
JOS
Duk da part din dazamu zauna yana jikin na ammine,dan amminma tacemun anan ta zauna kafin mamansu Saddam ta rasu, seda ta rasu ta dawo inda take yanzu. Amma wlh jinake kamar wani garin za’akaini me nisa gashi zuciyata cike take da fargabar yadda zamannamu ze kasance, nasan dai ni ina matukar sonsa amma shi nasan baya sona. Idannatuna hakan se inji duk zuciyata ta karaya jikina yayi zanyi, musamman ma yanda yake nuna halin ko’in kula akaina. dauriya kawai nakeyi ina boye damuwata. Zuwa yanzu umaimah tasan waye mustapha a gurin ammi, kuma tasan Maryam matarsa ce, dan part din mama taje ta matsa mata da tambaya akan waye mustapha, seda mama tabata labari ta samu sa’ida. Tsana da haushin Maryam ne suka cika mata zuciya ganin ta rigata mallakar irin mijin datake mafarkin samu, amma dadinta daya dayakasance gida ɗaya zasu zauna, ita kuwa zatasan yanda zatayi tajanyo hankalinshi yadawo kanta, zatayi duk yanda zatayi ganin ta kwaceshi daga hannun wannan karamar yarinyar wato Maryam.
Bayan sallar magriba ammi tasani nayi wanka na shirya cikin wata hadaddiyar doguwar riga me kamar alkyabba yanayin jikinta. nayi kyau sosai acikinta, nafeshe jikina da daɗaɗan turaruka masu sanyi kamshi. Bayan nagama shiryawa ammi tamun faɗa akan zamantakewar aure, mama ma, tamun. nidai hawaye kawai nakeyi ina saurarensu.
Bayan sallar isha’i ammi ta kama hannuna ita da mama suka rakani har inda yake a matsayin dakina ta zaunar dani akan gado. nasha kuka sosai bayan sun tafi. Daga baya kuma na rarrashi kaina nadena kukan. A hankali na tashi nakarewa dakin kallo yayimun kyau sosai sai kamshin turaren wuta da sabon fenti yakeyi. kayana su ammi sun jeremun su a cikin cover, su turaruka da mayuka duk anjeremun akan mudubi, komaidai need abun gwanin ban sha’awa. Falo na fito shima yayi kyau sosai babu wani tarkace, yasha labulaye masu kyau. daga falo kitchen nanufa, shima yaji kaya komai na amfani akwaishi. dakina na koma bayan nagama kalle_kallennawa, dakinsane kawai banyi gigin shigaba. ina mamakin wai wannan gidanane da kayan cikinsa komai nawane, nida bantaba zaton zansami koda rabin wannan ba. Zama nayi a bakin gado nashiga sake_sake. Ƙarfe goma da yan mintuna ya shigo part dinnasu, hannunsa dauke da ledoji manya. Kitchen ya nufa ya ajiye kajin daya shigo dasu kamar yadda ammi tace yasiyo. Shima seda yagama karewa gidan kallo, shima gidan yamasa kyau sosai, kafin yashiga daki seda ya saita kayan kallo danshi mutum ne meson kallon news da kallon ball. Ina zaune tsuru naji shigowarshi ajiyar zuciya nasauke cikin jindadi,dandama a tsororace nake da zaman nikadai, nandaima da wutar NEPA ne. Dakinshi ya shiga ya ajiye sauran kayan dayashigo dasu, sabulayene da mayuka da turaruka. Nashi ya kwasa ya jera a gaban madubin dakin. sannan dauki sabulu da saban towel din daya shigo dasu ya nufi toilet. bayan kusan 30 minutes yafito yazira jallabiya yafashe jikinshi da turaruka ya kwanta. Lumshe idansa yayi yana tunanin wannan aure da daddy yamasa. shiyanzu besan yazeyi da yarinyar mutaneba, tunda bashi da lafiyar daze bata hakkinta na aure akansa, kodama yanada lafiyar baya tunanin waccan karamar yarinyar zata iya dashi, shifa yaraina Maryam a matsayin matarsa ganinta yake yar karamar yarinya, dandai baze iya bijirewa daddy bane da……. wayarsace ta katse masa tunaninsa ta hanyar yin vibrate. Ahankali ya bude idansa ya tashi ya dakkota daga kan madubi. MY UNCLE yagani yana yawo akan screen ɗin wayar. kanin ammi ne dayake saudiyya kullum sesunyi waya dashi, dagawa yayi sukasha hira har yaransa yabawa suka gaisa sannan sukayi sallama. Nasihar da daddy yamasa ranar da zasu koma kano itace ta dawo masa kwanyarsa tamkar yanzu yake masa ita. “Mustapha, karike yarinyarnan amana kaga marainiyace kuma bata da wani gata sena Allah, idan ka cutar da ita Allah baze barkaba. Kuma yazama dole kakula da cinta da shanta da kuma lafiyarta.” Mikewa yayi yaɗauki ledar daya shigo da ita, bisa umarnin da zuciyarsa ta basa akan yakamata yaje yaga lafiyarta kafin ya kwanta, tunda yanzu amanace ita a hannunsa, da wannan tunanin ya nufi dakinta. Maryam dataga zaman ya isheta gashi ko digon bacci a idonta, seta tashi dama da alwalarta ta shimfida sabuwar daddumarta ta tada sallah………….✍️
By
Zeey kumurya
5️⃣4️⃣
Bismillahirrahmanirrahim
………… Ahankali ya tura kofar dakin yajita a bude, bakinsa dauke da sallama ya shiga dakin. wata irin faduwar gabace ta ziyarceni duk da Sallah nake jin shigowartasa. kamshinsane yatabbatarmun da shine, gaba-daya jinayi na diririce, narasama menake karantowa a cikin sallar saboda tsabar fargaba. shiko mustapha ganin sallah Maryam take, seya ajiye ledar hannunsa ya juya ya fice. Ajiyar zuciya nasauke jin yafita na sallame sallar amma banko motsaba daga inda nake, duk da yafitan amma bandawo cikin nutsuwa taba.gani nake kamar ina juyawa zanganshi yadawo cikin dakin, kusan 16 minutes sannan na daure na tashi daga kan dardumar har lokacin daddadan kamshinsa bebar dakinba. hijabin jikina na cire na ajiye, leda nagani dabansan da itaba a dakin. cikin mamaki na dakkota nafara fito da kayan dake ciki, sabulayen wanka ne dana wanki,se MacLean da sabbin burush guda biyu da mayukan shafawa harda sosan wanka me kyau acikin ledarsa araina nace, “gaskiya wannan ya iya siyayya, komai dayasan zan bukata seda yasiyo.” mayar da kayan nayi cikin ledar bayan na dauki abunda zan bukata a yanzu na ajiye a gefen gado. Toilet na fada nayi wanka, ina fitowa na zira rigar bacci nafada kan gado dan wani irin bacci naji inaji lokaci daya……
Washegari, bayan nayi sallar asuba ban koma bacciba, Alqur’ani me girma na dakko na karanta izifi uku nayi narufe na ajiye. Addu’a nayi sosai akan rayuwata, nayi mana addu’a sosai akan aurennan namu da hearbeat senaji duk wani tsoro da fargaba ya kaumun daga zuciya. Ƙarfe bakwai da yan mintuna nafito daga dakina domin na gyara gidan. babu wani datti yananan fess dinsa. kujerun na karkade nashare dan dattin dabaza’arasaba a falon, nagoge dining da tv. Kitchen na shiga shima babu wani abun datti a cikinsa, leda na hango akan karamar freezer dake kitchen din, da dan mamaki nakarasa nahau dubawa, dan jiya dana shigo babu da ita. kaza nagani a ciki har uku, se zuba kamshi takeyi. shiru nayi cikin karayar zuci, araina nace. “Kazar amarci dakowanne ango yake siyowa matarsa ya lallabata yabata taci, amma ni nawa angon saboda baya sona seyazo yadireta a kitchen” kwallace ta cikamun idona, maida ita nayi yanda naganta nafito daga kitchen din zuciyata namun kuna. “Yaushe bawan Allah’n nan zesoni? kamar yadda aliya tace, anya kuwa zanga wannan ranar ba yaudarar kaina nakeba kuwa? abun da kamar wuya” natambayi kaina hawaye na zubomun daga idona. Knocking din kofar falon akayi yasani saurin goge hawayennawa, kofar na nufa na bude batare da tambayar wayeba. Umaimah ce tsaye hannunta dauke da basket da kayan breakfast a ciki, ammi ce dazata kawo da kanta umaimah tace tabata takai musu, dan a zatonta mustapha ne ze bude kofar amma setaga Maryam. bata rai tayi sosai ta wani hade fuska, ko sannun da Maryam ta mata bata amsaba. matsa mata nayi ta wuce ciki nima nakoma na zauna akan kujera bankara kallon koda inda takeba harta fice danna lura yar rainin hankalice. tana fita na tashi na kulle kofar, inajin yunwa gaskiya dan tun jiya da rana rabona da abinci. Flates na dakko da cups nadibi abinda zanci nanufi dakina, Allah sarki ammi nasan wannan duk aikintane. koda nagamaci banfitoba wanka nayi na kwanta ina tunanin yanda zamanmu zecigaba dashi. seda goma ta wuce nafito Falour’n dauke da kwanukan danayi amfani dasu, nasan zuwa yanzu kam yafita. kan dinning na kalla naga shima kwanukan dayayi amfani dasu a gurin, da alamama bejima da fitaba danga kamshin turarensanan a falon. Tattara kwanukan nayi duka nakai kitchen na wanke na kara kimtsa wasu abubuwan. sannan naje na gaida ammi cike da jin kunyarta, a tunaninta mustapha yananan befitaba, muna gama gaisawa tace inkoma gurin mijina. Ƙarfe 12 na rana aka kawo mana wuta, dama nagaji da zama ba abunyi sena kunna kallo….. Yaran makota sun shigomun yau sosai harda yanmata kamar ni, dan su mama duk sun sanar amarya tatare. naji dadi kuwa sosai dama kewa ta isheni har bayan la’asar sannan suka tafi. kara gyara gidan nayi naturareshi da turaren wuta me dadi, Aunty zuhurace ta aikomun dashi da yawa a cikin bokiti. se kusan magriba mustapha yadawo gidan, ina zaune a falo ya shigo. Lumshe idonsa yayi saboda wani ni’imtaccen kamshi dayaji falon yanayi. shikam yanason kamshi a rayuwarsa yana kuma san tsafta. A hankali ya kalli inda yaji muryatarta data amsa masa sallamar dayayi, danbe zaci tana falonba. becemun komaiba yawuce dakinshi, ni kuma na bishi da kallo zuciyata cike da shaukinsa. Lumshe idona nayi nafada duniyar tunani, har aka kira sallar magriba inanan zaune inda yabarni. da kyar na yunkura na shiga daki nayi alwala danyin sallah. Da daddare yaya sadam yazo har part dinmu yace inshirya da safe zamuje amun passport za’akai makarantar dazanyi NECO. Wayyo daɗi kamar ze kasheni dan Murna dan da har na fiddarai da karatun……