Uncategorized

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE HAUSA NOVEL

kuyi hakuri da wannan, banjin dadine, dakyar nasamu na muku wannan ɗinma. ABUNDA KASHUKA FAN’S GROUP, nagode sosai da addu’oinku, Allah yabar zumunci mai ɗorewa Ameen????????

By
zeey kumurya
4️⃣8️⃣

Bismillahirrahmanirrahim

…………Fitilar dake hannunsu na hango ta cikin glass din motar,suna tafe suna dube_dube. wata boyayyiyar ajiyar zuciya nasauke lokacin danaji me motar yaja motar mun fara tafiya. Se’alokacin naji wani gumi yana ketomun duk da motar akwai sanyin a.c amma tamkar heater haka tazamarmun. tunanin mahaifiyata da kanina ne yafadomun a cikin zuciya, “yaya zasuji idan suka wayi gari sukaga babu ni a cikin gidanmu?” natambayi kaina, wasu zafafan hawayene naji sun zubomun a kuncina. Ga wata masifaffiyar kewar ɗana data cikamun zuciya, danasan zan hado da wannan bawan Allah, da bazan bada yarona ga wani wanda bansaniba, bansaniba shima koba mutumin kirki bane, idona yarufe a lokacin dana bada ɗana ko tunanin me mutumin yakeyi cikin dare a waje banyiba na bashi dana, kuka me karfine yatahomun, da sauri na cusa kasan dankwalina na toshe bakina dan kar kukan yafito. “Kiyi hakuri, ki fawwalawa Allah dukkan lamuranki, kuma dukkan tsanani yana tare da sauki” mai motar yafadamun haka cikin sanyin murya. Ajiyar zuciya nasauke ina kokarin hadiye kukana nace masa. “Nagode” “ina kika nufa ne, acikin wannan daren” ya tambaye ni. shiru na masa dan bansan mezan kumace masa ba, danni kaɗai nasan irin azabtuwar da zuciyata takemun. kuncin danake ciki a wannan lokacin baze misaltuba, rasama tunanin dazanyi nayi, tun ina gane wasu abubuwan harna fice daga hayyaci na, saboda damuwa. farkawa kawai nayi naganni a cikin gidannan, kwance akan gado, ansanyamun drip a hannuna. mama da mutumin daya daukoni a mota tare da matarsa na gani adakin, sannu suka shiga yimun tare damun ya jiki, nidai da ido kawai nake binsu,ba bakin magana. Bayan ruwan yakare anciremun, mama tataimakamun nayi wanka, tabani tea nasha bisa dole sannan nasha magani narama sallolin da’ake bina azaune. bansan yazan fada muku halacci da karramawa irin ta mutanen gidannanba, sun rike tamkar jininsu, mama tasoni sosai, dan bata banbantani da ƴaƴanta. Alokacin su A’isha suna yanmata tare take hadamu take yimana komai. A duk lokacin da mama da Alhaji Bashir (wanda yaɗauki ammi a mota) suka tambayeni tarihina bana ce musu komai sedai naita kuka, hakan yasa suka kyaleni suka dena tambayata. matar alhaji Nasir, zakiyya macece me kirki tajani a jikinta sosai bata nunamun wani abu na kyara ko tsangwama. A lokacin danazo gidan Saddam yana karami danko yayeshi batayiba. seyazama kullum nice mai rainonsa yana hannuna kokuma in goyeshi, shiyake debemun kewar Muhammad dina, wanda kullum sena kulle kaina adaki nayi kukan rashinsa dana adalin mijina. Ga kewar mahaifiyata data kanina tana damina a rai. haka rayuwa taita tafiya. wasa_wasa segashi har nayi shekara biyu a NIGERIA a garin JOS. Alhaji Nasir, dan kasuwane yana sarar kaya yana kaiwa gariri, ranar daya dakkonima yakai wa wani abokin kasuwancinsa kayane, kuma dare yamasa a hanya, gashi yana da uzurin dazeyi a safiyar ranar shiyasa bebari ya kwanaba a nijer ɗin. Lokacin da alhaji Nasir yanuna yana son aurena, kin amincewa nayi saboda yadda muke da matarsa. mama tayita bani baki akan na amince da auren, indai zakiyyace bata da matsala. Itama zakiyyan a lokacin dakanta ta dinga nunamun bakomai tana bani baki. Ganin haka sena amince, dama kuma bakinshi nakeba. suda basusan asalinabama suka nemi na shiga cikin zuri’arsu seni zankisu. munyi aure da alhaji Nasir muka cigaba da rayuwarmu cikin farin ciki. Alhaji Nasir yana kwatantata adalci atsakaninmu, muma kuma muna mutunta juna nida zakiyya, hakan yasa zamanmu lafiya lau. Saddam yana shekara 6, zakiyya takuma samun ciki. ta haifi yarta mace, aka samata sunan mama ummussalma, amma umaimah ake cemata. Umaimah batafi shekara 1 ba, akayi bikin A’isha da wani abokin alhaji Nasir. umaimah nada shekara uku Allah yayiwa mahaifiyarta zakiyya rasuwa. Se rikonsu yadawo hannuna gaba-daya ita da Saddam, nikuma har zuwa wannan lokacin ko batan wata bantaba yiba. Alhaji Nasir yama fini damuwa da rashin haihuwata shida su mama. wani lokacin ma ninake bashi baki, duk da nima abun nadamuwana amma haka nake danne zuciyata bana nunawa. Kullum da tunanin Muhammad ɗana, da mahaifiyata nake kwana nake tashi. A haka rayuwa tayita tafiya, ahalin gidannan suna sona sosai, tunda nake agidannan bantaba fuskantar wata matsala ta kyara ko cin mutunciba, girmamawa da mutuntawa itace tsakanina da kowa. Bayan wasu shekaru masu yawa munje kasa me tsarki sauke farali, Allah yahadani da kanina da mahaifiyata, munyi murna mara misaltuwa sosai a lokacinnan. mahaifiyata ta sanarmun da sun shiga tashin hankali bakadanba dasuka wayi gari babu ni a cikin gidanmu. kanina yashigar da yan’uwan modibbo kara akan sufito dani da ɗana, danyasan babu me zaceni sesu. Kuma yanada kwakkwaran hujja akan hakan, ganin dasukayi zetona musu asiri, sesuka masa asiri yabar kasar gaba-daya aka nemeshi aka rasa. Se bayan wasu shekaru yakoma, ya dauke mahaifiyarmu suka koma Saudiyya da zama anan yayi aure yanzu yana da yara guda biyu, mace da namiji. Se’alokacin su mama sukasan tarihina, dama tun lokacin da alhaji Nasir ze aureni, nasanar masa na taba aure mijinnawa yarasu. Amma banfada musu inada yaroba. mahaifiyata tamun fada sosai akan meyasa nabawa wani dabansanshiba yarona. daga karshe kuma takoma addu’a akan Allah yasa yana hannu nagari, idan yana raye Allah yahadamu, idan kuma ya mutu Allah yaji kansa. Alhaji Nasir a hanyarsa ta dawowa daga Niger wata ranar Litinin yakai kaya, Allah yamasa rasuwa. Naji mutuwarsa sosai shima kamar modibbo, nayi kukan rashinsa. Gashi shikadaine dan mama namiji se kannensa gasunan mata ne guda biyu, A’isha da nafisa. yanzu shekara biyu kenan da rasuwar tasa. Kanina yaso nakoma Saudiyya da zama, amma naki amincewa saidai nadinga kaimusu ziyara. dannasan idan natafi su mama bazasuji dadiba, gakuma umaimah datake kallona a matsayin mahaifiya, bazan iya tafiya inbartaba. Zuwa yanzu nariga na fidda rai, daganin Muhammad ɗana, dan shekara 33, ba wasabace. saidai kullum cikin yimasa addu’ar alkhairi nake, a duk inda yake.” numfasawa ammi tayi tace, “inafata yanzu dukkanninku kun fita daga cikin duhun da kuke” Maryam data kurawa matar ido kawai tana kallonta, kasa tayi dakanta tana hawayen dabatasan dalilinsuba. Mama ce, tace. “Gaskiya Maryama kinsha gwabarmaya, kai mutane babu Allah a ransu yanzu duk wannan abun dayafaru akan dukiyane fa, dukiyar daza’amutu abarta.” Aunty ce ta amshe zancen da fadin. “Hmmm, wlh mama abun ba daɗin ji, mutane gabadaya kudi yasa sun manta da Allah, kaga mutum yayi shirka, yayi kisa duk akan kuɗi, kuma karshedai dole mutuwa mutum zeyi ya barshi, Allah yasa mudace kawai.” “Ameen, suka amsa gaba-daya banda maryam da Mustapha daya amsa aransa. Kallon ammi daddy yayi yace, “angano wadanda suka kashe modibbonnaki?” kallon daddy ammi tayi itama, dasauri kuma ta dauke kanta daga kallonnasa sannan tace. “Ehhh, anganosu yan’uwansane suka sanya a kashe shi, yanzu haka suna gidan yari anmusu daurin rai da rai, dasu da wadanda sukayi kisan, amma mutumin biyu a cikinsu sun rasu, da babban su, da kuma na tsakiya yanzu saura su uku.” cikin gyada kai mama tace, “kinjifa, yanzu mene ribarsu akan abinda suka aikata?.. gashi yanzu karshe sedai sukare rayuwarsu a gidan yari, gashima wasu daga cikinsu harsun je inda shi modibbon yaje” “to ai dama mama duk ABINDA KASHUKA, SHIZAKA GIRBA arayuwarnan” cewar Aunty. Aliya kam mamakine yakara kasheta dataji wai mommy ba ita tahaifi yaya Mustapha ba, duk tarin kaunar datake nuna masa. gyaran murya daddy yayi yace. “Alhamdulillah, Alhamdulillah, Alhamdulillah. dukkan godiya da yabo sun tabbata ga Allah madaukakin sarki, daya nuna mana wannan ranar gabadayanmu, Allah yajikan wadanda suka rigamu gidan gaskiya mukuma intamu tazo yasa mucika da imani, Allah yarabamu dayin abin da zamuzo muna danasani akansa a rayuwarmu, Allah yaraya mana zuri’a, yashiryar dasu bisa tafarkin addinin Islama” “Ameen, ameen” suka amsa gaba-daya. duban ammi daddy yayi yace. “Nasan yanzu zuciyarki babu abunda takeson ji, sama dana baki labarin abunda yafaru bayan kinbada danki ko?” Murmushi ammi tayi tace, “kamar kashiga zuciyata kuwa, inason sanin kaina bawa ɗana, kokuma wanine yabaka riƙonsa kuma ina son sanin wacece ta raini ɗana, domin nagode mata.” shiru daddy yayi na wasu sakanni, yayinda ammi taketa kallonsa. “Nifa senaga tamkar nasankama amma narasa ina nasankan” A’isha ce tatari zancen ammi da faɗin, “zakisanshi mana, ko da agidan TV ko jaridu ne, shine fa alhaji mainasara” waro ido ammi tayi waje irin na mamakinnan tace. “Alhaji mainasara, shahararren dan kasuwar nan danakeji ana fadarsa” “ehh, shifa” gyada kai ammi tayi cikin mamaki. mamace tace, “kinyi mamaki ko Maryama, kinganshidai mutumin damukejin labarinshi a duniya, yau gashi zaune tare damu. Ai mainasara mutumin kirki ne, bakigaba yanda yamana da muna asibitinnan, karramawa babu irin wadda bamuganiba hakama ahalinsa suma masu mutunta dan’adam, basu dauki rayuwar su da zafiba,sundauki duniyarsu da sauki, shiya kullum yake ganin cigaba a al’amuransa.” murmushi daddy yayi ya kalli agogon hannunsa yaga har lokacin magriba yakusa, kuma yau yakeso su koma Kano, gashi yabar matukin jet dinsa a waje yana jiransu. gyara zama yayi yabasu labarin, daga lokacin da ammi tabashi Mustapha, har kawo yau atakaice. be boye musu komai ba, nadaga abunda mommy ta aikatawa Mustapha, dakuma taimakon da Maryam tayi agidansa. amma bece Sadik ne yakeyin fyaden ba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button