Uncategorized

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE HAUSA NOVEL

KANO

Aunty bayan sungama waya da Maryam ta kira layin suhailat, suhailat tana zaune abun duniya duk ya isheta, ga zaman kadaici dan har yanzu tananan da bakin girman kanta tafi ƙarfin tayi hira da matar da tazo tana yi mata aiki. gashi mommy ta hanata fita, ta hanata hawa online tana ganin kiransu faruq amma bazata iya dagawaba saboda tsoron masifar mommy. seyanzu kuma cikin yake damunta, ta matsu mommy ta dawo aje a zubar dashi gashi kullum cikin ciwo take babu lafiya. tanasoma ta sanar da kamal maganar cikin. a hankali ta kai hannu ta dakko wayarta jin tana vibrate alamar shigowar kira, ajiyar zuciya ta sauke me karfi ganin sunan Aunty yana yawo akan screen ɗin wayar, hannunta har rawa yakeyi wajen picking dantasan zata samu information akan Mustapha. jinta daga Aunty tace, “suhailat!” cikin mamaki. “Na’am Aunty” “meyake faruwa ne, in’ankiraki bakya dagawa, wayar Aunty Atika kuma bata shiga” rasa abun cewa suhailat tayi,tayiwa Aunty shiru kawai. “Bakya jinane suhailat” “inajinki Aunty, mommy’n batananne tayi tafiya Niger” “Niger kuma? To ke kina ina?” “Ina gidanta” “kekadai?” “Eh, sekuma mai aiki da maigadi” shiru Aunty tayi tana girmama rashin hankali irinna mommy, banda haka yazakayi tafiya me nisa irin haka, kabar yarinya budurwa ita kadai a gida” numfasawa Aunty tayi tace, “kituromun address din gidan zanzo nadaukeki anjima” “toh Aunty” suhailat ta amsa cikin jindadi zata koma gida kusa da masoyinta. kafin tatambayi Aunty ina mustapha Aunty ta kashe wayarta. Duban aliya dake danna waya Aunty tayi cikin bacin rai tace, “taso muje” kallon Aunty aliya tayi ganin yanda ta sauya lokacin ɗaya tace. “Lafiya Aunty? Meyafaru?” “Bansaniba kinsan bansan yawan tambaya ko?” shiru aliya tayi ta dakko hijabinta suka fita. batasha wahalaba wajen gane gidan gwaggo da kwatancen da Maryam ta mata, suna ɗan tattambaya har sukazo gidan. A kofar gidan gwaggo Aunty tayi parking, bayan sun fito daga motar taga gidan a kulle, Aunty bataji dadiba ganin gidan a rufe. Aranta tace, “sun rafka sabani kenan da gwaggo” har zata cewa aliya su koma gida kawai, se kuma tayi shawarar shiga makota kobatayi nisaba, dan ita yanzu idan tabar Kaduna batasan ranar dawowartaba. Gidan umma suka shiga. Umma tana daki tayi baki yan ganin lefe, saleemat kuma tana kitchen tana girki.

Da sallama suka shiga, saleemat dake kitchen ta amsa musu, tsayawa sukayi a tsakar gida bayan kamar 2 minutes saleemat ta fito. Da fara’a dauke akan fuskarta tace, “sannunku da zuwa” duk da bata wayesuba. “Ku shigo tana ciki” Aunty tace, ” barshi nanma yayi muna sauri ne” “to bari namata magana” saleemat ta fadi haka tana nufar dakin umma, sanar mata tayi tayi baƙi kuma sunce suna saurine. Biyo bayan saleemat umma tayi, da fara’a itama tayiwa su aunty sannu da zuwa, tare da kaisu falo. Bayan sun zauna sun gaisa umma tace. “Saidai banganekuba” murmushi Aunty tayi tace, “dama bakisanmu, nazo nanne makotanku naga gidan a kulle, shine nace bari nazo natambaya ko kwatancenne banganeba” umma tace, “gidanwa kuke nema” “gidan wata gwaggo wadda take rikon yarinya Maryam” umma na mamakin abunda yakawo wadannan kyawawan mutane, masu tattare da kamala gidan gwaggo, duk da sunsha hijabansu amma kallo ɗaya zakasamu kasan a daga gidan hutu suke, tace. “Eh, nanne kuwa bakuyi batan kaiba, saidai yanzu haka tana asibiti batada lafiya” “subhanallahi meyasameta” Aunty tatambaya cikin razani. atakaice umma ta musu bayani. Cikin jimantawa Aunty tace, “Allah Sarki, Allah yabata lafiya, yakiyaye gaba, sukuma wadanda sukayi Allah yatoni asirinsu” “Ameen” umma da aliya suka amsa a tare. “Tana wanne asibitin yanzu” Aunty ta tambaya. “Aminu Kano” daidai lokacin saleemat ta shigo dakin hannunta dauke da ruwa, godiya su Aunty suka mata, sannan suka kara gaisawa. Aunty ce tayiwa umma bayanin abunda ke tafe dasu atakaice. kafin umma tayi magana, saleemat cike da mamaki tace. “Maryam ditace take da aure yanzu?” “Ehh ita, kinsan iko na Ubangiji babu yadda baya canza al’amari, mu mutane muna namune Allah natasa, rabon aurennasune yakai Maryam aikatau gidan yaya” ganin yanda suka cika da mamaki, umma takara musu bayani sosai yanda zasu fuskanta karsu dauki abun da wata manufa. sun dan jima a gidan suna tattaunawa akan al’amarin seda sukayi sallar azahar sannan aunty suka tafi da saleemat asibiti dubo gwaggo. Lokacin dasukaje gwaggo tana duniyar bacci. wadda ke zaune a gurinta Aunty tayiwa bayaninsu kansu takuma tabbatar mata zasu dawo nan bada jimawaba harda Maryam din, seda Aunty ta cikasu da Alkhairi sannan suka musu sallama suka tafi. seda ta biya ta dauko suhailat bayan ta sallami matar dake zaune da ita, se bayan la’asar dai ta komo gidan daddy……..

JOS

Girke_girke mukayi, munsha aiki gaskiya. duk wannan hidimar akan yarinyar gidan dazata dawone wadda kullum senaji ammi da Aunty zuhura, da mama sunyi zancenta wai ita umaimah. daga jin yadda suke zancenta suna matukar ji da ita. Bayan mungama aikin nayi wanka na shirya cikin wata doguwar riga kalar dark pink, anmata adon baki da wasu fulawoyi a gaban rigar. faka gashin kaina dayasha gyara nayi ya sauka har gadon bayana, tattareshi nayi na cusa a cikin ribbom sannan na dakko wata bakar hula nasaka. dankunne fashion masu kyau nasaka tare da agogo da zobe. kwalli kawai nasaka a idona se white lipstick danasawa lips dina. humra me dadin kamshi na shafa a jikina, se wani turare na fesawa me sanyi da dadin kamshi. seya hadu yabada wani kamshi me dadin gaske. Kallon kaina nayi a mudubin dakin ammi, nikaina nasan nayi kyau, fatata tayi haske sosai jikina kuma ya murmure, tona samu kwanciyar hankalin zuciya tunda na mallaki heartbeat dina.

Maryam tana daki tana shiryawa umaimah ta dawo gidan, cike da farin ciki ahalin gidan suka tarbeta kowa na murna da farincikin dawowarta musamman ammi. Itama anata bangaren umaimah cike take da murnar dawowarta gida tayi missing dinsu sosai musammanma amminta, harsuka gama tarbe_tarbenta Maryam tana daki batamasan sunayiba. lokacin da Maryam ta gama shirinta ta shigo umaimah tana daki tana wanka. kusa da ammi naje na zauna bayan na musu sannu da gida. wayar Aunty na dauka nafarayin game, ita kuma suna hira da Aunty zuhura da mama. Bayan kamar 20 minutes umaimah ta fito daga dakinta karaf idonta yasauka akan Maryam, da dunbin mamaki take kallonta, danbatasan da zaman Maryam a gidanba. Aranta tace, “to wannan yarinyarfa, kodai daga Saudiyyan da Ammi taje tataho da ita?” a wani bangaren na zuciyarta kuwa kishi ne da kyashi ya turniketa na ganin kyawun Maryam, ita macece dabatasan taga anfita kyau, sekuma gashi yau taga wadda tafita komai da komai a cikin gidansu. hade rai tayi cike da hassada ta dauke kallonta daga kan maryam, kusa da mama taje ta zauna tana wani narke mata ajiki tana zuba mata shagwaba. se’alokacin Maryam tasan da zuwanta falon, dago kai tayi ta kalleta, mamakine yacikata ganinta katuwace amma take wannan sangartar, kallo daya Maryam ta mata ta dauke kanta tacigaba da game dinta. Ammi ce ta dubi Maryam tace, “ɗiyata ga autatah fa, danace miki tayi tafiya Abuja. kakaro fara’a Maryam tayi cikin sanyin muryarta tace, “sannu yakike” fuskarta babu fara’a tace. “Lafiya kalau” bankara cemata komaiba itama haka, a gani ɗaya dana mata naji ni sam batamunba, ita kam umaimah bakin ciki ne yakara turniketa dataji Muryar Maryam me sanyi da zaki, “yarinyar komai ta hada ga kyau ga zakin murya, salon yanda take maganama kawai abun burgewane” umaimah ta fadi haka a ranta cikin kyashi. Daidai lokacin Saddam da Mustapha suka shigo falon bayan sunyi sallama, kasancewar yau juma’a da wuri suke dawowa daga kasuwa. kamar ance ta kalli kofa idanunta ya sauka akan Mustapha. wani mayen kallo tabi mustapha’n dashi without control her self, kallonsa take tamkar zata lashesa…………✍️

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button