Uncategorized

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE HAUSA NOVEL

Nace zanmuku update around 9,Allah beyiba wani uzurin yakara tsaidani. Am sorry again se yanzu nasamu dama na muku, amma ko editing babu

By
zeey kumurya
5️⃣5️⃣

Bismillahirrahmanirrahim

………..Wata irin bugawa zuciyata tayi da ƙarfi lokacin dana jini ajikinsa batare da zato ko tsammaninaba. shiko mustapha lumshe idonsa yayi cikin wani irin yanayi dabeyi zatoba, zuciyarsace ta hau bugawa da sauri_sauri. kara firgicewa nayi ganin yana gyaramun kwanciyata akirjinshi, gaba-daya na tsorata jikina ya kama rawa saboda bansan mezemunba. runtse idona nayi kawai ina kara shigewa jikinsa batare danasaniba, ajiyar zuciya nahau saukewa ahankali cikin wani irin yanayi, luf nayi ajikinsa ina shaƙar daddaɗan kamshinsa me saukarmun da nutsuwa,wani dumin ni’ima naji yana ratsa jikina, har wani bacci_ bacci me daɗi naji yana fizgata. shiko mustapha kasa aiwatar da komai yayi, wata irin kasalace take baibaye dukkan gaban jikinsa. A hankali ya buɗe lumshashshun idanunsa, cikin matukar dauriya da yanayin daya tsinci kanshi yakai hannunsa dake ɗan rawa yacire ɗankwalin kan Maryam, jedar kitson data tusa a cikin ɗankwalin ta zubo a gadon bayanta. kansa yadora akannata yana shaƙar kamshin kanta daya matuƙar yimasa daɗi, batare dayasan yayi hakanba. A haka yakama jelar kitson ƙeya guda ɗaya yafara warwareshi da kibiya, be iya tsifarba hakan yasa se cisgar mata gashi yake, amma Maryam ko zafi daya batajiba batamasan meyakeba tatafi duniyar shauki, sekara manne masa take tamkar wata mage, da alama ta manta ajikin wanda take. Yayi 12 minutes kafin yagama tsefe kitson guda ɗaya jal, amma dakyar yakarasa saboda baƙon yanayin dayake kara dabaibayeshi mara misaltuwa. A hankali ya ajiye kibiyar akan kujera Zuciyarshi cike da tsananin mamakin ganin tabbas gashintane bata masa karyaba. Yaga mata masu gashi da yawa amma be taɓa ganin kamar na Maryam akan Hausa Fulaninmuba, yasan aunty da mommy da suhailat suna da gashi sosai amma be kama kafar na Maryam ba, kallon kannata kawai yake cike da shauki, shi mutum ne meson yaga gashi akan mace, yana kaunar yaga yana shafashi. A hankali yakai hannunsa yana shafa kitsonnata tamkar me mata tafiyar tsutsa. Wata nannauyar ajiyar zuciya Maryam ta sauke tana kara gyara kwanciyarta ajikinsa. Da sauri ya dago da fuskarta daga kirjinsa yabi fuskarta kallo. Bacci takeyi hankalinta kwance, numfashin datake saukewa a hankali ne, yasa yagane bacci takeyi. Kurawa kyakkyawar fuskarta ido yayi zuciyarsa na bugawa. Cikakkiyar girarta da kwantaccen gashin dake goshinta zuwa gefen kunnenta gami da zara_zaran eyelashes dinta, yasa isa shaida idan ka kalleta kasan zatayi gashi. Kara maida kanta tayi cikin jikinshi tana kara kankameshi. Wata irin kasalace take kara baibayeshi, tsigar jikinsa gaba-daya tatashi. Lumshe idonsa yayi cikin rashin sanin abunyi, yanaji ana kwada kiran Sallah amma yakasa motsa koda danyatsansane. “To meyake shirin faruwa dashi haka ne?” Yatambayi kansa, betaba tsintar kansa a irin wannan yanayinba seyau, yanayine me wuyar fassaruwa ga zuciyarsa dake ta aikin bugawa, kansane yaji yasara masa. tsawon 5 minutes suna zaune a haka, ita Maryam baccinta takeyi cikin kwanciyar hankali, baccin da bata masan sanda yadauketaba. Dakyar ya iya bude idanunsa dasuka masa matukar nauyi, tattaro duk wata dauriyarsa yayi yafara ƙoƙarin rabata da jikinsa a hankali dankarta tashi. Daukarta yayi cak kamar wata baby ya kwantar da ita akan doguwar kujera. A hankali yake kokarin zare hannunsa daga jikinta cikin lallabawa dan karta farka. Mikewa yayi ya kalleta na wasu sakanni, sannan ya fara tafiya yanufi dakinshi jikinshi a matukar sanyaye. kafin yayi alwala har an tada sallah anyi raka’a ɗaya. dakyar yake iya ɗaga kafafunshi yake tafiya. duk da yayi alwala amma yanayin dayakeji bebarshiba, bayan kasala har wani yammmm…yakeji ajikinsa,Tsigar jikinsa har lokacin batabar tashi ba. a haka dai yadaure yaje masallacin yayi Sallah. koda yadawo gidan part din ammi yawuce kamar yadda yasaba kullum, babu kowa a parlon dakinta yashiga bakinsa dauke da sallama. Ammi tana zaune akan darduma tana lazimi ya shigo. zama yayi a gefen gado tare da dafe kansa dayake cigaba da sara masa. seda ammi ta shafa sannan ta juyo ta dubesa tare da fadin, “NOOR an dawo?” Dago kansa yayi cikin dauriya da abunda yakeji yace. “Ehh ammi ya gida” bata amsa masaba se kafeshi datayi da ido kafin tace. “NOOR lafiya kake kuwa naganka wani iri?” “Lafiya kalau ammi” yabata amsa yana zaro wayarsa daga aljihunsa dan karta kuma masa wata tambayar. kallonsa ammi take sosai kamar meson tagano wani abu a tattare dashi, taga kamar wani abu nadamunsa amma tasan halinsa tunda yace mata babu komai koma da akwai ɗin ba fada mata zeyiba. Nisawa tayi tace, “Maryam ta faɗa maka gobe zamu kano ko?” Da sauri yadago yadubi ammi so surprise yace, “Kano kuma?” ammi tace “ehh, zamuje dubo gwaggon tane bata da lafiya”…ammi tabashi labarin abunda yasamu gwaggo. Cikin tausayawa yace, “Ayya, Allah yabata lafiya” “Ameen” “amma a goben zaku dawo ko?” “A’a sedai jibi” “ok, Allah yakaimu lafiya.” wata hirar suka cigaba duk da shi daurewa kawai yake dan kar ammi tagane wani abu, amma shikadai yasan meyakeji ajikinsa da zuciyarsa……

Maryam bayan fitarsa ba jimawa ta fara mutsu_mutsu tana rarumar jikin kujera kozataji shi, gaba-daya baccin yadena mata daɗi se juyi take. A hankali ta buɗe idanta tunda baccin yagagara daɗi. da sauri ta tashi zaune kamar wadda aka tsikara. sosai mamaki yakamata “bacci da magarubarnan?” Tatambayi kanta, tana dafe kanta. tunaninma ya akai tayi baccin tahauyi. “Ajikinshi bacci yadaukeni kenan kokuma ya?” Maryam ta fadi haka a fili tana waro duka idonta waje. shafa kanta tayi taji babu dan kwali. mikewa tsaye tayi ta dauki dankwalinta da kibiyar dake kan kujera ta nufi dakinta zuciyarta cike da tunanika kala_kala, abunda yafi daure mata kai baccin datayi batasan sanda yadauketaba…. Bayan ta idar da sallar magriba ta fara haɗa kayan dazasuyi tafiya gobe, ita da ammi zata bartama kwana biyu zatayi a Kano, tanason ganin Aunty ma, amma Aunty tace mata bazata samu zuwaba kafin azumi kamar yadda tace, abubuwa sun mata yawa sedai cikin sallah insha Allahu zatazo….. Maryam anayin sallar isha’i tadebi abincinta tayi daki bayan ta jera masa nasa akan dinning, da wuri takeso tayi bacci danta matsu gobe tayi, kuma batason ta kara hada ido dashi danwata irin kunyarsace taji ta lullubeta. Mustapha kam daren yau gaba-daya bayajin daɗin jikinshi, kamshin jikin Maryam dana kantane kawai yake masa gizo a hanci, koda ya kwanta bacci daya rufe idansa kyakkyawar fuskarta kawai yake hangowa lokacin datana bacci ajikinshi, da kyar yasamu bacci yadaukeshi……..

KADUNA

Aunty tun ranar data dakko suhailat ta fuskanci wani abu a game da yanayin ciwon suhailat ɗin domin bata iyacin komai, sedai taitashan drinks da kayan zaki su take wuni tana sha, idan kuwa Aunty ta matsa mata taci wani abun, to seta amayar dashi, gashi Aunty tayi_tayi suje asibiti a dubata taki yarda ita wai lafiyarta kalau ta warke. Aunty ta rabu da ita ta kyaleta, saidai duk abunda take Aunty na hanhalce da ita ta saka mata ido ne, kawai tana kallon gudun ruwanta…….

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button