Uncategorized

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE

ABUNDA KA SHUKA COMPLETE HAUSA NOVEL

suhailat bayan taci kukanta ta koshi bacci yadauketa adakin mommy batare data shirya masaba. se wajen 2 tafarka. tashi tayi dasauri tafito falo,tana mamakin baccin datayi. tsit taji falon babu alamar mutum acikin part din. Dakin aunty ta nufa tana kwala mata kira, amma taji shiru. handle din dakin ta murda tajishi a rufe, tayi knocking ma taji shiru. maryam dake ciki tana bacci batamasan metakeba. duddubawata tayi har kitchen batagantaba, har dakin maryam ta leka. “To ina aunty tatafi, ko itama tatafi tabartane?” tatambayi kanta. kasa ta sauko inda tatarar da daya daga cikin masu aikin gidan a falo. Tambayarta tayi ina aunty, tace mata sunfita ita da su faruq. mamakine yakama suhailat akan ina kuma suka tafi suka barta ita daya agida.sama takoma dasauri ta shiga dakinta tadakko wayarta, number mommy tayi dialing. mommy suna zaune ita da binta sunata sakawa da kwancewa har lokacin kiran suhailat yashigo wayarta. dakkowa tayi taduba ganin sunan Sweet daughter nayawo akan screen din wayar yasata dagawa dasauri. cikin kuka suhailat tace, “mommy, kintafi kinbarni suma gashi suma sunfita dukansu seni kadai agidan” mikewa tsaye mommy tayi tace, “what? daughter banganeba suwaye suka tafi?” “Daddy, da aunty da yaya, dasu yafaruq da wannan yarinyar” muryar mommy narawa tace, “ina suka tafi?” “Bansaniba mom, danbasu fadaminba, nima asabe ce takefadamun” yawun bakin mommy ne ya kafe kaf, murnarta ta koma ciki, dafe kanta tayi, dakyar ta iya kokarin cewa. “Kihada kayanki yanzu zansa adakkoki akawoki inda nake” “to mommy” jefar da wayar mommy tayi, batare data katse kiranba, kotaba suhailat amsaba. “Lafiya Atika mekefaruwa kuma?” binta tatambayi mommy cikin mamakin ganin yanda yanayinta yasauya lokaci daya, harta fara zufa. wani numfashi mommy taja mehade da huci tace, “wai su sulaimanne sukayi tafiya yanzu basa gidan, se suhailat kadai,kenan hakan nanufin zasubar garinne kokuma yaya?” “tafiya kuma, zuwa ina?” binta ta tambayi mommy. “Oho, inazansani inanan” mommy tafadi haka akufule tana share zufar data tsatstsafo mata a goshinta. shiru binta tayi ganin mommy a kidime take. ita kuwa mommy zarya tahauyi a falon tsahon wasu mintuna, kafin ta dauki wayarta dasauri. number sadiq ta lalubo takira, tayi sa’a kuwa tashiga sedai bedagaba harta katse. tamai missed call yakai 5,amma yakidagawa. dole ta hakura takira driver dinta, akan yadakko suhailat yakawota gidan da take………✍️

BY
zeey kumurya
ABUNDA KASHUKA
(shizaka girba)

4️⃣1️⃣

Bismillahirrahmanirrahim

………Daddy ne zaune a office din wani doctor yana masa bayanin abunda kedamun matar dayaka buge. “Yallabai ka kwantar da hankalinka ba wata matsala bace babba, buguwa kawai tayi a kanta, kuma alhamdulillah munshawo kan matsalar,fatanmu kawai Allah yasa ta farka cikin hayyacinta. sekuma dogon suma datayi. yanzu zaka iya shiga kaganta, da yardar Allah zata farka zuwa nanda awanni biyu munmata allaurar baccine” wata doguwar ajiyar zuciya daddy yasauke bayan doctor yagama masa bayani. se’alokacin hankalinsa yafara kwanciya yawu ya hadiya dakyar yace. “Shikenan doctor nagode sosai” “babu komai, yallabai. fatanmu kawai Allah yabata lafiya yakuma kiyaye gaba” “ameen,ameen” daddy ya amsa. Paper doctor yamikawa daddy ta magungunan daza’asiyane. sallama daddy yamasa yafita bayan ya karbi paper. dakin da’aka kwantar da direban nan daddy yanufa, yayi sa’a kuwa ya farka har nurses sun cire masa karin ruwan da’aka masa. da sallama daddy yashiga dakin, amsa masa direban yayi yana kokarin mikewa zaune. taimaka masa daddy yayi yazauna yana jera masa sannu. shidai direban mamakin daddy kawai yakeyi yanda yake nuna damuwa da kulawa agaresu tamkar ba shahararren me kudiba,da wanine sedai yabiya kudi yace amsusu dukkan abunda yadace tunda yana da halin yin hakan, shikuma yakama gabansa. Kuma ga dukkan alamu shima yana saurine ze gudanar da wani uzurinnasa. daga ganinsa rayuwarsa bashida damuwa,ko girman kai irinna wasu masu kudin. lallai samun kamar alh, mai nasara se”….. “Sannu, yajikinnaka” daddy yakatse masa tunaninsa da tambayarsa. ajiyar zuciya yasauke yace “dasauki Alhaji” zama daddy yayi akan kujerar dake fuskantarsa yace, “Allah yakaro sauki, yasa kaffarane” “Ameen Alhaji” “yawwa, zuwa yanzu yakamata ace kakira gida kasanar dasu halin da’ake ciki” “nayi yunkurin yin hakan tun dazu, amma Inata kiran number maigidanta ita hajiyar bata shigaba” “Allah, sarki, tokuma babu wani dazaka kira seshi, kota yayantafa” dan jimmm, direban yayi kafin yace. “Ai bata da yaya ranka yadade, sedai yayan yayanta dasuke zaune gida daya, sukuma gaskiya bani da number dinsu” jinjina kai daddy yayi yace. “To ita ina wayarta semunemi number mukira, kaga ai baze yiyu ace haryanzu wani nata besaniba” “hakane, Alhaji, wayartata tana cikin Jakarta, kuma ina tunanin mun barota a cikin motar mu” daddy bekara cewa komaiba se wayarsa daya dakko daga aljihun gaban rigarsa yakira bakaniken daya tura yadauki motartasu, yace masa yaduba motar idan yaga jaka aciki yadakkota yabada akawo masa asibitin aminu kano yanzu. Amsa masa bakaniken yayi cikin girmamawa sannan yaduba, yana dubawa kuwa yaga jakar, a take yabada aka kawowa daddy. Number da matar tayi waya da ita last, ita daddy yakira. wata kawartace dazatayi bikin yarta, bikinma matar tataho, kuma wannan shine karonta na farko zuwa kano daga garin jos. kawartata ta rude sosai, dama tanata kiran wayarta taji kota karaso bata shiga, cikin hanzari suka kimtsa ita da wasu yayanta suka nufo asibitin. ansamu number maigidannata ta shiga shima ansanar masa. masallaci daddy yanufa domin yin sallah, bayan yagama kiraye_kirayen wayar zuciyarsa cike da mamakin abunda yatsaida su aunty karasowa asibitin haryanzu……….

Abangaren su aunty ma, ansamu anshawo kan ciwon mustapha, dama damuwace kawai ta masa yawa, wanda hakan yasa jininsa yahau sosai. dukansu sunsashi agaba sunyi tagumi jigum_jigum, su haidar harda kuka dasukaji daddy sunyi accident. wannan wacce irin jarrabawace daga wannan se wannan, to Allah yatsayar haka,shine addu’ar dasukayi kawai. Numfashi aunty ta sauke cikin karayar zuci, na wannan bakon al’amari daya samesu. wayartace tayi kara. Ahankali tasa hannu ta daukkota, Abban aliyane ke kiranta dagawa tayi dayin sallama cikin sanyin murya. “Wa’alaikumussalam, hajiya sauda yajikin mustaphan?” (Dayake takirasa tafada masa) “dasauki Abbansu, gashinanma yanata bacci” cikin tausayawa abbansu aliya yace, “Allah yakara sauki, Allah yayankewa yaronnan wannan wahala haka” “Ameen, abbansu, kuntahone?” “A’a, yanzudai zamu taho, dan auta bata jima da dawowa daga islamiyyaba” “shikenan, Abbansu sekun karaso” sukayi sallama aunty ta kashe wayar. number daddy takira, har 3 missed call tamasa bedagaba, time din yana sallah ne, seda ya idar yabiyo bayan kiran. bayan tadaga yace, “hello saudart” “na’am, yaya yamasu jikin” “dasauki Alhamdulillah, danshi direbanma ya warware matarcedai haryanzu tana kwance tana bacci” “Allah yakara sauki yakiyaye gaba” “Ameen, sauda. Najiku shiru kuma baku zoba haryanzu, gashi su ashema ba’a garinnan sukeba, daga jos sukataho biki, babu wanda yazo haryanzu danbanma jima dasanar musuba, sedai gidan dasukazo bikin sunce gasunan zuwa.” shiru aunty tayi gabanta nadan faduwa, tana tsoron ta fada masa mustapha babu lafiya yakara shiga wani tashin hankalin. “Hello, sauda naji kinyi shiru, ina mustapha fa?” wata boyayyiyar ajiyar zuciya aunty ta sauke tace, “yaya mustapha, gashi kwance babu lafiya muna asibitima yanzu haka, shine dalilinma dayasa kajimu shiru” “innalillahi, meke damunsa kuma?” “damuwace kawai yaya, hartasa jininsa yahau, naki fada makane saboda kar hankalinka yatashi, ga wancan ga wannan” “ya salaammm, ya subhanallah” daddya yafadi haka cikin tsananin damuwa yana fesar da numfashi. “hakuri zamuyi yaya, haka Allah yakaddaro mana babu yanda zamuyi, amma insha Allahu, komai zedaidaita, banason katada hankalinka yaya, kacigaba da juriya da addu’a, da yardar Allah komai zezama tarihi kamar ba’ayiba” jinjina kai daddy yayi yace, “hakane sauda, yanzu kuna wanne asibitin?” Asibitin aunty tafada masa, yace gashinan zuwa. Daddy bebar asibitinba seda kawar matarnan tazo, yakuma siyo dukkan magungun da’aka bukata gami da duk wani dayasan zasu bukata, se wajen karfe biyar yabar asibitin….

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button