Uncategorized

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE HAUSA NOVEL

By
Zeey kumurya
4️⃣6️⃣

Bismillahirrahmanirrahim

………….Yarasa a wacce duniya yake saboda, dadi,al’ajabi da mamaki. Tamkar ansauke masa wani abu mai nauyi a cikin zuciyarsa haka yaji. farinciki mara misaltuwa ne yamamaye dukkan baƙin cikin dake cikin zuciyarsa. jikinsane yayi wani irin sanyi tubus hakan yasa yakasa tabuka komai, koda danyatsa daya yakasa motsawa. falon yayi tsit bakajin komai se sheshshekar kukan ammi wadda take kara manne Mustapha akirjinta, tanajin tamkar ta maidashi ciki saboda tsabar kauna. lumshe idonsa yayi yakara kwantar da kansa ajikinta yana shaƙar sassanyan kamshinta,wani dumi yaji yana shiga jikinsa, ajiyar zuciya yake sassaukewa akai_akai. Aliya da tsaiwa ta gagareta ta zube akan kujera cikin rawar murya ta dubi daddy dayaketa murmushi me nuni da yana cikin tsananin farin ciki tace. “Da..daddy.. tayaya tazama mom dinsa?..mommy fa?..” taku daddy yayi yazauna a kusa da ita har lokacin fuskarsa nadauke da murmushi, gefen kuncinta yashafa yace, “bazaki fuskanci komaiba, autar Aunty amma very soon nasan zakigane yanda abun yake nanbada jimawaba” yanda aliya ta kurawa daddy ido tana kallonshine yagane bata fuskantar meyake nufi. Aunty ma zama tayi a kusa da Maryam wadda ta kurawa su Mustapha ido, ko kiftawa batayi. share hawayen fuskarta Aunty tayi tare da kauda kanta daga kallon su Mustapha. Sosai tausayinsu yake ratsa zukatan kowa dake falon musamman ma ammi. A hankali mama tafara jan kafarta data mata nauyi tazo gaban daddy, cikin daukewar tunani tace masa. “Alhaji, dan Allah, kafitar damu daga cikin duhun dakuka samu, gabadaya kunsa zuciyoyinmu cikin tararrabi, tayaya danku dakukazo dashi zezama dan Maryama.?” “Labarine metsaho mama, dole semun zauna mun nutsu sanna zamu warware muku zare da abawa” “daddy yabata amsa cikin girmamawa. numfashi kawai ta fesar taja kafarta, ta karasa inda su Mustapha suke, tafarawa ammi magana cikin lallami danta fuskanci tahakane kawai zata iya barin wannan kukannata. “Haba, Maryam kukan na menene haka,kiyi hakuri kiyi shiru kibar kukan haka, kizo ki fitar damu daga cikin duhun dakika sanyamu” a hankali taraba jikinta dana Mustapha wanda ya wani manne mata, sekace karamin yaro. Kukan datakeyi ta dena se ajiyar zuciya take saukewa. Mustapha kuwa kasa yayi dakansa idanunsa a lumshe, beso tsohuwar ta katse masa samun nutsuwa da jindadin dayakeji dalilin jinsa a jikin mahaifiyarsaba sedai tsananin miskilancinsa baze bari kagane yanayin dayake cikiba. kama hannun ammi, mama tayi tazaunar da ita akan kujera ta fara share mata hawayen fuskarta cikin tsananin so da kaunarta. Tun ba yauba, ta fuskanci akwai wani abu dake damun zuciyar ammin, tana dannewane kawai, domin lokuta da dama tana taddata cikin zurfaffen tunani ko kuma cikin yanayi nadamuwa. kallon Mustapha kawai ammai takeyi takasa dauke idonta daga kansa, wani sanyi takeji yana ratsa zuciyarta. maida kallonta tayi ga mama tare da kama hannunta cikin sanyin murya tace, “mama dan Allah abunda yake faruwa gaske ne ba mafarki nake ba, wlh nakasa tabbatarwa da kaina.” cikin tausayawa mama tace. “Gaske ne Maryama ba mafarki kikeba, azahiri komai dakika gani yake faruw….” Ai ammi bata bari mama takarashe zancen taba ta zube a kasa tana sujjada domin nuna godiyarta ga Ubangiji. “Alhamdulillah, Alhamdulillah, Alhamdulillah” daddy, aunty, mustapha, ammi suke furtawa a cikin zukatansu tamkar hadin baki cike da tsananin farin ciki. A’isha da kanwarta mesuna Halima tare da surukarsu wato zuhura, mazauni sukayiwa kansu dan sunga abun bana ƙarau bane, ga ƙafafuwansu duk sun sage saboda tsaiwa………….

farincikin da dady da Mustapha da ammi suka nuna akan haɗuwar Mustapha da mahaifiyarsa a wannan lokacin baze misaltuba, duk miskilancin Mustapha kasa jurewa yayi yaje ya rungume mahaifiyarsa cikin tsananin shaukinta da kaunarta mara misaltuwa a cikin ransa, tabbas ya yarda mahaifiya daban take, dan yanayin dayake jin kansa akan bayyanarta baze misaltuba. ita kuwa ammi se shafa kansa takeyi tana sumbatarsa, takasa dauke ido daga kallonsa ko kunyar surukartata yau bataji. babu abunda yaraba Mustapha da mahaifinsa hatta tafiyarsu kuwa, har miskilanci data fahimci Mustapha’n dashi duk na mahaifinsa ne, yanayin yanda yake kallon abu dakuma lumshe ido shine kawai irinnata, amma komai na mahaifinsa ne. mama ganin kamar sun manta dasu agurin ta junansu kawai sukeyi tace sudai, ammi tazo ta fitar dasu daga cikin duhun dasuke. badan ammi tasoba taraba jikinta dana danta, abin kaunarta tace kowa yaje yayi Sallah don har anyi la’asar sannan ta basu labarin. Bayan kowa ya idar da sallar suka kara hallara a falon dukansu kowa yazaku yaji yanda abun yakasance, dan abun yarikitar dasu bakadanba musamman Maryam da aliya dasukasan mommy ce ta haifi Mustapha. Gyara zama ammi tayi tafara bada labarinta kamar haka…

“Sunana MARYAM IBRAHIM, mu yan ƙasar NIGER ne, anhaifeni a garin NIAMEY. Anan natashi anan na girma anan nayi makarantata anan nayi aure. mahaifina ba wani mekudi bane saidai yanada rufun asiri daidai gwargwado. mahaifiyarmuce kaɗai matarsa kuma mu biyu ta haifa, nice babba se kanina MUHAMMAD. muntaso cikin son junanmu, iyayenmu sunbamu tarbiyya wadda kowa yake yabanmu. inada shekara goma sha biyu kanina kuma tara, Allah yayiwa mahaifinmu rasuwa. Tun daga wannan lokacin rayuwa ta fara sauya mana,muka fara rayuwar maraici. Muhammad yakasance yaro me kwazo da zuciya. Tun baifi shekara goma sha biyuba, yake ƙoƙarin neman nakansa. Akwai wata makociyarmu matar tana da kirki sosai, kuma tsohuwace ta manyanta. mijinta itama yarasu yabarta da yaya maza guda biyar, tasake aure ta haifi yaro ɗaya shima mijinnata yarasu, se yan’uwan baban yaronnata suka daukeshi. Saboda masu kuɗi ne sosai, mahaifin yaron yamutu yabar masa dukiya me tarin yawa. Duk kafin a haifeni akayi haka, tsohuwar dakanta take bani labari. saboda Allah yahada jinina da ita. nibanmasan tana da wani ɗa ba, bayan biyar ɗin data haifa da mijinta na farko, dan da mijinta na biyun yarasu seta dawo gurin ƴaƴanta suka cigaba da zama tare. Tumunin takabar da’aka bata na gadon mijinta shitake juyawa take saide_saide. matar tana sona sosai kasancewar bata ƴa mace, haka zata saimun kayan kwalliya na mata da abubuwan buƙata. Seda dannata ya girma yazama saurayi sannan yadawo gurin ta, a lokacinma duka yayannata biyar ɗin sunyi aure. Sanda yadawo gurinta inada shekara 16. Kyakkyawane shi, dominshi ruwa biyu ne, mamansa buzuwace kamar mu, mahaifinsa kuma bafulatanine. Haka kawai Allah yadoramun tsoronsa dan gaskiya yana da kwarjini, gashi miskili, kuma baya sakarmun fuska, amma fa akwai shi da kyauta. Abun hannunsa betsone masa idoba. amma suna shiri sosai da kanina Muhammad saɓanin Ni, hakama mahaifiyarmu kullum seya shiga yagaisheta yamata abun arziki. sana’ar saida gwala-gwalai yakeyi yana zuwa Dubai da Saudiya yana sarowa, Allah kuma yabuda masa sosai. sauran yan’uwansa sesuka hade kansu suke nuna basa kaunarsa, afili karara suke nunu masa kiyayya. Amma shi babu ruwan shi haka yake girmamasu kuma komai suka ce yamusu yana musu, yasai musu gidaje yabasu jari, kuma idan suka zo da bukata haka zemusu. mahaifiyarsu da kanta take masa faɗa, akan yadena yawan basu kudi tunda suma barasawa sukayiba. Aduk lokacin da tamasa zancen haka, sedai yayi murmushi yace mata “idan be musuba wazewa bashifa da wasu yan’uwa sesu, tunda mahaifinsa shikadai yahaifa shima. ai bashida kamarsu.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button