Uncategorized

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE HAUSA NOVEL

Ba editing????????

BY
zeey kumurya
ABUNDA KASHUKA
(shizaka girba)

3️⃣9️⃣

Bismillah irrahmanirrahim

…………..Mommy tana gama fadar haka tajuya tafice daga dakin gabadaya tana kissima irin muguntar dazata kara shiryawa mustapha harma da maryam da daddy nangaba. har aunty ta mike zata bita daddy ya katseta da sauri ta hanyar fadin, “ina zaki kuma saudaurt?” batare da aunty ta juyo ta kalleshiba tace “zanje naduba jikin maryam ne, nasan zuwa yanzu tatashi” daddy yasan halin aunty sarai idan aka bata mata rai idan bataje ta mayar da martaniba batajin dadi yasan gurin mommy zata suyita cacar baki. Hakan yasa yace mata tadawo ta zauna zasuyi magana. batare da aunty tasoba tadawo ta zauna tana sassauke numfashi gami da huci cikin tsanananin takaicu. duban aunty daddy yayi da kyau sannan yace, “a matsayinki na mace wadda yakamata ace kin fini saka ido akan al’amuran cikin gida ina son kifadamun gaskiya akan duk wannan mummunan aikin da’ake aikatawa acikin gidana baki saniba.?” wani gwauron numfashi aunty ta sauke tace, “wlh yaya koda wasa bantaba jin wannan zancenba kokuma naga wani abu makamancin haka, duk da ina yawan zuwa gidannan amma ai kasan nimaba mazauniyar garinnan baceba tayaya zansani” shiru daddy yayi cikin tsananin takaici gami da kunar zuci, jin abun yake tamkar almara wai a cikin gidansa, dan cikinsa yakewa yara mata fyade. “Wa’iyazubillah” yafaurta a fili idanunsa na taruwa da kwallar bakin ciki, yarasa wacce irin mace Allah yabasa, yarasa wanne irin son duniyane da mommy. Yanzu duk daular datake ciki ita da yayanta amma be ishetaba to wanne irin kudi takeso ita kuwa tayi arayuwarta. Faruq ne yakatse daddy daga tunanin dayake ta hanyar fadin, “yanzu daddy kana kallo mommy tatafi batare dakadau wani kwakkwaran mataki akantaba ai kamata yayima kamikata ga hukuma su hukuntata akan lefin datayi” wani yawu me daci daddy ya hadiye dakyar kafin ya numfasa yace. “Babu matakin dazan dauka akan atika umar, kuma bazan mikata ga hukumaba kodan darajarku ku yayanta, amma maganar aure tsakanina da ita ta kare bazan iya kuma cigaba da zama da ita ba” “haba daddy wanne bashine iya hukuncin dayakamata kamataba kawai, kamar yadda yafaruq yafada yakamata kamikata ga hukuma su hukuntata” cewar haidar dayakatse daddy cikin tsananin takaici gami da bakin cikin abunda mahaifiyarsu ta aikata. “Hakan yakamata nayi nima Aliyu, amma kasani Allah ba azzalumun bawansabane da sannu tun anan gidan duniya zenunawa atika ishara akan abunda ta aikata, domin ” duk ABUNDA KASHUKA SHIZAKA GIRBA” shiru sukayi kowa da abunda yake sakawa acikin zuciyarsa. suhailat ce tatashi tafice daga dakin tana kuka wiwi meban tausayi, haidar ne yabi mata baya cikin tsananin tashin hankali. aunty ma batare data kalli kowaba tamike tafice domin tadubo maryam dan zuciyarta na ayyana mata tamkar mommy tanacan tana mata wani mugun abun. Zannurain da faruq ne suka bi bayanta, sadiq kam kunya tahanashi koda dagowa ne, shikansa betaba tunanin wannna ranar tonan asirin zata zo masaba arayuwarsa, dakyar ya iya mikewa shima yafice.binsa da kallo daddy yayi cikin tsananin mamakin sadiq din daya kasa barinsa har yanzu, sadiq din dayake ganinsa me hankalin dababu kamarsa kaf cikin yayansa amma shine yake aikata wannan danyen aiki. gaskiya yayi Allah wadai da auren mommy dayayi, ta cucesa ta cutar masa da yayansa tabata musu tarbiyya, yana tunanin ze sake shawarane ya mika mommy da sadiq hannun hukuma ta bakin su faruq din, domin yazama izna agaresu anan gaba. Mustapha dake zaune tamkar mutum mutumi, domin bazece ga a duniyar dayake cikiba. Saitin zuciyarsa yadafe da hannunsa saboda harbawar datakeyi gamida zafi tamkar ana watsa masa garwashi, gabadaya yadena fahimtar komai, duniya juya masa kawai takeyi. cikin tsananin dauriya idanunsa a lumshe ya sakko daga kan gadonnasa yafara takawa zuwa gurin da daddy yake a zaune. Kafafunsa tamkar ba’ajikinsaba saboda taruwar jinin da sukayi nazama guri daya, ga nauyin dasuka masa ga wani jiri dayake jibanshi abu goma da ishirin duk shi kadai. daddy dake binshi da kallo cike da tausayawa ya lumshe idonsa saboda wata kwalla data cika masa ido na tsananin tausayin mustaphan, yasan dole yafi kowa shiga tashin hankali agame da wannan al’amari domin rashin asali bakaramin tawaya bane ga rayuwar dan’adam. Ahankali ya tsugunna agaban daddy akan gwiwowinsa ya dora hannunsa akan cinyar daddy, ilahirin jikinsa rawa yakeyi saboda tashin hankali.bCikin tsananin dauriya yafara magana dakyar da muryarsa dake nuni da tsantsar damuwa yace. “Daddy bani da baki kokuma wasu kalmomi dazanyi amfani dashi gurin gode maka arayuwata, domin Kaine jigo kuma bango na rayuwartawa. tabbas kacika mutum me tsananin kirki da hali nagari da samun kamarka zeyi wuya a zamanin yanzu. Daddy alfarma daya zakamun ayanzu shine kafadamun inda mahaifiyata tabakani, nikuma ayau ba gobeba zantafi nemanta kuma da izinin Allah indai tana raye bazan dawoba harse nagamu da ita.” Yakasarashe zancen yana sassauke numfashin wahala tare da zubar hawaye masu dumi akan kuncinsa. Ahankali daddy yabude idanunshi dasuka rine zuwa ja yasaukesu akan fuskar mustapha. Hannunsa yakai yafara goge masa hawayen fuskarsa cikin tsanani so da kaunarsa kafin yafara magana kamar haka. “Insha Allahu, mustapha bama fada makaba kawai zanyiba, dakaina zankaika har garin kuma natayaka Neman mahaifiyarka da danginka, dama burinane hakan tun kafin yau. mustapha be iya cewa komaiba, saboda yanayin dayakejin kansa, mikewa yayi juwa nadibansa yanufi toilet domin yasakarwa kansa ruwa kozeji dadin jikinsa. binsa da kallo daddy yayi cike da tausayawa harya shige toilet din. cikin sanyin jiki shima ya mike ya fice daga part din….

Apart din mommy kuwa, mommy cikin sauri takarasa part dinnata direct dakinta ta nufa tafara hada abubuwan datasan zasuyi mata amfani domin tasan koda daddy befurta mataba tasan zamanta agidansa yakare daga yau, kodama bekareba yau dole ta bazama Neman mafita akan wannan kuncewar al’amarinnata dayazo mata alokacin dabatayi zatoba. cikin sauri take diban abubuwanta masu amfani tana zubawa acikin wata handbag dinta. Tana cikin hada kayan suhailat ta shigo dakin da gudu da kukanta. Sororo mommy tayi tana kallonta kafin ta tabe baki tacigaba da diban kayanta. ganin kukan suhailat din yaki karewa mommy ta dubeta a kufule tace, “daughter wai lafiya kikazo kika sani agaba da kokekoke?” cikin shan majina suhailat tace, “mommy dan Allah meyasa kikayi haka, meyasa kika cutar da yaya irin haka, me yayi miki da kika masa irin wannan tsanar?” Wani murmushi mommy tayi kafin tadubi suhailat tace, “daughter haryanzu ke yarinyace bakisan me duniya take cikiba,kuma duk bayanin dazan miki bazaki gane menake nufiba, amma komai danakeyi danku nake” mommy ta karashe zancen da daukar mayafinta ta yafawa. “wai mommy mekike shirinyi, ina kuma zaki?” suhailat tatambayi mommy cikin tsananin mamakin ganin yanda take ta sauri zata fita. “Zankoma gidanane dake lamido kafin gobe kuma nabar garin gabadaya” baki sake suhailat take kallon mommy ta bude baki zatayi magana mommy takatseta ta hanyar fadin. “Banson kikara cemun komai daughter, abunda nakeso dake kawai shine ki kwantar da hankalinki zandawo nanbada jimawaba,acan dinne senafi jin dadin yin aikin dazanyi batare da wata matsalaba.” Mommy tana gama fadar haka ta fice daga bedroom dinnata cikin sauri batare data jiraa msar suhailat ba. wani kuka suhailat tafashe dashi cikin tsananin jin takaicin halin mommy, duk abunta da mugun halinta bazata iya abunda mommy tayiba gaskiya mommy tabata mamaki bakadanba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button