Uncategorized

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE HAUSA NOVEL

mommy tana zaune a falo ta rafka tagumi abun duniya duk ya isheta, kullum seta Kira layin Sadik amma bata samunsa. gashi gobe da sassafe zasu tafi Niger ita da Binta, tana son neman shawarar Binta akan cikin dake jikin suhailat amma kuma batason tonawa kanta asiri dantasan binta bata da sirri, zuwa zatayi tayita yamadidi da ita a cikin kawayensu. shawara ta yanke kawai suna dawowa daga Nijar din zata kai suhailat a zubar mata da cikin, tunda Binta tace baza su wuce sati daya ba zasu dawo. da wannan tunanin taji zuciyarta ta dan mata sanyi akan damuwar datake ciki……….

kusan raba dare su Aunty sukayi suna shan hirarsu cikin nishadi, kokadan su haidar basuyi zancen mommy ba. se Aunty cema tace musu yakamata zuwa yanzu ace sunnemeta sunji halin datake ciki, dan kome mommy ta aikata mahaifiyarsuce matsayinta baze taba canzuwa a gurinsuba. sukace mata da safe insha Allah, zasu kirata……..

JOS

Sallar isha’i ce ta ta tashemu, bayan an idar muka dawo aka cigaba da hira. se kusan karfe biyu na dare sannan kowa ya nufi part dinsa, ashe part din da muke zaune na ammi ne. falo ne da dakuna uku, kowanne da toilet a ciki. Dakinta ammi tace naje na kwanta a kan gado. shikuma Mustapha ta bude masa wani dakin, da kanta ta share masa ta gogeshi tass, sannan ta sakamasa turaren wuta me dadin kamshi, a darennan seda ta wanke masa har toilet, duk da yana cewa tabarshi dare yayi da safe a gyara amma ammi tace a’a baze kwana A cikin dattiba. wanka nayi a toilet din ammi, kafin na fito ammi ta’ajiyemun wata rigar bacci sabuwa mara nauyi. rigar kawai nasaka kawai na kwanta saboda ciwon kan dake damuna, ga wani irin bacci danakeji. Mustapha yau yana cikin tsananin farin ciki, mara misaltuwa yanda ammi takeyin nan_nan dashi yafi komai yimasa dadi. dakin ya shiga da sallama bayan ammi tagama gyareshi, tsaf dashi dakin setashin kamshi kawai yakeyi. kayan jikinsa ya fara ragewa sannan ya shige toilet yayi wanka tare da dauro alwala. idanuwansa yau a bushe suke ko baccinma bayaji saboda farinciki, a gefe guda kuma zuciyarsa cike take da kewar yan’uwansa. dan yasan ammi bazata barshi yakoma Kano nan kusaba. tsayawa yayi a gaban madubin dakin yana tsane sumar kansa, tunanin abunda zesa a jikinsa yayi, dan gaskiya baze iya maida kayan daya cireba. Kwankwasa kofar dakin da’akayi ya katse masa tunaninsa. batare da yayi maganaba yaje ya bude kofar, ammi ce tsaye hannunta dauke da wata leda, dama yasan itace, murmushi yamata kamar yadda itama shine dauke akan fuskarta. “Sannu ammi, yakamata kije ki huta haka dare fa ya raba” yafada mata cikin sanyin murya. murmushi ta masa tace, “to shikenan Muhammad, baka bukatar wani abu?” Yace, “saidai abun sallah” mika masa ledar hannunta tayi tana fadin, “bari na dakko maka” karba yayi yajuya ya koma ciki. ledar ya bude ya duba, jallabiyace guda uku masu kyau, se tashin kamshi suke ammi ta feshesu da turare. murmushi yayi cikin tsananin jin kaunar ammi a ransa ya dauka guda daya ash colour yazira a jikinsa. ammi ce tashigo dakin da sallama ta ajiye masa daddumar a gefen gado. “Thank you real mom” murmushi ammi tayi me sauti dajin abunda yace. tana murmushin tace, “kana da fake mom ne?” murmushi yayi shima amma bebata amsaba, ya zauna a gefen ta tare da kwantar da kansa akan kafadarta. shikadai yasan irin dadin dayakeji idan ya rabi jikin ammi, yanajin dama karta tafi ta zauna su kwana tare, itama ammin hakanne anata bangaren bataso tabar gudan jininnata a halin yanzu shiyasa tun dazu takasa zuwa ta kwanta. tana shafa lallausar sumar kansa tana masa tambayoyi akan wasu abubuwa na rayuwarsa da suka shude, tun yana bata amsa har bacci ya daukeshi ajikinta, bacci me cike da nutsuwa daya manta rabon dayayi kamarsa. a hankali kamar wani jariri ammi ta lallaba ta kwantar dashi tare gyara masa kwanciya. kana kallon yanda yake baccin kasan cikin kwanciyar hankali da jindadi yake yinsa. Addu’a ta tofa masa, sannan tayi kissing goshinsa da kumatunta. seda ta rage masa hasken dakin sannan ta fice cikin shaukin dannata. sanda ta koma dakinta Maryam ta jima dayin bacci, wanka tayi itama sannan tafito tafara jero sallah domin nuna godiyarta ga Allah……

Har aka fara kiraye_kirayen sallah ammi bata runtsaba tana kan sallaya tana rokarwa danta addu’oin samun dacewa duniya da lahira. seda akayi kiran assalatu sannan ta mike. kan gado ta nufa inda Maryam take a kwance tanata sharar baccinta tafara tashinta a hankal tana kiran sunanta. A hankali Maryam ta bude idanta dake cike da bacci. “Diyata ki tashi lokacin sallah yayi” daga mata kai Maryam tayi tana kara lumshe ido kamar zata koma baccin. falo ammi tafita domin tatashi Mustapha shima, tana tura kofar dakin taga bayanan se motsin ruwa dataji a toilet, juyowa tayi takoma daki tunda yatashi. da kyar na iya tashi zaune, saboda baccin be isheniba. nina manta a inda nake, seda na watstsake na tuna, hakan yatabbatarmun da abunda yafaru jiya ba mafarki bane gaske ne, dan da kokwanto a raina na kwanta bacci musammanma aurenmu da heartbeat nafijin abun tamkar almara. toilet na shiga nadauro alwala, hijabi ammi tabani na zira na tada sallar. Bayan mun idar nadanyi lazimina nadubi ammi nace, “ina kwana ammi” da fara’a tace. “Lafiya kalau, ya kwanan bakunta?” “Lafiya kalau” na’amsa cikin jin kunyarta. hira ammi tashigamun tare mun tambayoyi akan rayuwata cikin hikima nikuma ina bata amsa. seda gari yafara haske sannan ta tashi ta fita. Tana fita nima na mike nashiga gyaran dakin, duk da babu wani datti a cikinsa se tashin kamshi dayake, bayan nagama na wanke toilet tass sannan nafita falo. Ammi bata falon kuma bata kitchen tanacan sunashan hira da danta. (Allah Sarki uwa mai dadi, Allah kajikan iyayenmu????????.) nariga nasaba da aiki idan na tashi da safe shiyasa duk randa banyiba se injini wani iri. kitchen din na shiga, dan babbane komai tsaf an killakeshi a mahallinsa, kayan da akaci abinci jiya da daddare su nahada na shiga wankewa, dan jiya hira bata bari anyi wanke_wankenba. Ina cikin yi ammi ta shigo ta sameni, kama baki tayi tare da fadin. “Diyata wayasaki aiki, na shiga dakima naga kin gyara shi fess, yanzu kuma shine kikazo kika kama wanke_wanke, aida kinbarshi nima zanyine kokuma zuhura idan tashigo setayi, dan ma umaimah batananne amma ita takeyi base kin wahalar da kanki ba.” murmushi nayi amma bance mata komaiba, danni banga abun wahalarwaba. da kyar ta barni na karasa amma da cewa tayi sedai na barshi ta karasa. Wajen karfe tara Aunty zuhura ta kawo mana lafiyayyen abinci na breakfast ammi da kanta ta zubamun ta dibarwa danta nasa takai masa daki, nidai har lokacin bamu hadu dashiba, inason inje ingaisheshi amma kuma nakasa.

Ammi abayoyi da jallabiyoyi take saidawa, kaninta yana turo mata daga Makkah kokuma intaje ta taho da wasu. Dilar datazo da ita a wannan zuwan datayi ita ta kunce, ta dibarwa Maryam abayoyi da yawa kafin a aiko mata da kayanta. shima Mustapha ta dibar masa jallabiyoyi. bayan nagama cin abinci nayi wanka na shirya cikin wata abaya me kyau a cikin wanda ammi ta kawomun, na yane kaina da mayafinta. ammi tace in fito muje mugaida mutanen gidan. se’alokacin muka hadu dashi, kaina a kasa nagaisheshi bayabo bafallasa ya amsamun. Part din mama muka fara zuwa mukagaisheta sannan part dinsu aunty zuhura, nasu matar da daddy yakadene na karshe. Bayan mundawo part din ammi, mukayi waya da Aunty tatambayeni babu matsalar komai nace mata babu, ta kara jaddadamun anjima zataje gidan gwaggo ta fada mata, nace dan Allah idan taje ta hadani da ita a waya. daga baya Aunty tabawa Aliya wayar mukasha hira tanatamun shakiyancinta da barkwancinta……….

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button