
masu complain na rage yawan typing, kuma kun rage yawan comment ne, idan kun gyara nima zan gyara
By
zeey kumurya
4️⃣5️⃣
Bismillahirrahmanirrahim
………..A tare zuciyoyinsu suka buga da karfin gaske, kallon cikin ido matar take yiwa Maryam. Ita kuwa Maryam dasauri tayi kasa da idonta bugun zuciyarta na tsananta. a ranta tana fadin, “tsarki ya tabbata ga Ubangijin da yayi wannan kyakkyawar halitta.” ita kuwa matar kara kafe Maryam tayi da ido, zuciyarta nacigaba da bugawa saboda mamakin abunda tagani a tare da Maryam. mama dabata lura da halin da Maryam da matar suke cikiba ta fadada fara’a tana duban matar tace. “Wannan matar yayansu ce daya rasu, shine babban dana, lokacin da akayi hatsarin tana Saudiya ne ta kaiwa mahaifiyarta da kaninta ziyara se jiya ta dawo” kallon matar daddy yayi a karo na biyu zuciyarsa na kissima masa wani abu akanta, muryarta ta masa dadi bakadanba, yayi mamaki daya kalli fuskarta yaga ta manyanta dan muryartata tamkar ta wata matashiyar saboda dadinta da sanyinta. ga muryartata ta sanya masa wani abu a cikin zuciyarsa wanda yakasa gane ko menene, hakan yasa yaji yanakuma son yakarajin muryartata. numfashi matar ta sauke, tana kokarin daidaita nutsuwarta. maida kallonta tayi ga Aunty datake gaisheta. Amsa mata tayi cikin sakin fuska. tana kokarin zama akan hannun kujerar da mama take, tamkar ance ta dago kanta idanunta yasauka akan Mustapha,daya kafeta da ido yana kallonta. wata mahaukaciyar bugawa zuciyarta tayi cikin tsananin razani tafasa zaman datake kokarinyi, ilahirin jikinta ne yadauki rawa tamkar mazari, hannunta na rawa take nuna Mustapha tanason tayi magana amma takasa, wani dimmm taji kanta yayi juwace ta kwasheta kawai segani akayi tayi kasa zata fadi. Dasauri matar da daddy yakade da mama sukayi kanta saboda sunfi kusa da ita, gaba-daya mutanen falon sukayi kanta, banda Mustapha dayakasa koda motsi, da Maryam. “Innalillahiwa’inna’ilaihirraji’un” abun bakunansu kawai suke iya furtawa kenan. “Zuhura kikira Saddam, maza yazo mukaita asibiti jibifa jikinta yashika ko numfashi batayi” cewar matar da dady kayade cikin tsananin tashin hankali. “Nashiga uku, ni salamatu, dan Allah kutaimakamun mukaita mota, base munjira wani Saddam ba, semunje ta mace mana” mama tafadi haka tana hawaye. Aunty ce tace, “dama tanayin haka, kotana da wani ciwonne” “wlh bata da ciwon komai yarnan, bamu taɓa ganin tayi haka ba, seyau” mama tabawa Aunty amsa da fadin haka. “Ina ganinfa kamar suma tayi, a kawo ruwa mugwada watsa mata,zata farfaɗo insha Allah” daddy yafadi haka cikin son ya kwantar musu da hankali, ganin yadda gaba-daya hankulansu yatashi, zuhura da kanwar matar da daddy yakade harsun fara kuka. zuhurance tayi sauri taje ta dakko ruwa a fridge ta kawo, zuba mata ruwan aka shigayi a fuskarta zuwa kirjinta. kusan mintuna biyu ana zuba mata ruwan kafin taja wata doguwar ajiyar zuciya. Numfargashi tafara saukewa akai,akai. ganin ta farfaɗo sukayo kanta da mata sannu zukatansu cike da Murna. “Babu shakka familinnan suna matukar son matarnan” Aunty ta fadi haka a cikin ranta.
A hankali ta bude idanunta tana kallon mutanen dake zagaye da ita, hannun matar da daddy yakade ta kama, cikin sanyin murya me cike da rudani tace mata. “A’isha bani ruwa insha, guntun ruwan da’aka tsiyaya mata, A’ishan ta taimaka mata ta bata tasha. Ajiyar zuciya ta sauke tana kallon mama tace, “mama wani mafarki nayi me rikitarwa” “wanne irin mafarki kuma diyar kirki” maman tatambayeta cike da mamaki. “Mama tunda natashi yau, nakejin wata irin faduwar gaba, jikina duk babu dadi kamar wadda wani mugun abun zesama, sekuma yanzu nayi mafarki A’isha tashigo dakina tasameni wai inzo mugaisa da mutanen dasuka bugeta, shine naga wani a zaune a falonnan, wlh yanda kikasan mijina na farko daya rasu babu abun daya banbantasu nakamanni, shine abun ya matukar firgitani” dammmm! Zuciyar daddy ta buga, jin muryar matar, a yanayin datayi magana yanzu babu banbanci da muryar matar data bashi Mustapha, shikanshi yana mamakin yanda amon muryar matar yakasa bacewa daga kwanyarsa duk kuwa da tsayin shekarunnan da aka dauka, a lokuta da dama idan yana zaune shikadai kalaman matar suna masa amsa kuwwa a cikin kwakwalwarsa. gabadaya falon tsit yayi dama Mustapha da Maryam basusan me’akeba. Sukuwa su mama, basu wani dauki zancen matar da mahimmanciba sun dauka zafin ciwon daya sametane lokaci daya ya firgitata. Aunty kuwa kallon matar kawai takeyi, ta kalli Mustapha ta kalli maryam. nuna Mustapha tayi tana kallon matar tace, “ko wancanne wanda kika gani ɗin?” dasauri matar ta kalli inda Aunty ta nuna mata, tozali idanunta suka mata da Mustapha wanda idanunsa suke a lumshe yanzu saɓanin dazu dayakafeta da tsumammun idanunsa shiyasama ta tsorata sosai harta sume. gani kawai sukayi ta mike tsaye zumbur, kura masa ido tayi na wasu sakanni kafin ta fara murza idonta dan tabbatar da ba gizo yake mataba. cikin karaji da matsananciyar rudewa muryarta na rawa tace, “sh…sh..shi..ne wlh, shineeeee!.” takarashe zancen da jan maganar.
“shine wa Aunty Maryam” Aisha tatambayeta tana riketa ganin yadda duk ta burkice lokaci daya, mama baki sake take kallonta, danko sanda mijinta dan maman yarasu batayi irin wannan birkicewarba da gigicewa. “Dan Allah A’isha wanene shi wannan din danake ganinsa, koku bakwa ganinshine, kikalleshi zakiga kamarshi da miji na MODIBBO” “Danane” muryar daddy ta doki dodon kunnenta, dasauri ta kwace daga rikon da A’isha ta mata, taje gaban daddy cikin kuka tafara masa magana da fadin. “Danka, kuma?” To meyasa yake kama da mijina, hatta azurfar hannunsa irintace a hannun mijina harya mutu” “wai MARYAM, meke damunki ne, wanne mijinnaki kike magana akai, mufa bamugane mekike nufiba,gabadaya duk kinbi kin firgitamu” mama tatambayeta cikin dunbin al’ajabi, dan ita abun matar yafara bata tsoro harta fara tunanin ko matar tayi gamone. hannunta Aunty takama ganin duk falon sunkasa aiwatar da komai, hatta daddy kuwa daya tsaya kawai yana kallon matar. cikin lallami Aunty tafara mata magana. “Baiwar Allah, nasan ke musulmace kuma kinsan babu ta yadda za’ayi wanda yamutu yadawo, a kalamanki kuma naji kina fadin mijinnaki yarasu, kuma wannan danmune dashi mukazo garinnan, kinga babu tayanda za’ayi yazama mijin ki” “tabbas mijinannawa yarasu tun shekara fiye da talatin dasuka wuce, Amma kuma yau gashi naga wani me matukar kama dashi ai dole na shiga rudu” “baku da dane tare da mijinnaki?” Aunty tatambayeta cikin son tabbatar da abunda take zargi. kasa matar tayi dakanta idanunta na shatatatar da hawaye, tausayintane yacika su mama da iyalanta. cikin matsanancin kuka tace, “bani da ɗa ko ɗaya a duniyar nan” hawayene yaciko idanun Aunty, wani matsanancin tausayinta ne taji yashigeta lokaci ɗaya. shikanshi daddy seda kwallar tacika masa ido saboda yanda matar take kuka tamkar ranta zefita, ga dukkan alamu an sosa mata wani mikine a cikin ranta. Lokaci daya Mustapha daya kurawa matar ido kawai yana kallonta tun sanda tafara magana, yaji wani matsananci tausayinta gami da zazzafar kaunarta ta cika masa zuciya. rungume matar Aunty tayi tsam ajikinta, sedai batayi yunkurin rarrashintaba dan ta hanata kukan datakeyiba. tasan kukanne kadai ze rage mata radadin datakeji a cikin zuciyarta dan rashin haihuwa ba karamin abu tawaya bane ga dan adam. Maryam da aliyama hawayene kawai yake zuba a fuskarsa na tausayin matar, dan duk wani me imani idan yaga yadda matar take kuka seya zubar mata da hawaye. su mama kuwa mamakine yakamasu na matar, dan bata taɓa shiga irin wannan yanayinba akan rashin haihuwartata, saboda macece ita me tsananin tawakkali akan duk yadda rayuwa tazo mata,lokuta da damama mijinta yafita nuna damuwa akan rashin haihuwar tata. Daddy dayakejinsa tamkar mafarki yake, saboda duk wata alama dazata nuna masa matarnan mahaifiyar Mustapha ce ta bayyana agareshi. Saboda hujjojin dayake dasu kwarara guda biyu. Nafarko zancen azurfar dake hannun Mustapha datayi, na biyu kuma kukanta datakeyi yanzu yayi iri daya sak da wanda tayi lokacin data bashi Mustapha. sunayen Allah kawai yake kira danshima nutsuwarsa kokarin barinshi takeyi, haryanzu yakasa tabbatarwa da kansa ba mafarki yakeba, matar data bashi Mustapha itace tsaye agabansa. tattaro duk wata dauriyarsa yayi ya sarrafa harshensa dakyar yace, “kin taɓa haihuwa ne?” barin jikin Aunty tayi da sauri saboda yanda tambayar ta daki zuciyarta batare data dena kukan datakeba tace. “Ehhh!” tamkar mekoyan magana. mamakine yakama su mama domin su bata taɓa ce musu tataba haihuwaba, sun sandai tataba aure kafin ta auri baban Saddam. dauke kukan datakeyi tayi dif tamkar ba itaba, taci gaba da magana. “Nataba haihuwa na haifi yaro namiji amma yanzu bansaniba koyana raye koya mutu dan……” “Yazakiji idan nace miki wannan shine dannaki dakika taɓa haifa?” Daddy yakatseta da fadin haka cikin karfin zuciya yana nuna mata Mustapha. Ba ita kadaiba babu wanda kalaman daddy basu daki zuciyarsaba a falon, hatta Aunty kuwa da take da haske akan hakan. Maryam da aliya sunfi kowa shiga rudu, dama aliya itacan arude take banda zare idanu tana kallon mutane babu abunda takeyi. Maryam kuwa bata fahimtar komai, cikin duhu kawai kalaman daddy suke kara sanyata. Shikuwa gogan wato Mustapha wata muguwar faduwar gabace ta riskeshi shifa gani yakeyi abubuwan dasuke faruwa duka mafarki yakeyi ze iya farkawa wani lokacin. batasan sanda ta kama hannun daddy ba duka biyu tana maimaita kalmar. “daaanaaa…daaanaaa…” Tamkar wata mara fahimta. Abin gwanin ban tausayi. daddy danne wani abu daya darsu a zuciyarsa yayi yace, “ehh, dankine, duk da banji wani bayani akan kiba amma wasu hujjojina masu karfi sun tabbatar mun da kece matar dakika bani jariri, a wani dare akasar Niger a garin Niamey?” ilahirin jikintane yaɗauki kyarma gami da ɗauke war numfashinta na wasu sakanni a lokaci guda. Tabbas bazata taba manta wannan ranar data bayar da danta gudan jinintaba harta koma ga mahaliccinta. “Kidena mamaki, akan ikon Allah, domin buwayarsa ta wuce tunanin me tunani, shine me sauya al’amari a duk sanda yaso kuma a lokacin dayaso,kije ga danki da Ubangiji ya hadaku a lokacin da bakuyi tsammaniba dukanku.” murmusawa daddy yayi yamaida kallo nsa ga Mustapha daya zama tamkar mutun mutumi yace. “Son, come to your real mom”
A matukar firgici ta juya ta kalli su mama, da mamaki yahanasu koda kwakkwaran motsi idanuwansu kawai suke bawa abinci suna ganin abun tamkar wasan kwaikwayo, banda haka daga mutane sun rakosu sekuma dansu yazama na wata. cikin sauri ta juya ta nufi inda Mustapha yake wanda ko motsawa beyiba daga zaunen dayake, zuciyarta na tsananin bugawa tasa hannunta dake rawa tafara balle botiran gaban rigar Mustapha, lumshe idansa yayi shima tasa zuciyar natsananta bugu tamkar zata faso kirjinsa ta fito, wanda har mahaifiyartasa tanajin bugun zuciyar tasa. singlet fara kar itace ta bayyana bayan ta gama balle botiran gaban rigar tasa, cikin zafinnama da karfin dabatasan tana dashiba ta yaga singlet din gida biyu, faffadan kirjinsa fari tass dashi me dauke da kwantaccen bakin gashi yabayyana. a kirjinsa daga ɓangaren dama ta kurawa ido, wani abune asaman nononsa baki. (rowa) abunka da farin mutum tafito tayi dodar. cikin fitar hayyaci saboda tsabar farinciki tarungume Mustapha ajikinta tana me fashewa da kukan murna. “babu shakka, kai danane nacikina, dukda nasan mafarki nakeyi,zan iya farkawa a kowanne lokaci amma hakan baze hanani nuna farincikinaba akan ganinka…….” Zantuka tayi ta saki na farinciki cikin matsanancin kuka tamkar zata shide tana shafa sumar kansa. shikuwa Mustapha lokacin data rungumeshi wata doguwar ajiyar zuciya yasauke, yanajin wani shauki nabin dukkan jiki da ruhinsa, wata nutsuwa saya rasa a rayuwarsace yaji ta lullubeshi lokaci guda, ga tsananin kaunar matar data cika dukkan zuciyarsa. wasu sanyayan hawayene suka fara zuba akan kuncinsa……….✍️