu ganiba duk domin dukiyarka ta zamo mallakinta ita yayanta,inama ana canza uwa dase nazanca mommy wlh, domin bata da imani kokadan” yakarashe zancen yana fashewa da kuka meban tausayi. mommy ce ta amshe zancennasa da fadin, “bana nadama kodanasani arayuwata tunda nafarata, kuma ayanzuma banyiba kuma bana fiddaran zanci nasara akan abunda nasa gaba,domin duk abunda na kudura arayuwata sena cimma nasara akansa komeneshi kuma komun wuyarsa ko…..” “ba’aiwa Allah izgili kada kiga kinsamu nasara abaya kiyi zaton zaki kara samu nangaba, insha Allahu alkadarinki ya karye daga yanzu, kuma da sannu zaki girbi abunda kika shuka da hannunki” daddy yakatse mommy da fadin haka cikin tsananin bacin rai gamida takaicinta tare da danasanin kasancewarta matarsa. Mommy batabi takan maganar daddyba. tadubesu duka tace, “bari na baku kadan daga cikin labarin irin abubuwan dana aikata duk domin nasamu biyan bukatar raina” gabadaya ido suka zuba mata akaro nababu adadi amma banda sadiq dakansa yake a sunkuye tunsanda daddy yafara bada labari. Mikewa mommy tayi tai taku uku sannan ta fara magana kamar haka:……….✍️

BY
zeey kumurya
ABUNDA KASHUKA
(shizaka girba)

3️⃣8️⃣

Bismillahirrahmanirrahim

…………Nakasance ni macece me hassada gami da kyashi akan duk wanda naga wani yafini samun wani abu na rayuwa tun ina yar karamata,tun ina budurwa na baci da bin bokaye da malaman tsibbu”. duban daddy mommy tayi tacigaba da magana. “Sulaiman yakamata ace kayi tunani akan yanda na dage kai nakeso da aure alhalin nakasance mace me shegen son kudi kai kuma baka da kudi a lokacin kuma Wanda kawuna yakeso yabani yafika kudi,amma na nadage kai nakeso. To kasani auranka danayima ina da dalilin yinsa kuma ban aureka da niyyar zama dakai na dindinba,na aurekane amatsayin garkuwa wanda dazaran nagama cimma burina zan tilasta maka ka sakeni” dasauri daddy yadago da niyyar yiwa mommy magana amma tadaga masa hannu alamar yadakata sannan taci gaba da magana. “Na aurekane bisa umarnin wani boka danaje gurinsa akan wata bukatata yakuma tabbatarmun da bukatata bazata biyaba harse na auri miji irinka kamar yadda ya siffantamun, kuma gashi nayi nasara na aureka nacika burin dayasa na aureka tun aurenmu bajimawa, amma bazan fada muku ko wanne buri bane saboda ba huruminku bane. lokacin da burinnawa yagama cika ina kokarin cewa kasakeni wannan arzikin yazomana shiyasa nafasa rabuwa dakai. Idan baka mantaba afarkon aurenmu nayi barin ciki toba barewa yayiba nina zubar dashi da kaina domin banason haihuwa dakai, daganan kuma nafarashan magungunan hana daukar ciki, daga baya kuma Allah yanunamun ikonsa duk da inashan maganin amma sega cikin sadiq, a lokacin naso zubar dashi kawai kuma sena hakura. Tun lokacin daka kawo mustapha haka kawai naji tsanar yaron ta cikamun zuciya sannan kuma zuciyata ta kasa aminta da labarin daka bani akan yanda kasamesa. hakan yasa tun yana dan jariri nayita gasa masa azaba iri_iri wanda kai sulaiman baka saniba kana gurin aiki, Allah ne kawai yayi mustapha yanada rabon shan ruwa a duniya datuni yadade da mutuwa domin na dade ina yunkurin kasheshi. bayyanar dukiyar mustapha shine abu nafarko mafi rinjaye acikin duk wani abu nafarinciki daya sameni arayuwata,bansan yazan misalta muku farin cikin danayiba a wannan lokacin, domin dama nican burina sonake inzama matar hamshakin me kudi wanda duniya tasanshi sekuma gashi Allah yakawowa sulaiman kudin a lokacin da banyi zatoba. Sedai kuma wata matsala daya da sulaiman yacemun dazarar mustapha ya girma ze damka masa dukiyarsa gaba daya a hannunsa. Alokacin daya fadamun natada hankalina naita fadace_fadace domin dai sulaiman yacemun yajanye ra’ayinsa amma yaki. Nanfa nafara tunanin hanyar dazanbi dan ganin nahana wannan kudiri nashi cika. haka muka cigaba da rayuwa ina nunawa mustapha kauna fiye da kowa a duniyarnan kuma koda wasa bantaba fadawa wani bani nahaifi mustapha ba domin ina da muradin nakasheshi dazarar yakai wasu shekaru kuma banason agane nina kasheshidin. sulaiman yasakarmun bakin aljihu inayin yanda naso da kudi hakan yasa nabazama gurin bokaye Neman maganin dazan hallaka mustapha cikin sauki nakuma mallake sulaiman akan se abunda nace yayi shizeyi. wata kawata hannatu ita tahadani da wani boka wanda shiyakemun aiki har yanzu wato boka tsidau ta kuma tabbatarmun da aikinshi tamkar yanka wuka yake duk abunda nakeso yamun zemun amma fa yana bada aiki masu wahala gami da cazar kudi. nace mata nidai indai bukatata zata biya koma menene zanyi kuma ko nawane zan kashe ba matsala bane. can wani kursungumin kauye a garin katsina hindatu ta kaini inda anan bokan yake da zama, muna zuwa tunkafin nafada masa bukatata yasanarmun hakan yasa nakara gasgasta zancen hindatu na aikinsa nada kyau, domin alamar karfi tanaga me kiba. abu nafarko dayasanarnun zanyi shine nafara kawar da duk wani wanda yasan mustapha badanmu bane, ma’ana nakasheshi. Godiya namasa nadawo gida.Tun daga ranar nafara bin duk hanyar dazanbi danganin na kashe isma’il domin a iya sanina shikadaine yasan wannan maganar, dama kuma inajin haushin yanda sulaiman yake sakasa a komai na harkar kasuwancinsa kuma damacan bama wani shiri dashi duk da yakasance mijin kanwata. Isma’il gabadaya a kowanne sati yana abuja yana kula da kamfanin dake can na sulaiman, se weekend yake dawowa nan kano, ko tausayin suhailat banjiba a lokacin nasa aka cire burkin motar sulaiman wata ranar Monday da safe ranar ze koma abuja, Ashe ni bansaniba jamila ta tatakura masa a daren da ana gobe zasuyi tafiyar akan tanaso tabishi abujan itama shine suka shirya suka tafi tare. dama suhailat a gurina ta kwana aranar. Tafiyar sassafe zasuyi shiyasa jamila batazo mana sallamaba, kuma tasan idan tazo bazan barta su tafi tareba saboda banason tayi nisa dani, shiyasa idan tace zata bishi nake hanawa. seda suka fice daga gidan sannan tamun text a wayata nibanmaga text dinba seda aka kira sulaiman akace sunyi hatsari duk sun rasu, hankalina bakaramin tashi yayiba danaji harda yar’uwata tuggun dana hada yakama nayi kuka kuma nayi takaici amma duk da haka bansadudaba bayan rasuwar tasu komai yalafa nakoma gurin boka, yacemun aikina akan mustapha baze tafi yadda akesoba harse na hada da namiji saurayi wanda betaba aureba kuma yakasance jinin sulaimanne,amma a lokacin yabani maganin dazanyi amfani dashi domin na mallake sulaiman din, kuma maganin yamun aiki yanda nakeso. Nikuma a lokacin na fito da kissa da kisisina tare da biyayya akan sulaiman tamkar wata ta Allah, duk dan na kawar da tunaninsa akan zargina da wani abu agaba. Haka nacigaba da rainon suhailat cikin tsananin so da kaunarta domin ita nake gani ta debemun kewar yar’uwata rabin jikina. Naso mustapha ya lalace yanda sulaiman zeji ya tsaneshi shiyasa na turashi karatu kasar waje amma abun Allah seshi be lalaceba yayana nacikina su suka lalace. Nayi nasarar mantar da sulaiman komai akan mustapha saboda yanda kullum cikin zancen dukiya batasa bace ta mustapha ce. Ni kuma da raina da lafiyata bazan bari wannan dinbin dukiyar ta tserewa yayanaba inaji ina gani. Lokacin da yarana sadiq da faruq suka tasa suka zama samari senajewa da boka tsidau da maganar ga samarin ansamu,yayan sulaiman nema nacikinsa kuma bani da matsala dasu zasumun komai danakeso,tunda yayanane. boka yacemun akwai maganin daze bani inawa mustapha amfani dashi ze mutu cikin sauki, amma wannan azurfar dake tsintsiyar hannunsa wadda da ita mahaifiyarsa tabawa sulaiman acikin jakarnan tana bashi kariya ga sihiri kuma mustapha mutum ne meriko da addini gami da addu’a dan haka sedai muyi wani aikin daban. Aikin da boka ya bani shine yanason daya daga cikin yayana yayiwa yanmata guda goma shabiyar fyade sannan kuma daga baya aljanunsa zasu shanye jinin jikinsu su mutu,bayan ya shanye wanda yazuba na budurcinsu. daga zarar nayi haka to burina guda biyu ze cika aduniya na mutuwar mustapha da mutuwar sulaiman aranar da akayiwa yarinya ta goma shabiyar din fyaden koda bata mutuba. Gaskiya wannan aikin da boka yabani ya girgizani bakadanba domin bansan ina zansamu yanmataba wadanda zanyi aiki dasuba a lokacin. Alokacin inada wata me aiki dake kula da part dina wadda bazatafi shekara 40 ba, se sulaiman ya nuna yana sonta ze aureta. aiko nan nayita bala’i na kuma koreta, sulaiman yata bani hakuri domin Alokacin aikin boka nacinsa se’abunda nace yayi shiyakeyi. Da wannan abun na fake aka dinga kawomun yara yanmata aikatau sadiq na musu Fyade sena maidasu gurin iyayensu su karasa mutuwa acan. Da farko faruq nafarawa maganar bukatata domin naga duk cikin yayana yafi kowa zuciya gami da kwazontaka amma faruq yaki bani hadin kai se wasu wa’azizzika daya shiga yimun danaga yana kokarin tonamun adiri sena bada sunansa gurin boka ya rufe masa baki tundaga lokacin faruq ya koma tamkar kurma seya wuni yakwana beyi maganaba. kuma kome akayi baze iya magana akaiba sedai yabi mutum da ido kawai. Lokacin dana tunkari sadiq da maganar nayi mamaki daya amincemun da gaggawa domin banyi zaton haka daga gareshiba kasancewarsa mutumin kirki azahiri, daga lokacinma senadena zuwa gurin boka da kaina sedai natura sadiq yajemun. yanmata uku aka farayiwa fyaden wanda duk wata tsohuwace take kawomun su daga kauyensu daga baya mutanen garin suka ganeta se sukasa aka kamata har gidan yari aka akaita nikuma namata gargadi da cewa matukar tabari sunana yafito acikin abun senasa ankarar da duka danginta hakan yasa ta tsorata taki fadin sunana bansan kuma yasuka karkeba ita da mahukunta. talatu itace farkon me aikina kuma ita kadaice tasan sirrina saboda abun yafaru akan jikarta da wasu yan garin su guda biyu data kawomun. sena koma bin kauyuka daban_daban inda ba’asanniba inasa ana dakkomun yara aikatau ahaka har’akayiwa yara 14 fyaden saura daya kenan. Boka yatabbatarmun dacewa aranar da akayiwa ta cikon 15 din mustapha da sulaiman bazasu kwana arayeba. Maryam itace yarinyar danasa wata kawata lami ta nemomin tun ranar da aka kawo maryam gidannan a kallon farko dana mata naji gabana yayanke yafadi, wanda kuma bansan daliliba. hakan yasa nake yawan kallonta dan ganinakeyi kamar zangano wani abu atattare da ita. Maryam itace ta zamo silar lalacewar kowanne shirina.” Numfashi mommy taja ta kalli mustapha fuskarta cike da tsantsar mugunta tace, “bayan duk wannan abubuwan namaka asirin da bazaka taba iya wata mu’amalar aure da wata diya maceba, hakan yasa ko tunanin aure bakayi. Boka tsidaune yacemun matukar nabari kayi aure kowanne shirina ze lalace. Lokacin da suhailat tazomun dabatun kai takeso hankalina bakaramin tashi yayiba, saboda nasan sulaiman yanajin zancen zece ayi auranku, amma ganin yanda suhailat din duk tabi tadamu sena maka zancen kuma nace kasota,amma seta gama karatu zakuyi aure,duk dan hankalinta ya kwanta amma banada niyyar kuyi aureba. Nabi hanyoyi dadama domin ganin na muzantaka gami da bataka a idon jama’a amma banyi nasaraba, har yan kamfaninku nahada baki dasu duk dan abata maka suna. idan zaka tuna wata rana da P.A tazo office dinka tayi tari amatsayin asmarta tatashi hartazo zata fadi ka tallafota jikinka, alokacin manager ya daddaukeku photo a wayarsa da niyyar ya watsashi aduniya amatsayin kuna lalata amma ita P.A din ta gogeshi saboda tace tana sonka bazata iya ahada baki da ita a cutar dakaiba. Na kyaletane kawai saboda nasamu hanyar dazan kasheka cikin sauki wato wannan cutar dakayi ta watanni. wani maganin boka yabani yace inmaka turare dashi cikin dare, zanga abun mamaki. Cikin Daren ranar da sadiq yakawomun maganin nazo namaka turaren a lokacin ma idanunka biyu nace maganin tsarin jiki zanmaka. Shine da safe katashi da wannan ciwon, dalilin dayasa kenan nakafe baza’a maka maganin hausaba, amma saboda takurawar saudart seda takira malaminnan, maganin malaminnan yana aiki sosai hakan yasa namisanya makashi da wani maganin daban dayake kara ta’azzara ciwonnaka harta ruwan tofin daya baka seda nasauyashi. Kullum cikin dare zanzo inwatsa wani magani koni ko sadiq acikin wannan yarkaramar tukunyar kasar da maryam ta dauka wadda ni dakaina nasanya maka ita acikin filonka,kuma acikintane sihirin dana maka yake wanda nahada harda gashin kanka. Addu’ar da maryam take maka shiyake sanyaya tukunyar daga mugun zafin datake dashi tana zafafa maka jikinka, nikuma dazarar tsakiyar dare tayi zanzo inkara barbada magani acikinta wanda zata koma ainihin zafinta. bansan ya’akayi tukunyarnan taje hannun maryamba, tabbas maryam tazamemun ciwon idanu, ta rushemun ginin dana debi shekaru masu yawa ina ginasu acikin yan mintuna. kasani mustapha maryam ta batamun duk wani shirina akanka amma banhakuraba danni mutumce bame raguwar zuciyaba zankoma incigaba indora daga inda natsaya senaga bayanka dakai da maryam da sulaiman d…..” “karya kikeyi mushirika da yardar Allah karshenki yazo kuma zakiga sakayya tun anan gidan duniya kikiyayi ranar da zaki girbi abunda kikashuka na sharri da hannunki” cewar aunty cikin kuka data katse mommy da wannan maganar. Gabadaya dakin kuka sukeyi banda daddy daya daure yakeyin na zuci,amma idanunsa sunyi jajur saboda tsananin bacin rai da bakin ciki da damuwa gami da dumbun takaicin halin mommy. da kuma mustapha dayaji jikinsa yayi masa wani irin sanyi duk ya shika, tsanar mommy gabadaya ta gama baibaye zuciyarsa ta maye gurbin tarin kaunar dayake mata. bayason mugunta kuma bayason mugun mutum, yanxo mommy akan dukiya tayi sanadiyyar rasa rayukan mutane da yawa, ko tunanin itama wataran zataje inda sukaje din batayi, lallai wanda yayi nisa bayajin kira,yaji yatsani kansa da duniyarma gabadaya,yanayin dayakejin kansa baze misaltuba. Cikin kuka haidar yadubi mommy dake tsaye har lokacin yace, “mommy amma baki kyautamanaba mu yayanki mukika cuta kika bata mana suna, wlh nayi danasanin kasancewarki mahaifiya a gareni, kin cutar damu gashi baki bamu tarbiyyaba w…..” Kuka yaci karfinsa meban tausayi wanda yasashi kasa karasa abunda yakeson cewa. Suhailat ma kuka takeyi tamkar ana zare mata numfashi dataji mommynta mafi soyuwa agareta ita tayi sanadiyyar barin mahaifanta duniya. Daddy ne yadubi sadiq Cikin kunar zuciya yafara magana. “Amma sadiq kabani mamaki kaida nake ganin ko mutuwa nayi zaka gajeni segashi dakai aka hada baki gurin yin wannan mummunan danyan aikin, yanzu mezakacewa da ubangijinka idan ka mutu akan cutar da bayinsa da basujiba basu ganiba dakayi” cikin shashsheka sadiq yadago yana duban daddy yace, “daddy kagafarceni wlh sharrin shedanne da kuma sharrin zuciya, gami da hudubar mommy. Tabbas yau naji wata nadama ta lulllubeni gamida kunyar ubangijina akan abunda nadade ina aikatawa tsawon wasu shekaru”. maida dubansa yayi akan mommy yacigaba da magana. Kin cutar dani mommy kindorani akan zunubin da ubangiji baze taba yafemunba, mafi girman zunubi kuma agurin Allah ga kuma hakkin wadanda nazalunta,wanda ahalin yanzu basa doran duniya bare nanemi yafiyars…” kukane yaci karfinsa. faruq ne yashare hawayen dake malala akan fuskarsa yadubi daddy yace, “babu shakka zuwan maryam alkhairi ne agidannnan domin kuwa ta sanadinta duk wani shirin mommy ya lalace wanda harnima nadawo cikin hayyacina daga mugun asirin da mommy tamun. Duk abunda mommy da sadiq suke kullawa ina sani amma harshena baze iya sarrafuwaba balle harna fadawa wani. A duk lokacin da sadiq yakaiwa wata yarinya hari a gidannan ina hankalce dashi sedai bani da ikon hanashi kokuma natona masa asiri. Wannan ruwan addu’ar da maryam takeyiwa mustapha kullum idan yayi guntu shinake zuwa nasha batare da kowa yasaniba, da haka harna farajin nima nafara dawowa daidai. A Daren jiyane da zannurain yayi bacci nadauka ruwan nasha a lokacinne kuma naji dukkan nutsuwata ta dawo, kaina yamun wasai tamkar ansaukemun wani abu me mugun nauyi acikinsa. Dama tunda naji sadiq yace yayi tafiya nasan batafiya yayiba domin haka yakeyi duk sanda zeyi mummunan aikinshi seyace tafiya zeyi. barin part dinnan nayi gabadaya nakoma part din mommy na buya a inda babu me ganina, kuma inada yakinin dama da yardar Allah sadiq baze samu nasara akan maryam ba, harya shiga dakin yafito banbar part dinba, ina tsaye a inda nabuya naga yafito da gudu dafe da goshinsa nima binbayansa nayi dasauri harya buya ajikin fulawoyi sukayi waya da mommy duk ina biye dashi besaniba ya tashi da niyyar guduwa shine narikeshi kokuwa muka shiga yi dashi hardai nayi nasara akansa saboda yafara galabaita ga jinin dake zuba ajikinsa. Kamasa nayi nakaishi can bayan gida na daureshi dankarya gudu, seda azubane nadaukeshi nakaishi asibiti aka masa treatment a hannunsa da goshinsa shinema kuka ganmu munshigo tare dashi. dama nataho da niyyar nazo na fayyace muku komai sekuma natarar da yaya mustapha yatashi haryana’iya magana da kansa” Shiru dakin yayi bayan faruq yagama magana, babu abunda kakeji se tashin kukan suhailat dana sadiq,aunty kam girgiza kai kawai takeyi tana mamakin rashin imani irinna mommy sekace ba musulmaba,akan duniyar dakowa zebarta. Mustapha kuwa jikinsa yayi tubus tamkar andafa dankali ko danyatsansa daya ya kasa motsawa soyayyar mahaifiyarsa gami da muradin ganinta susuka cika masa zuciya,yanajin tamakar yabude idonsa yaganshi agabanta. kudiri yadaukarwa kansa ayau ba gobeba zefara nemanta a duk inda take acikin duniyarnan matukar tana numfashi . Zannurain datun dazu shine bece komaiba ya katse shirun nasu yana duban mommy da fadin. “Mommy dan Allah kihakura haka, duk abunda kikayi abaya be ishekiba sekinyi yunkurin karayin wani mugun abun, memakon kikoma ga Allah kinemi yafiyarsa da wadanda kika zalinta amma sema kara wani kudirin kikeyi babu alamar nadama atattare dake, bayan kuma Allah yanuna miki ishara a lokaci daya ya karya dukkan wani shiri naki da kikayi shekaru masu yawa kina kullawa.” Wata dariya Mommy takece da ita irinta marasa imani sannan tace, “yaro man kaza, ai rago shiyake ja baya a fada. Karfa kamanta akan wannan cikar burinnawa yar’uwata guda daya tal tarasa rayuwarta kuma nice sanadi, sannan kuma kawata hindatu data rakani gurin boka, naga irin mutuwar wulakancin datayi a sanadiyyar bin bokaye, duk besa nasadudaba se dan wannan abun. To kusani ba gudu baja da baya yanzu aka fara wasan,idan kaga banga bayan mustaphaba da sulaiman to katabbatar bana numfashi a doron duniya………….✍️

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button