KUSKUREN BAYA 1 TO 48

juyawa yayi a matukar fusace ya bar d’akin zuwa dayan bangaresa ya shiga ziriya a falon yana kai kawo “zuciyarsa ta dinga raya masa ya amincewa aurenta ko dan ya musguna mata ya koya mata hankali yayinda wata zuciyar take ce masa ” kai da baka son aure yanzu karka sake ka yarda ka aureta ya bawa kanshi amsa “ina bazan aureta ba a daren yau din nan zan sa a maidaita gidansu, taje can ta k’arata” yana cikin wannan tunanin wayarsa ta soma ringing ya ciro wayar daga cikin aljihun wandonsa yana dubawa ganin sunan zahra na yawo a screen din wayar yasa shi jan dogon tsaki , yaki daukar kiran ya kashe tare da ajiye wayar akan mirrow dinsa ya shiga bathroom wanka yayi shap shap ya fito, ya sauya kawa zuwa manya kaya farin yadi vol mai matukar kyau da tsada ya karasa inda jerin takalmansa suke ya dauki takalmin mai yanayin cover shoe Wanda bayansa ke bude ya feshe ilahirin jikinsa da turaruka masu dadin kamshi da tsayawa arai ya fito yana taku kamar baya son taka kasa ya karasa inda motorsa ferary take Parke ya shiga ya bar gidan ..
A hankali yake tuki yana tunanin zantuttukan yarinyar har ya karaso unguwarsu yayi parking a kofar gidan daya ginawa mahaifiyarsa jamar dake zaune a unguwar suna ganin motarsa suka mike domin kawo gaisuwa ya fito a natse suka gaisa cike da natsuwa tare da kwanciyar hankali ya shiga gidansu a hankali kannenshi suka shiga farincikin ganinsa haniyarsu ce tasa hajiyarsa fitowa domin jin sautinsu suna kiran sunansa ta fito , ganinshi tayi tsaf kamar koda yaushe cikin natsuwa da kamala taji dadin ganinsa sai dai ta hade rai saboda kusan sati biyu kenan bata sanya shi a cikin kwayar idanunta ba, fuskarsa ta dauke da murmushin yace “Hajiya ina yini ? Cikin rashin walwala tace “um lafiya sai yau kaga damar zuwa ? “Kiyi hakuri duk cikin kwanankin nan ban zauna bane tunda na dawo sai faman zirga zirga muke yi akan wani aiki daya tasanyomu gaba dasu jabir “shine har ka ɗauki tsawon sati biyu duk yan’uwanka sun damu da rashin ganinka “nasan zaku ji babu dadi rashin zuwana sai dai ayi min hakuri saboda yanayin aikina ai muna waya da sadiq akai akai “ya fada min sai dai ai zuwan naka na da mahimmancin “koda yake ko babu yanayin aiki zaka iya dauke kafafunka saboda maganar aure da nake yawon maka “yayi murmushin yana Kallonta cike da matsanamcin soyayyarta yana matukar kaunarta ita da yan’uwansa numfasawa yayi sannsn yace” wallahi ba haka bane Hajiya shifa aure lokaci ne “,nafi ka sanin lokaci ne amman shi kanshi niyya yana da matukar tasiri idan kuma sai na mutu zakayi shikenna sai ka faɗa min na hakura “kiyi hakuri inshallah nan kusa zan kokarta “gara ka kokarta dan ga sadiq nan yana son yin aure amman yace dole sai ka fara yi ,dogon numfashin ya sauke sannan yace “shikenan zan san abun yi'”Allah yayi jagora nan suka shiga hira da zai tafi ya bawa kannenshi kudi yace su sayi duk abinda suke so bai yi musu tsaraba ba mahaifiyarsa ma kudi masu yawa ya bata hajiya tace “haba bazan amshi kudin nan ba yaushe kayi mana sako “ki amsa hajiya da bani da shi bazan muku ba “haka ne Allah ya kareka da kariyarsa ya albarkacin da zuri’a masu albarka “shine abinda nafi bukata daga gareki adduarki tana da matukar tasiri a rayuwata kuma ina gani cigaba ,a cigaba da yi min addu’a”Allah yayi maka albarka ya baka abinda kake so duniya da lahira ya kare min kai, yayi murmushin jin dadi sai bayan la’asar sannan yayi mata sallama ya fito inda jamar unguwar suka yi masa caaaa kudi ya raba musu sannan ya wuce
DARLING’S????????????????????????
KUSKUREN BAYA
????????????????
????????????????????????
WRITING BY
BAGUDO& MIMI’S QUEEN
WATTPAD @HAUESH
bismillahirrahmanirrahim
????️05
Cikin natsuwa yake murza kan
Stearing motarsa zuciyarsa cike fal da matsanancin farinciki baro mahaifiyarsa da kannensa cikin farinciki mai tsanani da yayi, a nan duniya bashi da burin daya wuce sanya ahlinsa cikin farinciki , numfashi ya janyo ya fesar yana ɗan dukan kan stearing “zan dangwama ina baki farincikin da kika rasa ammina har sai kin gaji , inshallahu zan ɗauke miki kewar komai ,zan mallaka miki duk wani dadi dake cikin duniyar nan ke da yan’uwana lafiyarku farincikinku jin dadin rayuwa zan yi kokari ……
Kiran Anas da ya shigo wayarsa ne ya katse masa zancen zuci da yake , ya sauke naunauyen ajiyar zuciya sannan ya kai idanunshi kan wayar a natse ya kai hannunsa ɗaya ya ɗauki bluetooth dinsa ya manna a kunnen ya dannan wayar take muryar Anas ta doki dodon kunnenshi “kana Ina munzo gida mai gadi yace baka nan ? Iskar ya furzar sannan yace “naje ganin ammina ne gani akan hanyar dawowa ku bani minti goma zan karaso “okay sai ka karaso muna jiranka ..
Ya cire bluetooth din ya ajiye a mazauninsa ya cigaba da tuki yana sake lulawa zance zuci har zuciyarsa ta shiga hasko masa yarinyar daya baro a gidansa dogon tsaki yaja saboda tuno kalmar ta gareshi kalmar da yaki jininta kuma take bashi haushi ….
Jaguwa zaune cikin d’akin daya tanada domin tautauna bayanai masu mahimmanci akan aikinsa ,gabansa laptop dinshi ne ,yana faman operating yana sauraron bayanan jubi inda yake bayani akan alhaji tanko gote wanda ya kasance shararraren dan kasuwa wanda duniya tasan da zamansa sannan ya tara tarin dukiya bilaadadin anan gida nigeria da kasashen ketari ,ya mallaki qadarori da dama da companies a kowace jaha dake ƙasar nigeria ” bincikenmu ya nuna mana mutumin baya zaman gidansa da daddare sai da rana bayan haka akwai tsaro mai tsanani tun daga bakin get doping estate har zuwa cikin gidansa ta kowani bangare dakarunsa zagaye suke da gidan bayan boyayyun camerori dake lugu da sako na gidansa, me zai hana mu hakura da wannan taget din muyi facing din wani yayi shiru hade da numfasawa sannan ya cigaba da magana “jaguwa a ganina mu hakura da wannan aiki kawai ko me kuka ce yan’uwa ? ya fadi haka yana kallon sauran yan’uwansa dake zaune suna sauraronsa , duk suka gyara “gaskiya mu hakura tun da tsaro yayi yawa inji cewar kamil ,Anas ya numfasa yace ” kuna nufin bazamu yi nasara ba akan aikin da muka ɗauki tsawon lokaci muna jiran aiwatar dashi ? a qalla wannan shine karo na hudu da muke rusa budget din aiki akan Alhaji tanko gote gaskiya a ganina bai kamata muyi wasa da damarmu ba kawai mu fara shirin aiwatar dashi kuma a cikin satin nan “dan Allah malam ka natsu kayi nazari akan operation din nan jabir ya katse masa hanzari ta hanyar fadar haka”the best solution mu hakura tunda jubi da kamil suka nuna abar shi , kai koni nayi supporting dinsu mu hakura kawai muyi facing din wani aiki ……