
A falo mommy sukayi kicibus da aunty data shigo. Aunty danne bacin ranta tayi taki koda kallon inda mommy take tayi shigewarta dakinta inda maryam take. Mommy kuwa bin aunty tayi da kallo kafin tayi wani murmushi da ita kadai tasan ma’anarsa sannan tafice tanufi parking space, yau ko direbanta bata nemaba dakanta zatayi driving din. Har lokacin maryam tana kwance tana baccinta, sedai daga gani baccinnata bana jin dadi bane, a wahalce take yinsa. Ahankali aunty takarasa gareta tasa hannunta tana shafa fuskarta, tausayin maryam ne yakara mamaye mata zuciya yanda take fitar da numfashi kana gani kasan na wahalane.
toilet aunty ta nufa ta watso ruwa ajikinta domin taji dadi, dan yanda takejin kanta a wannan lokacin baze misaltuba, jinta take a wata duniyar databan tsabar damuwa. Tana fitowa daga toilet din taga maryam na mutsu_mutsu alamar tatashi. Da sauri aunty ta karasa gareta ta tallafota jikinta tana kiran sunan sunanta. Memakon maryam tabata amsa se kuka data saka cikin wata wahalallaiyar murya tafara fadin, “dan Allah kumaidani gida gurin gwaggo ta, gwara na zauna agurinta akan zaman gidannan da’ake son cutar da rayuwata d…… Rufe mata baki aunty tayi, ganin haryanzu bata gama dawowa cikin nutsuwartaba, daidai lokacin daddy ya murda handle din kofar dakin bakinsa dauke da sallama, yazone domin yaduba jikin maryam din, kuma yanata knocking aunty bata jiba, kalaman maryam gabadaya akunnensa tayisu, runtse idonsa yayi cikin tsananin takaicin wai yau gidansa ake neman tsarin zama acikinsa, gaskiya atika ta gama dashi. Muryar maryam da yanda tayi maganar cikin kuka yatuno masa da muryar matar dabaze taba mantawa da itaba arayuwarsa, tamkar itace ta dawo take masa magana a yanzu. cikin sanyin jiki yakarasa cikin dakin inda sautin kukan maryam ne kawai yake tashi, aunty kuma na aikin rarrashinta. “saudart jikinnatane haryanzu” aunty dabatasan da shigowarsaba ta juyo tana kallonsa idanunta cike da kwalla tace, “inajin fa yaya haryanzu bata dawo hayyacintaba,yanzu ta farka sekuma ta fara surutai” daddy bece komaiba ya mike yanufi karamin fridge din dake dakin ya dakko ruwa a roba medan sanyi, ya tsiyaya a cup sannan yatofa addu’a yamikawa aunty yace tabawa maryam din tasha. Tallafota aunty tayi takafa mata cup din a baki, aiko Tass maryam ta shanye ruwan. “Akaro miki ruwan?” Aunty ta tambayeta. Girgiza kai tayi alamar a’a tana sauke ajiyar zuciya, taimaka mata aunty tayi ta koma ta kwanta saboda jikinta sam babu kwari. “ya Jikinnaki, yanzu inane kuma yake miki ciwo?” Aunty ta jero mata wannan tambayar. kanta dake mugun sara mata ta nunawa aunty da hannunta idanunta a lumshe, se kuma hannunta inda ta yanke da madubi. “sannu Allah yakara sauki, hannunnaki kuma bari nakira doctor yazo yaduba mikishi” gyada mata kai kawai ta iyayi. tanaso tatambayeta yajikin mustapha amma maganama wahala take mata. “Maryama, sannu kinji,Allah yakara sauki” muryar daddy ta doki kunnena, bude idona nayi da sauri najuya inda najiyo sautin muryartasa. Daga masa kai nayi shima alamun da sauki. fita daddy yayi ya zauna a falo, ya rafka tagumi yanata tunane_tunane. Aunty ce ta mike ta hadowa maryam tea mekauri, taimaka mata tayi,cikin ikon Allah kuma tasha sosai. Se’alokacin naji wata nutsuwa tafara lullubeni har gumi yana tsatstsafomun ajikina. aunty ce tataimakamun takaini toilet domin nayi wanka ko zankara jin dadin jikina. Jikina Sam babu kwari haka nadaure na watsa ruwan. ga zuciyata dakemun wani irin bugu tamkar wani abu yana shirin faruwa dani. Falo aunty tadawo gurin daddy bayan maryam tashiga wanka, zama tayi agefensa tana kallonsa yanda ya rafka uban tagumi da hannu bibbiyu. danne duk wata damuwarta tayi domin ta taushi dan’uwanta danta fuskanci yana cikin tsananin damuwa. Cikin tausasa lafazi tafara masa magana. “Yaya dan Allah kayi hakuri akan abunda yafaru mudauki komai amatsayin kaddara wadda tariga fata. kuma rubutacciya haka Allah ya kadarto mana babu yanda zamuyi.” wani gwauron numfashi daddy yasauke sannan yadubi aunty Cikin raunin murya yace, “saudat zuciyata cike take da tsananin bakin cikin abunda atika tayi,yanzu ace a gidana akeyin wannan danyen aikin, amma bansaniba yanzu idan duniya taji kotasan halin da’ake ciki wanne kallo za’amun, dayawan mutanema cewa zasuyi ninakeyi dan wata bukatar kaina” “kayi hakuri dai yaya, mugodewa Allah dayasa maganar bata yaduba ita kuma aunty atika kabarta ita da Allah,shikadai yasan meze mata” “hmmm, nacanza tunani saudart zankai karar atika da sadiq ga hukuma da kaina, domin a yanke musu hukunci daidai da abunda suka aikata” da sauri aunty tadago ta dubi daddy cikin mamakinsa, shida dazu_dazu yagama cewa yabarsu da halinsu amma kuma yanzu yacanza ra’ayi. kara gyara zama aunty tayi ta fuskanceshi sosai, sannan tace. “Haba yaya yakuma zakace haka, hannunka baya taba rubewa kayanke kayar, sadiq naga nadama tsantsa a idonsa, nasan yanzu yanacan yarasa ina zesaka kansa. Kuma yanzu idan kayi kararsu katonawa mustapha asirinsa dake rufe, duniya zatasan kowaye shi. kaga mukuma bazamuso hakaba, dan Allah yaya kamar yadda kace da farko kabarsu da halinsu yanzunma kajanye batun mikasu ga hukumar.” “Saudat abunda atika tayifa bakadanbane ta cutar da bayin Allah dabasujiba basu ganiba, kina ganin idan muka barsu bamuso kanmu dayaba” “yaya babu batun sankai, ayanzu koda kayi karar anti atika tanada kudin dazata iya kwatar kanta, tunda kasan shari’ar yanzu bata Allah baceba, karar anti atika da sadiq daidai yake da muntonawa kanmu asiri” shiru daddy yayi bekara cewa komaiba. Ganin haka aunty tashiga rokonsa gami da bashi baki, dan ita bazataso ayi karar su mommy, batason kowa yasan mustapha badan daddy bane. badon daddy yasoba yahakura yakuma tabbatarwa da aunty ta shirya idan anyi sallar la’asar zasu tafi Niger domin nemo dangin mustapha, kuma da maryam daza’atafi. Aunty taso fahimtar dashi hakan bamafita bane, domin idanma sunje Niger din gurinwa zasu nufa ta ina zasu fara Neman wani dangin mustapha, kuma kodama sunsan inda zasu nufa yau yayi wuri su tafin, tunda mustaphan ba ishashshiyar lafiya gareshiba. Amma daddy yace mata hakan kawai shine mafita dan mustapha yatada hankalinsa sosai. Badon tasoba ta amince. batayi kuma tunanin komaiba da daddy yace, zasu tafine tare da maryam, danko befadaba bazatabar maryam dinba dankar mommy ta cutar da ita.
Daddy bayan sungama magana da aunty direct masallacin dake manne ajikin gidansa yanufa domin ya kaddamar da abunda ya kudurcewa ransa tun a lokacin dayayi arba da maryam, yadade da kudirin aransa amma yau yayi alkawarin kafin subar kasarnan seya idda nufinsa. Kamar yadda yazata kuwa liman na zaune a masallacin shida wasu tsirarun mutane. Gaisawa sukayi da kowa cikin mutunci da sakin fuska tamkar babu abunda yake damunsa,duk da karfin haline kawai yakeyi. Gefe suka koma shida malam liman yamasa bayanin bukatarsa, yakuma tabbatarmasa da a yanzu yakeson ayi. Sauran mutanen dake masallacin malam liman yahado kansu atake agurin aka daura auren da daddy yabukata akan sadaki naira dubu hamsin wanda daddynne yabada. Malam liman ne yayi waliccin amarya daddy kuma na ango.(To Allah yasanya albarka a auran, yabada zaman lafiya me dorewa, tunda daddy bebari naji daurin auren konasu wayeba????)….