Uncategorized

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE HAUSA NOVEL

Idona a runtse harya saukeni, sosai kirjina ke dukan uku_uku cikin wani irin yanayi. gabadaya salon nasa yadauremun jijiyoyin jiki tamau, jinin jikina kuwa babu tantama ya daskare. Kaina naƙasa nakasa kallon koda inuwarsace har ya buɗe Kofar part dinnamu ya shige abunsa beko ƙara kallon inda nakeba. jan kafata dakyar nima nayi nabi bayansa. harnayi wanka nayi Sallah bandawo daidaiba, kwanciya nayi akan gado na lumshe idona ina tuno ni a jikinsa, wani murmushi ne na farinciki ya subcemun, kankame filo nayi a kirjina inajin dama shine.(????azumi ne dai mero) bansan sanda bacci me daɗi yadaukeniba………

Ammi tana kwance akan gadonta tana bacci, sama_sama takejin wayarta na ringing. A hankali tatashi zaune, bacci fal idonta ta janyo wayar ta daga ta kara a kunnenta. “Assalamu alaikum” daga ɗaya ɓangaren aka faɗa. ‘wa’alaikassalam” ammi ta amsa sallamar tana tunanin kamar tasan Muryar me maganar. gaisawa sukayi duk da ammi bata gane shiba. Daddy ganin bata gane shiba yace, “kina magana da yaronki mainasara” murmushi ammi tayi tace, “yaro kodai ubangida” cikin zolaya daddy yace, “yaro dai, tunda ke baki nemeniba nina nemeki, kodan yanzu ɗanki yazo hannunkine shiyasa kika dena neman mu” murmushi me sauti ammi tayi tace, “to ayi hakuri na tuba kaina bisa wuyana zandinga nemanka akai_akai daga yanzu insha Allah” “dakuwa kin kyauta, dan zanso hakan sosai” batare da tunanin wani abu akan maganar daddy ba ammi tace. “yame jiki kuwa” “jiki da sauki Alhamdulillah, tunda yanzu yadawo hayyacinsa yana gane abubuwa.” “Masha Allah, Allah Ubangiji ya ƙara sauki yasa kaffarane” “ameen ya Allah” daddy yatambayi lafiyar su Maryam da kowa da kowa, ammi tace duk suna lafiya. Numfasawa daddy yayi yace. “Hajiya Maryam nakirakine muyi magana akan dukiyar Mustapha dake hannuna, tun kwanaki nakeson muyi maganar ciwon Sadiq yatsaidani amma yanzu tunda komai yadaidaita semusan yanda za’ayi.” ammi tace. “Yallabai, aini bani da hurumi akan wannan maganar, Muhammad ai ɗankane kuma dukiyarsa takace, a ganina babu wani bukatar yaza’ayi da dukiya, kacigaba da juyata kawai agurinka, amma ni bazan karbi komaiba, kuma Muhammad haka” cike da mamakin ammi daddy yace. “Hakane Hajiya, mustapha ɗanane amma yazama dole nabashi hakkinsa dake wajena, tunda yanzu shima yakai munzalin daze iya juya ta” “to shikenan kazamu lokaci kazo semu tattauna akan hakan.” godiya daddy yamata sukayi sallama.

Se kusan la’asar natashi daga bacci. Fuskata na wanke na kuskure bakina sannan na nufi part din ammi, dan anan muke aikin azumi na duka gidan. A baranda natarar da ammi da mama A’isha suna ferayar dankali. Mama kuma tana gefe tana wankin waken kosai. Bayan mun gaisa ammi ta dubeni tace, “ɗiyata har kin tashin kenan, dazu NOOR yashigo ai, yacemun harkun dawo amma kin kwanta, ya exam din.?” Kaina na ƙasa nace, “Alhamdulillah” “Masha Allah, Allah yabada sa’a” gabadaya muka amsa da “ameen” ciki na shige na nufi kitchen. Aunty zuhura ce, kadai a kitchen din tana girki. “Aunty zuhura sannu da aiki” nafada bayan na shiga kitchen din. “Yawwa Mamana, kindawo kenan” “nadawo Aunty zuhura tun kafin 1.” “Sannunki ya jarrabawar?” “Lafiya kalau, Aunty zuhura. Bari nazo natayaki aikin” Aunty zuhura na murmushi tace, “dakinyi zamankima danna kusa karasawa miyace kawai tayi saura, kar a wahalar da babynmu” murmushi kawai nayi bance komaiba, nafara tayata aikin. Zuhura dama tana sane tayiwa Maryam wannan zancen, danta fuskanci har yanzu babu abunda yashiga tsakaninsu da mustapha, danta fuskanci yanada shegen miskilanci, amma zata taimakawa Maryam da dabaru ta yanda zataja hankalin mustapha zuwa gareta, Wannan miskilancinnasa duk se tayi maganinsa. fita tayi tacewa Maryam tana zuwa, bayan kamar minti goma ta dawo da waya kare a kunnenta tana faɗin. “Bangane tunda kukayi aure haryanzu babu wani abu daya tsakaninkuba.” shiru tayi alamar tana sauraren wanda suke maganar na tsawon 50 seconds sannan tace. “Haba salma kekamar ba wayayyiyaba ace haryanzu kinkasa ɗaukar hankalin Tahir zuwa gareki yana mijinki kuma kuna gida ɗaya, haba salma karki bani kunya mana.” Shiru ta karayi na wasu sakanni kafin tace, “wannan duk ba matsala bane, salma dan hadaku aure akayi, ai baza’ace shikenan bazakuyi soyayya kuyi rayuwar aure kamar kowaba, kuma koda baya sonki tunda ke kina sonshi sekiyi kokari kibi duk hanyoyin dazaki jawo hankalinsa zuwa gareki, kefa macece” Takarayin shiru sannan tacigaba da fadin. “Akwai hanyoyi da dama salma dazakibi kijawo hankalin mijinki zuwa gareki, batare daya gane danshi kikeba kokuma kina son shine, shifa namiji tamkar jaririne agurin matarsa duk ta yadda kikabi dashi haka ze tashi yana miki, yanzu idan kika zauna kuncigaba da rayuwa a haka kefa zaki cutu, danshi idan yana da bukatar mace aurensa ze kara, kuma yadinga bawa matarsa kulawa kekuma kina gefe ko oho, gwarama tun wuri kifarka daga nannauyar baccin dakike kibawa makiya kunya, kijawo hankalin mijinki zuwa gareki tun kafin dare ya miki kizo kina cizon yatsa” ta karayin shiru tana saurare sannan tace, “yawwa kawata yanzu naji batu, bari na baki wasu shawarwari danasan insha Allahu zasu taimaka miki. idan yana zaune a falo irin da daddarennan yana kallo, kekuma ki tsalo wankanki cikin kananun kaya, ki baza kamshi a kowanne lungu da sako na jikinki me daɗin gaske, wanda dole idan ya shaka seya dago ya kalleki, karkiji kunya ko tsoron komai, kifito falon abinki kina tafiya ta daukar hankali, kiyi kamar baki ganshiba kishige kitchen kamar zaki dauko abune, in kinfito zaki koma kice masa sannu, kiyi kamar se lokacin kika ganshi kikoma daki abinki, kiyi kamar kwana uku kinayin haka, seki dena fitowar. Nina faɗa miki da gayyama zena zaman falon danyaga fitowarki, duk randa baki fitoba kuwa ki leko ta window zaki gansa yana kallon kofar dakin ki hankalinsama gabadaya baya kan kallon, to yanaso kifito ya shaki kamshi yaga kuma abubuwan harka na juyawa. Sannan kuma kisan dabarun dazaki na yi jikinki na haɗuwa da nashi” Shiru ta ƙara yi, sannan tace. “Kai salma na rasa irinki, yanzu bakisan yanda zakiyi jikinku ya haɗu ba, to bari na baki misali ɗaya. Bayan kinyi abinda nace miki kamar na sati ɗaya ko biyu. wataran bayan kinfito falon, sekinzo kusa dashi, seki fadi da gangan ki zube a kasa, zaki ga yataso da saurinsa yana tambayarki meyafaru duk yabi ya rude, to yana tsoron kar ko kinji ciwo sosai yadena ganin gilmawarki. kekuma seki langwabe harda hawayenki ki rirrikeshi kina nuna masa kin firgitane tare da zuba masa shagwaba, duk miskilancinsa ranar zakisha mamaki nina faɗa miki, kamshin dakike zubawa kadai ya isa ya hautsina masa lissafi.” Shiru ta kumayi daga can tayi dariya tace, “yawwa kawata kinfara hawa layi haka nakeso, ki dauke masa hankalin daga kan yanmata masu farautar mazajen wasu, dama gaki da kyanki da jiki na daukar hankali…..”

Shawarwari da dabaru masu yawa zuhura ta lissafo sannan tayi sallama ta aje wayar. kallon Maryam tayi wadda tayi tsit tana sauraren zuhura da dukkan hankalinta tace. “Sannu mamana, na barki kinata aiki ke kadai ko, wlh wata kawatace ta kirani akan matsalar ta ita da mijinta” murmushin ƙarfin hali na kakaro nace, “bakomai Aunty zuhura ai babu ma wani aikin” murmushi kawai Aunty zuhura tayi. suna aikin tana satar kallon Maryam, yanda tayi tsumu alamun tana tunanin wani abu, tasan abubuwan data faɗane Maryam take tunani akai, dama kuma duk wayar datayi pretending ne kawai, dan Maryam din taji tayi, ai kuwa tayi nasara danta saka Maryam a zullumi da tunani…

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button