
Saleemat bayan tagama abunda take tayi wanka ta nufi gidan gwaggo. tundaga soro take zuba sallama amma taji shiru, tsayawa tayi a tsakar gida dan basa shiga dakin gwaggo. sallamar tacigaba dayi amma taji shiru. kofar banɗaki ta kalla taganta abude babu kowa a ciki. “Ko gwaggo batananne?” Saleemat ta tambayi kanta. amma kuma ai ko fita zatayi tana rufe dakinta koda tabar gidan abude. dakinnata ta shiga da sallama dauke abakinta, atunaninta ko gwaggo bacci take. yanayin dataga gwaggo bakaramin firgitata yayiba, kwance taganta baki a daure cikin jini, ga dakinta duk a birkice. cikin kidima ta fice da sauri taje ta sanar da umma, tare suka dawo gidan da umma. bakaramin gigita ummantayiba itama, fita tayi tasamu wani makocinsu ta masa bayani, saboda suna ganin girman umma mazan unguwar shiyasa ya yarda ya shiga gidan gwaggo amma badan itaba. hankalinsu umma a tashe ta kira baban saleema ta fada masa halin da’ake ciki. Napep aka samu akasaka gwaggo aka nufi asibin AMINU KANO da ita………….
Likitar mommy bata dawo kawo mata result dinba seda yamma bayan ta tashi daga aiki, kafin tazo suhailat tayi amai yakai sau hudu, kuma taki cin komai, amma zazzaɓin jikinnata yasauka, se Rashin kwarin jiki kawai kedamunta, har wanka ta iya yi da kanta. likitan ta girgiza dataga abun dake damun suhailat din. Jiki a sanyaye ta nufo gidan mommy, gaisawa sukayi da mommy dake zaune a falo tana waya, sannan tatambayeta ina suhailat ta nuna mata dakin datake da hannu. suhailat na kwance, Dr ta shigo dakin da sallama. Amsa mata tayi tare da yunkurin tashi zaune. “Sannu patient ya jikinnaki? cewar Dr, bayan ta zauna akan stool din mudubi. tace “Da sauki Dr,” “Masha Allah, yanzu i nane yake miki ciwo?” Dr, tatambayeta tana tsareta da ido. Tana yamutsa fuska tace, “kaina sekuma jikina da babu kwari inajin kasala sosai, sekuma jiri da tashin zuciya” Dr, tace. “Sannu, yaushe rabon dakiga period ɗinki?” dan jimm suhailat tayi tace. “Gaskiya namanta” “ohk, bari nasa Miki drip dinnan” Dr, ta fadi haka tana janyo jakar kayan aikin datazo dasu. Allurai taiwa suhailat na tsaida aman, sannan tasa mata karin ruwa. magunguna ta rubuta tabawa suhailat. addu’ar Neman sauki tamata sannan ta fice daga dakin cewa zuciyarta cike da tausayinta. Har lokacin mommy bata gama wayar datakeba. zama tayi taɗan jira mommy’n. katse wayar mommy tayi badan ta gamaba sedan ganin Dr ta fito. tace “Sannu Dr, harkun gama?” Dr, tace “Ehh, Hajiya namata allurar tsaida aman nakuma samata ruwa” “ok, babu magungunan daza’a siya?” “Akwai na rubuta nabata” “yawwa Dr, Nagode, amma babu kuɗi cash a hannuna, amma insha Allah anjima zanmiki transfer” “babu komai Hajiya, nizan wuce, ga result ɗin abunda ke damunnata” Dr, ta fadi haka tana mikewa. karba mommy tayi ta’ajiye akan kujera batare data dubaba, kokuma tatambayi Dr, abunda ke damun suhailat dinba, hankalinta nakan wayar dasukeyi ita da Binta akan zuwansu gurin boka gobe. sallama sukayi da Dr, tafice. daukar wayarta mommy tayi takira Binta suka cigaba da maganarsu……..
Su dadddy sun sauka a garin Kano lafiya. daddy zuciyarsa fess yakejinta yau yasauke dakon dake kansa na shekaru masu dama. Aunty a part din su baaba talatu ta sauka, anan sukayi sallah itada Aliya,baaba talatu ta kawo musu abinci sukaci sannan Aunty tatara ma’aikatan gidan mata tace musu za’a sallamesu gobe, badon sunyi lefin komaiba. amma za’acigaba da biyansu albashinsu, godiya sukayiwa Aunty duk da basusan dalilin hakan ba. abunda yasa Aunty tayi haka, a ganinta bedace suci gaba da zama agidanba tunda babu mata a gidan, bazeyiyu su zauna daga su se ya’yan gida da megidaba. seda suka kebe a daki sannan Aunty tayiwa baaba talatu bayanin abunda yake faruwa atakaice kamar yadda ta bukata. sosai baaba talatu tacika da rudu, da al’ajabin wannan abu. Amma batayi mamakiba dantasan halin mommy ciki dabai. amma bata taɓa zaton ba ita tahaifi Mustapha ba.
Aunty tana fitowa daga part din su baaba talatu ta nufi part din su Sadik, dan yau ta kudurcewa ranta seta ganshi taga halin dayake ciki, ai hannunka baya taba rubewa ka yanke kayar. su faruq duk suna part din daddy. knocking din dakinnasa ta shigayi, data murda handle din tajita a rufe. bubbuga dakin taitayi amma bebudeba, dole ta hakura ta kyaleshi. part din daddy ta zarce, nan suka hadu sukaita hira dasu faruq cikin nishadi, daddy da Aunty nabasu labarin abunda yafaru a jos. sunyi farin ciki sosai dajin yayansu yahadu da mahaifiyarsa. Amma fa zasuyi missing yayansu sosai…………✍️
Kuyi manage da wannan, muhadu gobe idan meduka yakaimu
By
zeey kumurya
ABINDA KASHUKA….
5️⃣1️⃣
Bismillahirrahmanirrahim
………..Mommy bata tashi duba result din da Dr, ta kawo mataba se bayan magriba. wani irin zabura tayi ta mike tsaye daga zaunen datake lokacin da taga abunda ke rubuce a jikin takardar. gani tayi kamar idontane benuna mata daidaiba, dakinta ta nufa da sauri ta dauki glass dinta ta saka sannan ta kara duba takardar abunda tagani da farko dai shita kara gani, da sauri ta fito falo hartana tuntube ta dauki wayarta tayi Dialing number doctor, ringing uku Dr, ta daga da sallamarta. batare da mommy ta amsa mataba tace: “Dr, Rahila yanaga wani result daban gane masaba, kodai bana suhailat din bane?” Cikin girmamawa Dr, tace. “Hajiya shine mana, natane” mommy na haki tace, “to ai bangane meke damunnatabane kimun bayani yanda zangane” numfashi Dr, taja tace: “Hajiya am sorry to say suhailat na dauke da ciki na tsawon sati shid……” “What” mommy ta katseta cikin karaji tare da yarda takardar hannunta. “Dr, kinsan mekike fadamun kuwa, suhailat din tawace take da ciki?” “Yes mah” abinda Rahila kawai tace mata kenan dan ta san duk bayanin dazatayiwa mommy a yanzu baza ta taɓa fuskantartaba.
batare da mommy ta kashe wayarba ta cillar da ita akan kujera tanufi dakin suhailat da saurinta. suhailat tana kwance tana tunanin Mustapha wanda kewarsa ta cika mata zuciya ta hanata sukuni. turo kofar dakin da mommy tayi da karfi yasata tashi zaune a firgice, gabantane yayanke yafadi ganin yanayin mommy’n. cikin tsananin bacin rai mommy tafara magana, “suhailat! nizaki kunyata, ki tozartani a idon duniya, ubanwa ya miki ciki?” Rasssss gaban suhailat yayanke yafadi cikin rawar murya tace. “Mo..mo..mmy cik..ciki kuma?” wani mugun kallo mommy’n ta watsa mata sannan tace. “Rahila zata miki karya ne, kuma yanayin ciwonkima kadai ya isa ya zama shaidar kina da shigar ciki, kifadamun ubanda ya miki ciki kafin na illataki yanzunnan” runtse ido suhailat tayi cikin tsananin tashin hankali, wata mahaukaciyar bugawa kirjinta yashiga yi. “Nashiga uku, yanzu idan yaya naji labarin cewa nayi ciki ze aureni kuwa?” ta fadi haka hawaye na zubo mata. cikin tsawa mommy tace. “Ina tambayarki uban da ya miki ciki, keta wani banzama can kike ko?” cikin kuka suhailat tace. “Kamal ne” “kamal” mommy ta maimaita cikin tsananin mamaki. jijjiga kai kawai mommy takeyi kafin tayi kwafa ta fice daga dakin. kuka sosai suhailat ta fashe dashi, ita zancen ciki betada mata hankaliba kamar yadda take tunanin rasa Mustapha, domin idan har yaji wannan labarin tasan maganar auransu ta rushe, danyasha fada mata yatsani zina kuma yatsani mazinaci!……….