Uncategorized

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE HAUSA NOVEL

Aunty ce, ta umarci faruq idan yayi sallah yaje yadakko maryam, yakawota asibitin tasan yanzu tamacan tanata zullumi dama ita ba cikakkiyar lafiyaba, gashi tabarta ita kadai a gida. ina zaune a falo bayan na idar da sallar magariba naji ana kokarin bude kofar falon. Ajiyar zuciya nasauke domin duk a tunanina aunty ce tadawo, amma senaga ya faruq. da sallama yashigo falon, amsa masa nayi Cikin girmamawa tare da gaisheshi. bayabo babu fallasa ya amsamun, yakara da fadin. “Ki shirya, aunty tace nazo nadaukeki nakaiki gurinta” aida sauri namike domin zaman kadaicin ya isheni, dama yanzu nake tunanin zuwa part din su baaba talatu idan su aunty basu dawoba. dadduma kawai nakai daki nakulle dakin sannan nafito muka tafi, bayan na kulle kofar falon gabadaya. Bamuyi wata tafiya menisaba naga munkaraso wani guri, nibanma gane ina bane seda muka fara tafiya na fahimci asibitine. gabanane yayanke yafadi dannasan baze wuce yaya mustaphane, bashida lafiyaba. yana tafe ina binshi abaya, zuciyata na luguden bugu har muka karasa bakin kofar dakin, inda bugun zuciyata yakaro fiye dana da. jikina asanyaye nashiga dakin da sallama, cike da fargabar halin dazan riskeshi aciki na rashin lafiya. Ina dago kaina karaf muka hada ido dashi bayan nashiga dakin, dan gadon dayake kai yana fuskantar kofar ne. wata mummunar faduwar gabace ta ziyarceni bugun zuciyata ya karo, tamkar wadda akayiwa dole nakasa dauke idona daga cikin nasa, duk da tsananin kwarjinin dayamun, dauriya kawai nakeyi. yanda maryam taji faduwar gaba dasuka hada ido da mustapha haka shima yaji, haka kawai kuma yaji yakasa dauke idonsa daga kanta. kallon maryam Aunty tayi, ta kalli mustapha, da sauri tajuyo takara kallon maryam Cikin tsananin mamakin abunda tagani, kara maida kallonta tayi akan mustapha, abunda tagani dai shita kara gani babu canji, bakamar yadda tazataba ko idontane kemata gizo…………✍️

_sorry, zakuga typing error, inajin baccine????

BY
zeey kumurya
4️⃣2️⃣

Bismillahirrahmanirrahim

………Sosai abunda aunty tagani ya matukar bata mamaki ba kadanba, kuma wani Ikon Allah bata taba luraba seyau kodan yau tataba ganinsu suna kallonne alokaci guda? kasa nayi da nawa idon saboda juriyar tawa ta kare, ahakanma nikadai nasan yanda nakejin zuciya na kallon kwayar idonsa danayi akaron farko arayuwata, jikina gabadaya jinsa nake a matukar sanyaye. “Maryam kikaraso mana” muryar aunty ta katsemun tunanin danake. Ajiyar zuciya nasauke cikin dauriya nakarasa ciki, daddy nafara gaisawar wanda yaketa murmushi a boye wanda shikadai yasan ma’anarsa. cikin fara’a da kulawa ya amsamun ya tambayeni Jikina nace masa da Sauki. jikin aunty na matsa nace, “aunty nah, ina wuni?” “Lafiya kalau, diyata ya Jikinnaki?” Aunty ta amsamun da murmushi dauke akan fuskarta. “Naji sauki aunty, dan yanzuma babu abunda nakeji na ciwo ajikina” “Masha Allah, haka mukeson ji, Allah yakaro sauki” “Ameen, yajikin yaya” “Alhamdulillah” aunty ta fada tana maida dubanta garesa. ya lumshe idonsa kawai yanajinsu. shiru dakin yy kowa da abunda yake tunani acikin zuciyarsa,inaso namasa ya jiki, amma kuma nakasa kwarjininsa dayakemun duk ya cikani. nayi tunanin ina zuwa zanga mommy da suhalat amma kuma sebangansuba, kamar na tambayi aunty sekuma na kyale tunda ba hurumina bane. Daddy ne yakatse shirunnamu da fadin, “saudart, bari naleka candin nakara dubasu.” aunty tagane asibitin da mara lafiyarsa take yake nufi. “Tom, yaya kagaishesu kafin muzo” “zasuji insha Allah, yanzuma ai dasu Aliyu zamu koma, kekuma ko gobe da safene sekuje” “toh, sekun dawo” Maryam da mustapha dai basu gane inda maganarsu daddy da aunty ta dosaba, dan mustapha besan daddy sunyi accident ba, aunty tace kar afada masa seya kara samun sauki. faruq dake zauna yana danna waya yabi bayan daddy suka fita tare, kujerar da daddy ya tashi nan Maryam ta koma ta zauna. tunanin yaya Sadiq ne yafadomun arai, bansan nadamu dashi hakaba seyau dabanji duriyarsaba gaba daya, duk senaji kewarsa ta cikamun zuciya. tunanika kala_kala nahauyi akansa, nasan duk inda yake ba kalau yakeba, tunda har wuni guda benemeniba, amma bansaniba ko wani aikinne yadauke masa hankali. kasa daurewa nayi nadubi aunty nace, ”Aunty yau kuwa kunyi waya da yaya Sadiq?” cikin son basar da zancen aunty tace, “ehh, yacema yana gaisheki” ajiyar zuciya nasauke cikin jindadi tunda sunyi waya da aunty nasan yana lafiya kenan. “Ina amsawa” nafadi haka ina maida kallona kan tv dake dakin. har gurin mota faruq yaraka daddy inda su haidar suke jiransa sannan yakoma ciki. Wannan ciwon na mustapha babu wanda yasani dan aunty tace kar’asanar da kowa saboda kar sirrin boye yafito fili…….

Bayan tafiyar daddy bajimawa matar ta farfado, Alhamdulillah ta farko cikin hayyacinta sedai babu bakin magana se ido datakebin kowa dashi. “Sannu Aisha” cewar kawarta tana kara matsawa jikin gadon. ido kawai ta bita dashi dankokanta bazata iya motsawa, saboda wani dimmm dataji yamata. yamata wani irin nauyi kamar andora mata dutse. Duban daya daga cikin yayannata matar tayi tace. “Rasheedah, jeki kirawo doctor kice masa ta farka” “toh, umma” wadda aka kira da rasheedah ta amsa tare da fita daga dakin. cike da jimantawa kawartata take kallonta, kana taka Allah na tashi, lafiya lafiya fa sukayi waya tace mata sunshigo Kano, amma ba’afi minti talatinba segashi ta riski wannan mummunan labari. yanda Aisha taci burin zuwa Kano da bikinnan amma gashi zuwan bezo mata da dadiba,Allah karabamu da mummunar kaddara, Allah ma yatakaita batayi wani rauni meyawa…dawowar doctor da rasheedah yakatse mata tunaninta. gaisawa sukayi da doctor yamusu yame jiki, sannan yaduba matar. Tambayar matar yayi inane yake mata ciwo bayan yatambayeta jikinnata. Kanta ta nuna masa da hannunta sekuma kafadarta ta barin dama. mammatsa mata kafadar yayi, ita kuwa se runtse ido takeyi, sannu yake mata, dama yasan dole zataji ciwo agurin tunda tanan ta fadi, danma Allah yatakaita amma dazata iya samun karaya akafadar. gefen fuskartama duk ta kukkurje. Seda yamata duk abinda yadace sannan yafita. kawartatama sallama tamata tatafi akan zata dawo Anjima, danse kiranta akeyi a waya. babbar yarta rasheedah ta bari, sekuma direban matar. harsu daddy suka karaso yan’uwan matar basuzoba, dama se cikin dare daddy yayi tsammanin zuwansu dan hanyar bata da kyau. sun mata sannu, kuma sundan jima sebayan isha’i suka bar asibitin……..

Wajen 8:30 su aliya sukazo asibitin, zuwansu kenan ko gida basu jeba. naji dadin ganin aliya sosai itama haka. basu wani jimaba, aunty tatasamu agaba muka koma gida, harda ita. daddy da faruq aka bari agurin mustapha, Maryam jitayi tamkar karsu tafi don bata gaji da kallon heartbeat dintaba. hankalin ahalin alhaji mainasara yafara dawowa jikinsu, tunda Jikin mustapha Alhamdulillah, yayi kyau, dasu Maryam ma suka tafi sunbarshi yana ta baccine…….

BAYAN SATI DAYA

jikin mustapha yayi kyau sosai yanda akeso, jininnasa yadaidaita. Yacire komai na damuwa daga cikin ransa, dan kullum daddy da aunty cikin yimasa nasiha sukeyi. Maryam ma taji sauki sosai, yankewar datayi ahannu ya warke dama bawani yanka sosai mudubin yamataba. Zuwa wannan lokacin Maryam tagane, gidan babu lafiya, tunda gashi sati guda cur batasaka yaya Sadiq da mommy da suhalat a idontaba. kuma batakara tambayar aunty komai game dasuba, tunda ta lura bataso tasani. Ammafa abun yana matukar daure mata kai, ace kamar mustapha babu lafiya, amma mommy tatafi tabarshi, tunda ita haryau batasan meyake faruwaba. Aunty tanaso ta tambayi Maryam taji tayaya wannan tukunyar sirihin da mommy tayiwa mustapha asiri tazo dakinta amma basu samu sun kebeba, saboda zirga_zirgar asibiti, gana mustapha gana matar da daddy yabuge. Mommy tasamu information din su daddy suna gari, harma da accident da ciwon mustapha, duk taji labari. sungama shirinsu da kawarta binta zata rakata gurin wani hamshakin boka a garin Niger acan wani kauye. Nanda kwana 3 masu zuwa zasuyi tafiyar, danma binta ta tsaya yin wani uzurinta datuni suntafi. Suhalat kam,gabadaya kwanakinnan tayisune cikin tsananin damuwa na rashin kasancewa da mustapha dakuma rashin sanin matsayinta agurinsa,taso zuwa gida amma mommy tahanata. Abangaren Sadiq kuwa gabadaya ya boye kansa daga idon mutane, kodayaushe yana dakinsa a kulle, yarame yayi baki, ga kewar Maryam data addabeshi, mommy kullum seta kirashi a waya, amma baya picking. kullum cikin zullumi da tsammanin kamuwa da ciwo yake kamar yadda boka yafada. ko abinci baya iyaci, seyaji tamkar ze mutu yake iya jefa wani abu acikinsa. daddy kam yana sane, amma yayi banza da lamarinsa. Aunty cema takewa daddy zancensa akan yakamata su jawoshi ajiki tunda yayi nadama, amma daddy yayi biris yace tabarshi nadamama aitana gaba bega komaiba har yanzu,tunda shi yasiya da kudinsa……

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button