
Yau zamuje dubo matar da daddy yabuge nida aliya da aunty, dan tun washegarin ranar bamu kara komawaba, ranar damukajema bacci takeyi. misalin karfe hudu na yamma muka fito cikin shirunmu, bansan daliliba bankuma san meyasaba gabana yaketa faduwa tunda akayi zancen zuwanmu dubiyar, yanzumma da muka fito hakance ta kasance. muna cikin tafiya aliya tadubi aunty tace, “aunty pls kibani key nayi driving dinnan” harararta aunty tayi tace. “Aizaki iya zuwa ki kwata, uwar rawar kai kawai” duk da yanayin danakejin kaina seda na murmusa, aliya kuwa tsit tayi bata kara maganaba,se baki data turo gaba. Aunty da aliya suna matukar burgeni, suna kuma bani nishadi, har inji dama nice da mahaifiyata. “Allah kajikan mahaifiyata da innata, dama dukkan musulmi baki daya. Ameen” nafadi haka araina Aunty ce tayi driving dinmu har asibitin………✍️
By
Zeey kumurya
4️⃣3️⃣
Bismillahirrahmanirrahim
……….Da bismillah na fito daga motar saboda gani nake tamkar wani abu ne zesameni saboda yanda nakejin zuciyata. Aunty nagaba aliya nabinta abaya seni kuma ta karshe har muka karasa dakin da matar take. matar tana zaune akan gadonta, mahaifiyarta da kanwarta sune ke kwana tare da ita, suna zaune suma akan wani gado dake dakin, se megidanta shima dayazo yana zaune akan wata kujera dake fuskantar matar. da sallama aunty ta yaye labulen dakin ta shiga. a tare suka amsa mata gaba-dayansu harda marar lafiya. dasauri kanwar matar ta mike tanawa aunty sannu da zuwa tare da nuna mata gurin zama. Kafin aunty tagai ga zama muma munshigo dakin, bakunanmu dauke da sallama. kaina na kasa na shiga dakin, gefen aunty muka karasa muka zauna. Duban mahaifiyar matar wadda ta manyata sosai aunty tayi tace, “ina wuni baaba” “lafiya kalau, yarnan ya hidima damu?” Murmushi aunty tayi tace, “haba baaba aiba wata hidima, Yamejikin?” “Jiki da sauki, Alhamdulillah” “Masha Allah, Allah yakara sauki” kanwar matar ce tagaida aunty, muma muka gaishesu duka mukayiwa mejiki sannu. har lokacin kaina na kasa. Muryar dattijuwar naji tana fadin, “ai likitanma yace insha Allahu, gobe ko jibi za’a iya sallamarta, tunda jikinnata ya warware. Tun shekaran jiyama take cewa a sallameta ita ta koma gida, likitanne yace ta dad’a hakuri zuwa gobe.” “Allah Sarki, ai zamanne guri daya babu dadi, duk se mutum yaji yatakura” cewar aunty. “Hakane kuma da wannan dan wannan, to ita kaddarace bawa be’isa ya kauce mataba, yanda Aisha taci burin zuwa bikinnan tanata murna zatazo Kano taga ya Kano take, ashe rabon wahala ne ke kiranta” “To Allah ya takaita yakiye gaba, Allah yasa kaffarane” wayar kanwar matar ce tayi kara alamun shigowar kira. kafin wani a dakin yakara magana. dakkowa tayi taduba tace, “Mama kinga, aunty Maryam ce take kira, kuma naga da number dinta ta naija ce, ko sun saukane?” “watakil Asiya daga kiji dai” wayar harta katse se Asiyan ce tabi bayan kiran. dadokinta ta amsa sallama kafin tace, “Aunty Maryam, saukar yaushe?” daga daya bangaren matar tace, “saukar yanzunnan Asiya, ko gida bamu karasaba muna hanya nadora sim dina nace bari nasanar muku ya jikin A’ishan?” “Dasauki bari na bata wayar” ta karashe zancen tana mikawa mara lafiyar wayar. basu wani jima suna wayarba ta mikawa mahaifiyartasu, ita sundan jima suna magana sannan ta mikawa mijin matar shima sukayi magana. daga gani wadda sukeyin wayar da ita suna ji da ita, yanda kowannensu yake farinciki da hakan, su Aunty sungane hakane ta fuskokinsu data bayyana tsantsar farincikin da suke ciki. mundan jima sannan muka musu sallama muka tafi. Kafin mutafi seda Aunty taje office din doctor suka kara tattaunawa akan ciwon matar sannan muka nufo gida. hamdala nayi ga Ubangiji da muka dawo gida lafiya babu abunda yafaro, dan yanda zuciyata taitamun rawa nayi tunanin wani abunne ze faru dani. Adaren yau aka sallamo yaya Mustapha daga asibiti, itama matar da daddy yaje da daddare likita yatabbatar masa gobe insha Allahu zasu sallameta…
Tunanin yaya Sadiq ya yawaita acikin zuciyata a daren yau, jikina duk ya sanyaya komai cikin rashin kuzari nayisa, har Aunty take tambayata koda matsalane nace mata babu komai. Bayan mungama komai munzo kwanciya nakasa daurewa nadubi aliya nace. “Aliya niko dan Allah Intambayeki mana” inajinki matar yayana?” harararta nayi nace, “banson iskanci se’inma fasa tambayartaki” “yihakuri tawan ta abubakari kwandon sukari” ta fadi haka tana dariya. numfashi nasauke nace, “kamar kuwa kinsan akanshi zantambayeki, aliya yau kimanin fiye da sati guda kenan bansashi a idonaba, nasan dai yacemun zeyi tafiya amma baze jimaba zedawo, gashi wayata batanan bare nakirashi naji ko lafiya, nikuma ina kunyar na tambayi aunty” “hmm,wlh bake kadaiba nima nayi mamaki dabanga yaya Sadiq ba har tsawon sati guda,shida su mommyba. Dana tambayi aunty nace mata suna ina, setacemun bata sani ba. amma nifa nafi kyautata zaton bakalauba,akwai abunda ke faruwa agidannan” shiru nayi, domin nima nadade ina tunanin da akwai wani abu dake faruwa a gidan, banda haka ace duk ciwon da Mustapha yayi babu mommy ba yaya Sadiq ba suhalat, kuma ko zancensu banji Aunty tanayiba ko waya banga sunayiba gas… “Kinyi shiru Maryam” aliya ta katsemun tunanin danakeyi. Ajiyar zuciya nasauke nadago nadubeta nace, “narasa abun cewane Aliya, amma inason sanin halin dayake ciki, zuciyata cike take da kewarsa, dan Allah kitambayarmun Aunty halin dayake ciki” “shikenan kawata karki damu, kikwanta kiyi baccinki, zan tambayarmiki ita insha Allahu, dasafe” kwanciya nayi ina fadin, “nagode” atakaice, dan yanda nakejina doguwar maganama bazan iya taba. inajin Aliya na tsokanata wai soyayya dadi, nidai namata banza, harta gaji ta kwanta itama.
Abangaren Sadik ma, yau tunanin Maryam ya yawaita aransa fiye da kullum, kewarta ta masa katutu a zuciya, jiyakeyi tamkar zerasata ne. Idanuwansa ita kadai suke da muradin gani. kaunar Maryam na azabtar da dukkan jiki da zuciyarsa. betaba tunanin abun zejuye masa hakaba, daga soyayyar wasa da yaudara ta juye zuwa ta gaske, soyayyar Maryam tamasa bazata tamasa mugun kamun dake barazanar tarwatsa kwakwalwarsa. yazama dole gobe yafita danya ganta koyaji sauƙin abunda yake ji acikin zuciyarsa……..
washegari Mustapha yatashi garau tamkar bashine yayi wannan doguwar jinyarba,dama haka Allah ke ikonsa. babu wani guri ajikinsa dayake masa ciwo. Yariga ya fawwalawa Allah al’amarinsa kuma ya amshi kaddarar datazo masa cikin rayuwarsa da hannu bibbiyu, addu’a kawai yake yi Allah yabashi juriya akan abinda ya jarrabesa dashi. babban abunda yafi komai dugunzuma hankalinsa idan yatuna shifa yanzu besan asalinsaba, besan wani jininsa. wannan abu idanyatunashi seyaji yatsani duniyarma gabadayanta. gashi yau tunda yatashi yakejin wani iri ajikinsa, haka dai yadaure yayi wanka yashirya cikin wani yadi mekyau da tsada milk colour. part din daddy yanufa jikinsa a matukar sanyaye tamkar anmasa duka. daddy nashirin fita shikuma yana shigowa, a falo sukayi kicibus. cike da tsananin farinciki daddy yake dubanshi wanda har yakasa boyuwa a fuskarsa, saboda ganin Mustapha fess dashi yana takawa da kafafunshi. fuskarsa ce, kawai tayi fayau da ita sekuma haske daya kara. “Good morning Dad” mustapha yafadi haka, cikin danne damuwar dake nukurkusar ransa. “Morning too, son. Dafatan katashi lafiya” “lafiya kalau daddy” yabashi amsa bayan ya zauna a daya daga cikin hadaddun Royal chair din dake falan. “Masha Allah, son daga gani babu tambayata jiki yayi kyau, dama yanzu nake shirin zuwa part dinnaka nadubaka, kafin na wuce asibiti, doctor yakirani tundazu zebasu sallama.” “Alright, sekadawo” daddy kamar yace masa su tafi tare, sekuma dai kawai yafasa yasa kansa ya tafi. Lumshe idanunsa yayi bayan daddy yafice, mommy ce tafado masa a rai. haryau yakasa mantawa da ita, acikin ransa. Mamakintama yaki barinshi ace duk tarin kaunar data nuna masa duk ba gaskiyabane, ita kuwa mommy wacce irin mutum ce…… ahaka Aunty da daddy yaturota takawo masa abinci tazo ta samesa yanata tunane_tunane. nasiha taita masa cikin hikima kamar kodayaushe, dakanta ta bashi abincin abaki, duk dan yadena damuwa. danta hango damuwa karara acikin idanunsa. shima boye duk wata damuwarsa yayi yazage yayi break fast din, sosai yaci abincin duk dan Aunty taji dadi. Aikuwa Aunty taji dadin sosai, tata jero masa addu’oi…..