
Daddy yaje asibiti yatarar harsun gama shirinsu, ciwon matar begama warkewaba bandejin kawai aka cire mata,dandai ta matsane kawai aka sallamesu. kanwartata tun sassafe suka wuce ita da driver da mamanta. megidantane kawai yazauna su tafi tare. Da niyyarsu daga asibiti su wuce Jos,amma daddy yace dole sesun biya ta gidansa. wajen 12 na rana suka karaso gidan alhaji menasara. Part din mommy daddy yakaisu, sun samu tarba sosai a gurin su Aunty. Daddy ne yacewa Aunty su shirya tare zasu tafi Jos din, suraka matar. Aikuwa Maryam da aliya se murna za’a tafi dasu. dan Aunty tace bazata tafi tabarsuba kafarta ƙafarsu. Mustapha yana kwance a falon daddy, daddy yakirasa a waya yace yazo part din mommy yagaisa dasu matar kafin su wuce, tunda basu taba haduwaba. Amsa masa yayi cikin ladabi sannan ya mike yafito yanufi part din mommy………✍️
kuyi manage da wannan pls
By
Zeey kumurya
4️⃣4️⃣
Bismillahirrahmanirrahim
………..Cikin takunsa me cike da nutsuwa da kasaita gami da daukar hankali ya shigo falon mommy bakinsa dauke da sallama, daddadan kamshinsa mesanya nutsuwa ya mamaye falon gaba-daya. wata ajiyar zuciya daban shiryamataba nasauke, tare da maida kallona bakin kofa dasauri ina satar kallonsa. gaba-daya mutanen dake falon suka amsa masa sallamartasa a lokaci guda. akan carpet ya zauna ya fuskanci matar da megidanta ya gaishesu. matar datunda Mustapha yashigo ta kura masa ido tana kallonsa. numfashi ta sauke ta amsa masa gaisuwar batare data dauke idonta daga kallonsaba. shikuwa Mustapha kansa yana kasa bemasan tanayiba. Daddy yace, “wannan shine babban dana, sunanshi Mustapha, shine kuma mara lafiyar danace muku” mijin matarne ya amshe zancen da fadin “Allah Sarki, sannu kaji dan samari ya jikinnaka” “dasauki” ya amsa atakaice, saboda yanayin dayakejinsa yafara yawaita. “Allah yakara sauki” matar tafada still dai idanta nakan Mustapha bata dena kallonsaba saboda ita kadai tasan metagani a tattare da Mustapha’n. Aliyace ta gaisheshi cikin girmamawa, nima cikin dauriyar abunda nakeji agame dashi nagaisheshi. Daddy ne yadubemu yace, “Maryama kuje kukarasa shiryawa yanzu zamu wucefa munayin sallah,kuma a yau zamu dawo insha Allah” “to daddy” muka amsamasa cikin ladabi, tare da mikewa muka nufi dakin Aunty. duban daddy matar tayi tace, “Alhaji hardasu a yan rakiyar ne?” murmushi daddy yayi yace. “Ehhh, mamansu tace bazata tafi ta barsu sukadaiba” mijin matarne ya amshe zancen dacewa. “Amma Alhaji dasunyi zamansu har ita Hajiyan, aganina wannan ai wahalar daku zamuyi, bayan dawainiyar dakukasha damu yanzukuma harda rakiya.” dubansa daddy yayi cikin tsanaki yace, “haba, wannan ba wahalar dakai bane, muda mukeso akulla zumunta, wadda zata dore har’aba. Aiko bakomai maje muga muhallinku” “Amma dai da wannan dannaka zamu tafi ko?” matar ta fadi haka tana kallon Mustapha. shima daddy kallonsa yayi yace, “A’a bandashi” “to nidai gaskiya inason yarakamu sa…..” “Saboda kinga kyakkyawan saurayi ko?” mijinnata ya katse ta dafadar haka. murmusawa tayi tace. “Ehhh, najidin” “uhmm, kodai kinaso kihadashi da mummunar yarki umaimah ne?” dariya suka saka har daddy, amma banda Mustapha dabemasan mesukeba, yatafi can wata duniyar daban. “Nidai kawai inaso yakaramu babu ruwanka dameyasa” matar ta fadi haka tana dariya. daddy batare da tunanin komaiba yace, “to shikenan tunda kince haka, semu tafi dashi din, da dakaninsa zamu tafi, amma tunda kince haka semu tafi dashidin ba wani abu” “yawwa Alhaji godiya nake”…..
Bayan anyi sallar azahar kamar yadda daddy yafada muka fito gabadayanmu domin tafiya. Ni, Aunty, Aliya, daddy sekuma matar da mijinta. bamusan da yaya Mustapha za’a tafiba seda mugaka yafito cikin shirinsa, yacanza kaya banadazu bane. yanzu wata dakakkiyar shaddace ajikinsa kalar light blue, yayi matukar kyau,amma fuskarnan tasa a tsuke take daga gani ba’ason ransa za’ayi wannan tafiyar dashi ba. Matar da daddy yabuge ita bada wata manufa tace atafi da Mustapha ba, sedan wata yar yayanta dasuke gida ɗaya ta ganshi. yarinyar sunanta umaimah, budurwace amma zatayi shekara 27. Ita umaimah ta kasance tana bala’in son kyakkyawan namiji gentle duk wanda yazo yace yana sonta setace ita bemataba, haryanzu bataga kamar namijin datakeso ta auraba, kullum cikin siffanta yanda takeso mijinta yakasance take. A lokacin da matarnan tayi arba da Mustapha, setaga babu abunda yayi saura daga yanda umaimah take siffanta yanda takeso mijinta yakasance a tattare da Mustapha. shine abun yamatukar bawa matar mamaki, dansu gani sukeyi kamar baza’a iya samuba gashi kuma kamar yadda take so dan hamshakin mekudi, harta matsu sukoma gida taga yanda umaimah zatayi idan taga Mustapha’n.
Mota muka shiga nida Aunty da Aliya da matar, yaya faruq ne zeyi driving dinmu. suma su daddy wata sukahau sukuma driver ne zeyi driving dinsu, nayi zaton a mota zamu Jos din, amma senaga muntsaya a wani guri,gurin katon filine. Fitowa daddy yace muyi. babu bata lokaci muka fita dukanmu mukabi bayan daddy zuwa cikin gurin. ashe airport ne mukazo, seda muka dan jira daddy yayi magana da wasu mutane sannan muka kara yin gaba. wajen wani abu muka tsaya, mekamar jirgin sojoji (JET) (kasancewar garin Jos basuda filin saukar jirage, shi yasa daddy yayanke shawarar su tafi a jet din) Gani nayi kowa a cikinmu yana shiga cikin shi babu fargabar komai, nikam senaji wani iri tunda bantaba hawaba, banma taba tunanin zanganni a airport ba balle harta kaini ga shiga jirgi. senaji kamar mafarki nake, wai yau nice zanhau jirgi har yayi shawagi dani a sama. danne duk wani kauyancina da fargabata nayi, nayi bismillah nima na hau. Bayan anyi duk abunda yakmata muka lula sama, banda ya faruq da driver su gida suka koma. Ajiyar zuciya nasauke nadubi aliya dake kusa dani kasa_kasa nace mata. “Ke kinji yanda nakejina kuwa gaba daya atsorace nake” dariya aliya tayi ahankali yanda babu mejinta seni tace, “aina lura dake tun ashigowa tamkar mekoyon tafiya” “kedai bari abunda baka saba” “kenima wannan ne hawana na uku, dama indai zakuyi tafiya da daddy, indai irin state ne haka ba wata kasarba a Jet yake zuwa” “auww, dama wannan ne jet din a wani American firlm nataba ganinsa” “ehhh, shine na dady ne yanama da wani bayan wannan” kawar da zancen jet dinnayi da fadin “kinwa Aunty zancen yaya Sadiq kuwa?” “Ehhh, na mata tacemun zamuyi maganar idan mundawo daga tafiyar yan” “Tom shikenan,Allah yadawo damu lafiya” “Ameen”…..
Munsauka a garin Jos lafiya a unguwar Rikkos. Garin lumlumlum dashi babu zafi, bakamar kanoba da muke da tsananin rana, garin ya burgeni gasu da duwatsu. Hamdala matarnan tayi ganin sun sauka a gida lafiya, ita kam zuwa Kano bemata dadiba amma bawa baya kaucewa kaddararsa koda a gidama take idan Allah yayi setayi accident din. Gidannasu babbane me kyau daga gani suma masu haline. Amma irin family house dinnanne. wani part dake hannun dama muka nufa,muka yada zango a falo. wata mata ce tatarbemu wadda bazata haura shekara 32 ba. da fara’arta se sannu da zuwa take mana. dukkanmu muna zaune a falon harda yaya Mustapha da daddy. duban matashiyar matar A’isha tayi tace. “Zuhura ina Aunty Maryam, dasu mama?” “Mama tana part dinta, ammi kuma tana ciki, may be bataji zuwanku bane” mikewa A’isha tayi ta shiga wani daki dake falon bayan tace mana zuwa, itama matar damuka tarar mikewa tayi ta shige kitchen. Shiru falon yayi, nikam tunda muka shigo gidannan gabana yake faduwa bana wasaba, abun harya bani tsoro sosai, akwanakinnan inajin haka sosai atattare dani amma na yanzu yafi na kullum, addu’a kawai nashiga karantawa a cikin zuciyata. satar kallon yaya Mustapha nayi naganshi yajingina bayanshi da jikin kujera idanunsa a lumshe tamkar kowanne mafiya yawan lokuta danake ganinsa. maida kallona nayi ga Aliya datake danne danne waya. maman matar damuka kadece ta shigo falon da sallama ita da kanwar matar fuskokinsu dauke da fara’a. “Sannunku da zuwa” tsohuwar ta fada bayan ta zauna. daddy ne ya amsa mata da fadin. “Yawwa sannu baaba, dafatan kunzo gida lafiya, ya hanya?” “Lafiya kalau Alhaji, sannunkufa angode, Allah yasaka da alkhairi” “Ameen, ameen” gaisheta mukayi gabadayanmu amma banda yaya Mustapha dako motsawa beyiba, itama kanwar matar gaisawa mukayi ta nufi kitchen gurin zuhura. “Mustapha!” Daddy yakira sunansa ganin yanayin dayake ciki. Mustapha dayakejinshi a wata duniyar daban, saboda wani matsananci bugu da zuciyarsa take masa,kansama jinsa yakeyi tamkar ze rabe biyu. idanuwansa da suka masa nauyi yabude a hankali ya kalli daddy. amma bece komaiba. kallo daya daddy yamasa yasan da akwai matsala saboda yanayinsa gaba-daya ya sauya.ya hango tsantsar damuwa a idanun dannasa. cikin tausayawa daddy yace masa. “Ga mahaifiyarsunan kugaisa” maida dubansa yayi ga matar, zuciyarsa na kara tsananta bugu, cikin matukar dauriya yace mata. “Ina wuni?” asanyaye. matar wadda ta zuba masa ido kawai tana kallonsa tace. “Lafiya kalau, ya jikinnaka” (dayake duk sunsan bashi da lafiya) dauriyarsa ta kare hakan yasa ko harafi daya baze iya kara furtawa dan yanayin dayakejin kansa ya yawaita, dakai kawai yabata amsa. gaba-daya falon yabasu tausayi musamman Aunty da daddy dasukan damuwarsa, kawar dakai Aunty tayi daga kallonsa cike da tsananin tausayinsa. Maryam kuwa batasan daliliba kawai taji kwalla tacika mata ido. maman azatonta jikinnasane dan haka tace, “Allah yakaro sauki, aidama yayi zamansa tunda bashi da lafiya, tafiyarma seta karawa mutum ciw…” Fitowar matar da daddy ya kade ita ta katsewa mama maganar datakeyi. wata kyakkyawar macece tamkar balarabiya biye abayanta, tana sanye da abaya me matukar kyau, wadda taji adon dutsuna, ta yane kanta da mayafin abayar. tana sako kafarta cikin falon wayarta dake hannunta tayi kara alamun kira, dakatawa tayi ta daga wayar cikin wani irin bakon yanayi mewuyar fassaruwa daya risketa a lokaci daya. kafin tagama wayar su zuhura sun fito daga kitchen hannayensu dauke da farantai dake dauke da ruwa da lemuka,suka dire agabanmu. da sallama kyakkyawar matar ta karaso falon, gabadayanmu muka daga kai muka kalleta saboda dadin muryarta duk da ta manyanta. siririn farin glass din dake idonta ta zare ta rike a hannunta, kyawawan idanunta farare tass suka bayyana wanda ta saukesu akan fuskar Maryam………….✍️