
Yau Biyar ga sallah tun asubar fari mommy ta sauka a garin Kano. Tun kafin azumi suka baro garin NIGER, Binta ta dawo Nigeria yayin da mommy ta wuce ƙasar da suka zauna acan baya tayi azuminta acan, a cewarta bazata iya azumi a naija ba rana tayi yawa. se washegarin sallah ta dawo Nigeria ta sauka a garin Abuja gidan wata kawarta matar wani ɗan majalisa, seyau kuma tayi asubanci ta biyo jirgin ƙarfe 6 na safe zuwa Kano, batason asan da dawowarta harta se ta gama gudanar da kudirinta akan daddy da mustapha harma da maryam. shiyasa ta dako sammako dan karma wani daya santa ya ganta. Tana sauka a filin jirgi ta saki wani murmushin da ita kaɗai tasan ma’anarsa, zuciyarta fari ƙal tanajin kamar burinta ya gama cika. Driver’n ta data kira tun daren jiya ta sanar mata zuwannata yana gurin yana jiranta. Jan trolly dinta tayi ta nufi inda ta hango motarsa. dasauri ya fito daga mota shima ya karbi trolly’n hannunta yana jera mata sannu da zuwa cikin girmamawa. a ƙasaice ta amsa masa. Buɗe mata gidan baya yayi ta shiga, shima yazagaya ya shiga driver seat bayan yasaka trolly’n nata a But. gidanta dake lamido cresent tace yakaita. Cikin mintuna 20 suka karasa gidan kasancewar hanyar babu go slow tunda safiyace. Har cikin falo driver’n yakaimata kayanta. mommy dake tsaye tana karewa falon kallon cikin tsananin mamaki, ko sauraren sallamar dayake mata batayiba, ganin falon duk yayi kura. dakin da suhailat ta zauna ta nufa tana kwada mata kira, amma taji shiru. mamakine ya ƙara kamata ta shiga dube gidan tana kwala kiran sunan suhailat ɗin amma taji tsit. hankalintane ya fara tashi, cikin sauri ta fito ta nufi dakin megadi ta kwala masa kira. megadi dake ƙoƙarin komawa baccin da zuwan mommy ya katse masa ya fito da sauri daga dakinsa. A rude mommy tace, “inuwa ina yarinyar dana bari a gidannan?” Megadi na kallon mummy da mamaki yace, “wacce fa?” “Yarinyata dai dana bari budurwa, kafin na tafi nace maka karka barta ta fita ko da leke” megadi yace. “To to, nagane. Ai wata matace tazo suka tatafi da ita.” Agigice mummy tace, “what? wacce matar?” Megadi daya fara ɗan firgita yace. “Bansantaba Hajiya” cikin tsawa mommy tace, “bakasantaba shine kabari tafitarmun da yarinya, saboda bakasan me kakeba, bakasan aikinkaba.” Masifa mommy ta masa sosai kamar zata cinyeshi ɗanye. shikuma yanata aikin bata hakuri, bata saurareshiba ta wuce ciki fuuu, bayan ta tabbatar masa da duk abunda yasamu yarinyarta seta hukuntashi. tana shiga falon ta buɗe handbag dinta ta dakko wayarta jikinta na tsuma tayi dialing number suhailat. Suhailat na kwance tana baccinta wayarta ta fara vibrate, har Kiran ya katse bata dagaba. seda mommy ta mata 3 missed call sannan tatashi dakyar ta janyo wayar tana jan tsakin katse mata baccinta da akayi. batare data duba wake kirannataba ta ɗaga wayar tare da karawa a kunnenta. “Suhailat!” Mommy ta faɗa da ƙarfi. Zunbur suhailat ta tashi zaune tare da cire wayar daga kunnenta ta duba wanda yakirata. Sweet mom ta gani. “Suhailat bakya jinane” mommy ta ƙara faɗa. Cikin damuwa suhailat tace. “Mom, se yau kika tuna dani?” Cikin faɗa mommy tace, “niba wannanba suhailat, wacce matar ce tazo ta daukeki har gidana?” “Aunty ce” ta bata amsa. “What!? Aunty, wacce Aunty’n?” Mommy ta tambayeta cikin karaji. “Aunty’n Kaduna mana” “kina nufin saudart” “eh ita” mommy tana kankance ido cikin bala’i kamar suhailat na ganinta tace. “Waya faɗa mata inda kike?” Suhailat data fara gajiyawa da faɗan mommy tace. “Nina faɗa mata” mommy tace, “akan me to, banayi warning dinkiba kafin na tafi, kuma ina matar dana barku tare a gidan?” Suhailat tace, “kirana tayi a waya shine na faɗa mata, ita kuma matar aranar da muka taho ta sallameta tatafi.” masifa mommy ta shiga yiwa suhailat kamar taɓabbiya akan bin Aunty datayi, a karshe tace mata kuma ta shirya kayanta zata turo a ɗauketa a yau dinnan, suhailat ta amsa mata sannan mommy ta kashe wayar. Babu ɓata lokaci suhailat tatashi ta hau haɗa kayanta, dama zaman gidan auntinnan duk a takure take jinta. Aliya bata dakin tana kitchen suna haɗa breakfast dan yau zasuje Jos sukaiwa su maryam ziyara. Aunty ce tashigo ɗakin ɗan ganin ko suhailat tatashi. ganin yanda suhailat ɗin take haɗa kayan se Aunty ta tsaya turus tana kallonta kawai. can ta nisa tace, “kayan me kike haɗawa haka suhailat, bafa dadewa zamuyi a Jos dinba, jibi insha Allahu zamu dawo” suhailat tana haɗa kayan yari dinta tace, “Aunty nifa Kano zankoma” aunty na mata wani kallo tace. “Akanme?” Shiru suhailat tayi dan batasan me zata cewa Aunty ba. Babu wasa a fuskar Aunty kokaɗan tace, “ki hada kayan da zaki bukata na 2 days kamar yadda nace miki jiya, ki kuma shirya, karki bata mana lokacin” tana gama fadar haka ta juya ta fice. suhailat tabi bayanta da kallo ranta babu daɗi. ta rasa wazatabi maganarsa mommy ko Aunty? zama tayi kawai a bakin gado ta rafka tagumi. Tasan halin Aunty sarai, tun tana yarinya. Aunty nada hakuri amma bata daukar raini ko wani mis_behav. Mommy kuma yanzu ta koyi yimata masifa amma duk da haka tafi tsoron Aunty akan mommy, kuma bazata bijirewa Auntyba dan tasan ita kaɗaice zata sa mustapha ya yayarda ya aureta, dan haka dole tadinga bin umarnin ta. badan tasoba ta tashi ta ƙara haɗa kaya kamar yadda Aunty tace mata. Ƙarfe tara suka fito cikin shirinsu tsaf suka yiwa masu aiki sallama da abbansu aliya driver’n Aunty ya daukesu zuwa Jos. Suna fara tafiya mommy ta Kira suhailat, seda ta saci kallin aunty sannan ta ɗaga, amma ta kasa magana. Mommy tace, “daughter ga shinan naturo za’azo a daukeki” kasa_kasa suhailat tace, “mommy bama kaduna fa” a harzuke mommy tace “kuma ina?” “Munje wani gida da su Aunty a Jos, amma yanzu muna hanyar dawowa, idan muka dawo sena kiraki” tsaki mommy taja tace, “to sekun dawo ɗin, karfa kifada mata na dawo garinnan, dan banaso kowa yasani.” “Toh mommy bazan faɗaba” har mommy zata katse wayar tatuna tace, “dafatan dai baki faɗa mata maganar cikinnanba” satar kallon Aunty suhailat tayi tace. “Ehh” daga haka sukayi sallama.
Yau ina cikin farinciki, wanda kallo ɗaya zakamun kagano hakan saboda zuwansu Aunty. Tun jiya muka fara haɗa musu delicious, yauma munayin sallar asuba muka fara. Se wajen 12 muka gama komai. Part dinmu na koma naɗan kwanta akan gado da nufin na ɗan huta bansan sanda bacci ya ɗaukeni. Su Aunty sun iso lafiya inda aka musu masauki a part din ammi. Su mama dasu ammi se maraba da zuwa suke musu. Aliya kam baza ido takeyi taga ta inda zataga Maryam ɗinta ta bullo. Suhailat kam kallon su kawai take da mamaki, tasandai wadannan ba yan’uwan daddy bane sedai ko yan’uwan babansu aliyane. Amma duk inda ammi tayi se binta take da ido. Bayan sungama gaisawa ankawo musu ruwa sunsha Aunty tace, “ina Maryam ne da Muhammad?” Ammi tace, “bari nakirasa naji” ta ƙarashe zancen tana latsa wayarta tayi dialing number mustapha. Mustapha yana kwance a dakinsa akan gado kiran ammi yashigo wayartasa, dauka yayi ya daga ammi ta sanar masa su Aunty sun iso suzo shida Maryam. Mikewa yayi da hanzari ya fito ya nufi dakin maryam. Fitowata daga wanka kenan ina shiryawa naji ana knocking, sauri nayi na karasa shirinnawa sannan na buɗe Kofar. kallo ɗaya yayi mata ya dauke kansa, kamar bayason yin magana yace. “Su Aunty sun karaso” bandamu da yanda yamun maganaba dan naga kwana biyu miskilancinnasa ya motsa. faɗaɗa fara’ata nayi cikin jin daɗi na dakko mayafina nabi bayansa. Sunata shan hirarsu yayi sallama ya shiga falon. da sauri suhailat ta mike tsaye jin muryarsa da kuma ganinsa da tayi un_expected da ƙarfi tace, “yaya!” cikin tsananin mamaki da farinciki tana waro idonta waje, domin bata taɓa tsammanin ganinsa a wannan lokacinba a kuma nan garinba. kallo ɗaya ya mata yaɗauke kansa batare dayace mata ƙala ba. suhailat babu jira ko tunanin komai ta taho da gudu ta faɗa jikinsa ta rungumeshi tana murmushi cikin tsananin murnar ganinsa. daidai lokacin Maryam ta ƙaraso falon. Tsayawa nayi cak cikin matsananciyar faduwar gaba, Muryar Aunty suhailat ce ta tabbatarmun da itace inda take cewa. “Yaya i missed you so much” kallonsa kawai nakeyi naga yanayin re_action ɗin dazeyi ina ƙoƙarin fizgo numfashina ganin yana ƙoƙarin daukemun. Wani irin kishi naji acikin raina ganin wata mace kwance a kirjin mijina, bansan ya a kayiba kawai gani nayi najuya na fice daga falon ina haɗe hanya. Cire suhailat yayi daga jikinsa batare yace mata komaiba yana yamutsa fuskarsa kamar yaga kashi shima ya juya yabi bayan Maryam. suhailat dabatama lura da zuwan Maryam ba, balle tasan ita tabi ta taho itama zata bishi. Tsawar da Aunty ta matace yasa ta tsayawa zatayi magana ammi ta ɗaga mata hannu, fuskarta a haɗe tace. “dawo ki zauna” suhailat kamar zatayi kuka ta dawo ta zauna tana leken kofa. Umaimah kallon suhailat take cikin kishi, yanda tayi ya tabbatar mata da itama son mustapha’n take.